FAR 39

Yusufu da Matar Fotifar

1 Aka kuwa gangara da Yusufu zuwa Masar. Sai Fotifar Bamasare sarkin yaƙin Fir’auna, shugaban masu tsaron fāda ya saye shi daga hannun Isma’ilawa, waɗanda suka gangaro da shi zuwa can.

2 Ubangiji yana tare da Yusufu, har ya zama mutum ne mai galaba a gidan maigidansa Fotifar, Bamasaren.

3 Maigidansa kuwa ya ga Ubangiji yana tare da shi, Ubangiji kuma yakan sa albarka ga aikin hannuwansa duka.

4 Don haka Yusufu ya sami tagomashi a wurinsa, ya zama mai yi masa hidima. Fotifar kuma ya shugabantar da shi a bisa gidansa, da bisa dukan abin da yake da shi.

5 Ubangiji ya sa wa gidan Bamasaren albarka sabili da Yusufu tun daga lokacin da Fotifar Bamasaren ya shugabatar da shi a bisa gidansa da dukan dukiyarsa. Albarkar Ubangiji na bisa dukan abin da yake da shi, na gida da na jeji.

6 Ya bar dukan abin da yake da shi a hannun Yusufu. Tun da ya same shi, ba ruwansa da kome, sai dai abincin da zai ci.

Yusufu fa kyakkyawa ne mai kyan gani.

7 Ya zamana fa, wata rana, sai matar maigidansa ta sa idonta kan Yusufu, ta ce, “Ka kwana da ni.”

8 Amma ya ƙi, ya kuwa faɗa wa matar maigidansa, ya ce, “Ga shi, tun da maigida ya same ni, maigidana ba ruwansa da kome na cikin gida, ya kuwa riga ya sa dukan abin da yake da shi cikin hannuna.

9 Bai fi ni iko cikin gidan nan ba, ba kuma abin da ya hana mini sai ke kaɗai, domin ke matarsa ce. Ƙaƙa fa zan aikata wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?”

10 Ko da yake ta yi ta yi wa Yusufu magana yau da gobe, amma bai biye mata ya kwana da ita ko su zauna tare ba.

11 Amma wata rana, sa’ad da ya shiga cikin gida ya yi aikinsa, mazajen gidan kuma ba wanda yake gidan,

12 sai ta kama rigarsa, tana cewa, “Ka kwana da ni.” Amma ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita.

13 Da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu, ya fita waje,

14 sai ta yi kira ga mutanen gidan, ta ce musu, “Ku duba ku gani, ya kawo mana Ba’ibrane ya ci mutuncinmu. Ya zo wurina don ya kwana da ni, sai na yi ihu da ƙarfi.

15 Da ya ji na ta da murya na yi ihu, ya kuwa gudu ya bar rigarsa, ya fita waje.”

16 Ta ajiye rigar a wurinta har maigidansa ya komo.

17 Sai ta mayar masa da magana, ta ce, “Baran nan, Ba’ibrane wanda ka kawo cikinmu, ya shigo wurina don ya ci mutuncina,

18 amma nan da nan da na ta da murya na yi ihu, sai ya gudu ya bar rigarsa a hannuna, ya gudu zuwa waje.”

19 Sa’ad da maigidan Yusufu ya ji abin da matarsa ta faɗa masa, “Ka ji yadda baranka ya yi da ni ke nan,” sai ya husata.

20 Maigidan Yusufu ya ɗauke shi ya māka shi a kurkuku, inda ‘yan sarƙa na sarki suke tsare, can ya zauna a kurkuku.

21 Amma Ubangiji yana tare da Yusufu, ya kuwa nuna masa madawwamiyar ƙauna, ya sa ya sami farin jini a wurin yarin kurkukun.

22 Yarin kurkuku ya shugabantar da Yusufu bisa dukan ‘yan sarƙa da suke a kurkuku, dukan abin da ake yi a wurin kuma shi yake yi.

23 Yarin kurkukun, ba ruwansa da dukan abin da Yusufu yake kula da shi, domin Ubangiji yana tare da shi, dukan abin da ya yi kuwa Ubangiji yakan sa wa abin albarka.