FAR 45

Yusufu ya Bayyana Kansa ga ‘Yan’uwansa

1 Yusufu ya kasa daurewa a gaban dukan waɗanda suke a tsaye kusa da shi, sai ya ta da murya ya ce, “Kowa ya ba mu wuri.” Saboda haka ba mutumin da ya tsaya a wurin sa’ad da Yusufu ya bayyana kansa ga ‘yan’uwansa.

2 Ya yi kuka da ƙarfi, har Masarawa suka ji, labarin kuwa ya kai gidan Fir’auna.

3 Yusufu kuwa ya ce wa ‘yan’uwansa, “Ni ne Yusufu. Mahaifina yana da rai har yanzu?” Amma ‘yan’uwansa ba su iya ba shi amsa ba, gama sun firgita a gabansa.

4 Yusufu ya ce wa ‘yan’uwansa. “Ku matso kusa da ni, ina roƙonku.” Suka matso kusa. Sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku, Yusufu, wanda kuka sayar zuwa Masar.

5 Yanzu fa, kada ku damu ko kuwa ku ji haushin kanku domin kun sayar da ni a nan, gama Allah ne ya aike ni a gabanku don in ceci rai.

6 Gama shekara biyu ke nan da ake yunwa a ƙasar, amma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.

7 Allah kuwa ya aike ni a gabanku, domin in cetar muku da ringi a duniya, in kuma rayar muku kuɓutattu masu yawa.

8 Don haka, ba ku kuka aiko ni nan ba, amma Allah ne, shi ne kuwa ya sa in zama uba ga Fir’auna, da shugaban gidansa duka, mai mulki kuma bisa ƙasar Masar duka.

9 “Ku gaggauta, ku hau zuwa wurin mahaifina ku ce masa, ‘Ga abin da Yusufu ɗanka ya ce, “Allah ya maishe ni shugaban Masar duka, ka gangaro wurina kada ka yi wata wata.

10 Za ka zauna a ƙasar Goshen, za ka zauna kusa da ni, kai da ‘ya’yanka da jikokinka, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunanka na shanu, da dukan abin da kake da shi.

11 A nan zan cishe ka, gama akwai sauran shekara biyar masu zuwa na yunwa, don kada ka tsiyace, kai da iyalinka, da duk wanda yake tare da kai.’ ”

12 Yanzu, da idanunku kun gani, idanun ɗan’uwana Biliyaminu kuma sun gani, cewa bakina ne yake magana da ku.

13 Ku faɗa wa mahaifina dukan darajar da nake da ita a Masar da dukan abin da kuka gani. Ku gaggauta ku gangaro mini da mahaifina a nan.”

14 Sai Yusufu ya rungumi ɗan’uwansa Biliyaminu ya yi ta kuka, Biliyaminu ma ya yi kuka a bisa kafaɗun Yusufu.

15 Ya sumbaci ‘yan’uwansa duka, ya yi kuka bisansu, bayan wannan sai ‘yan’uwansa suka yi taɗi da shi.

16 Sa’ad da labari ya kai gidan Fir’auna cewa, “’Yan’uwan Yusufu sun zo,” abin ya yi wa Fir’auna da fādawansa daɗi ƙwarai.

17 Sai Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ka faɗa wa ‘yan’uwanka su yi wannan, ‘Ku yi wa dabbobinku laftu ku koma a ƙasar Kan’ana.

18 Ku ɗauko mahaifinku da iyalanku, ku zo wurina, ni kuwa zan ba ku yankin ƙasa mafificiya a Masar, za ku ci moriyar ƙasar.’

19 Ka kuma umarce su ka ce, ‘Ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin ‘yan ƙanananku da matanku, ku ɗauko mahaifinku, ku zo.

20 Kada ku damu da kayayyakinku, gama abin da yake mafi kyau duka a ƙasar Masar naku ne.’ ”

21 Haka kuwa ‘ya’yan Isra’ila suka yi. Yusufu kuma ya ba su kekunan shanu bisa ga umarnin Fir’auna, ya ba su guzuri don hanya.

22 Ga kowane ɗayansu ya ba da rigar ado, amma ga Biliyaminu ya ba da azurfa ɗari uku, da rigunan ado biyar.

23 Ga mahaifinsa kuwa ya aika da jakai goma ɗauke da kyawawan abubuwa na Masar, da jakai mata goma ɗauke da tsaba, da kuma abinci da guzurin hanya saboda mahaifinsa.

24 Ya sallami ‘yan’uwansa. Da suna shirin tashi, sai ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya.”

25 Suka haura daga Masar, suka zo ƙasar Kan’ana zuwa wurin Yakubu mahaifinsu.

26 Suka ce masa, “Har yanzu Yusufu yana nan da rai, shi ne kuwa mai mulki bisa ƙasar Masar duka.” Sai gabansa ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.

27 Amma sa’ad da suka faɗa masa jawaban Yusufu duka, waɗanda ya faɗa musu, sa’ad da kuma ya ga kekunan shanun da Yusufu ya aiko don a ɗauke shi, sai ruhun mahaifinsu Yakubu ya farfaɗo.

28 Isra’ila ya ce, “I, ya isa, ɗana Yusufu yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”