An Ci Amoriyawa da Yaƙi
1 Da Adonizedek, Sarkin Urushalima, ya ji yadda Joshuwa ya ci Ai, har ya hallakar da ita sarai kamar yadda ya yi wa Yariko da sarkinta, da kuma yadda mazaunan Gibeyon suka yi amana da Isra’ilawa, har suna zama cikinsu.
2 sai ya tsorata ƙwarai, gama Gibeyon babban birni ce kamar ɗaya daga cikin alkaryai, har ma ta fi Ai girma, mazajenta duka kuwa ƙarfafa ne.
3 Adonizedek Sarkin Urushalima, ya aika zuwa ga Hoham Sarkin Hebron, da Firam Sarkin Yarmut, da Yafiya Sarkin Lakish, da Debir Sarkin Eglon, ya ce,
4 “Ku zo, ku taimake ni, mu yaƙi Gibeyon, gama ta yi amana da Joshuwa da Isra’ilawa.”
5 Sarakunan nan biyar na Amoriyawa, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon, suka tattaru da dukan rundunansu, suka haura, suka kafa wa Gibeyon sansani don su yaƙe ta.
6 Gibeyonawa dai suka aika zuwa wurin Joshuwa a zango cikin Gilgal cewa, “Kada ka yar da bayinka. Ka zo wurinmu da sauri, ka cece mu, ka taimake mu, gama dukan sarakunan Amoriyawa da suke zaune a ƙasar tuddai sun tattaru a kanmu.”
7 Sai Joshuwa ya tashi daga Gilgal da dukan mayaƙa, da dukan jarumawa tare da shi.
8 Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu gama na riga na ba da su a hannunka, ba mutuminsu da zai iya tsayawa a gabanka.”
9 Sai Joshuwa ya tafi ya auka musu ba labari, gama daga Gilgal ya bi dare zuwa can.
10 Ubangiji kuwa ya sa suka gigice a gaban Isra’ilawa. Isra’ilawa suka kashe su da yawa a Gibeyon, suka runtume su ta hanyar haurawa zuwa Bet-horon. Suka yi ta karkashe su har zuwa Azeka da Makkeda.
11 Sa’ad da suke gudun Isra’ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kashe da takobi.
12 Sa’an nan Joshuwa ya yi magana da Ubangiji a gaban Isra’ilawa a ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa gare su, ya ce,
“Ke rana, ki tsaya a Gibeyon,
Kai kuma wata, ka tsaya a kan kwarin Ayalon.”
13 Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya,
Har al’ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābansu.
Ai, wannan a rubuce yake a littafin Yashar. Rana dai ta tsaya a tsaka, ta yi jinkirin faɗuwa da misalin yini guda.
14 Ba a taɓa yin yini kamar wannan ba, ko kafin wannan yini, ko bayansa kuma, da Ubangiji ya saurari muryar mutum. Gama Ubangiji ya yi yaƙi domin Isra’ilawa.
15 Sa’an nan Joshuwa ya koma zango a Gilgal tare da dukan Isra’ilawa.
16 Waɗannan sarakuna biyar kuma suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda.
17 Aka faɗa wa Joshuwa cewa, “An sami sarakunan nan biyar, sun ɓuya a kogo a Makkeda.”
18 Sai Joshuwa ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu, ku rufe bakin kogon, sa’an nan ku sa mutane su yi tsaronsu.
19 Amma kada ku tsaya a can, sai ku runtumi abokan gābanku, ku bugi na bayansu, kada ku bar su su shiga biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya ba da su a hannunku.”
20 Joshuwa da jama’ar Isra’ila suka karkashe su da yawa ƙwarai, sauransu kuma da suka ragu suka shiga birane masu garu.
21 Sa’an nan dukan mutane suka koma wurin Joshuwa a sansani a Makkeda lafiya. Ba kuma mutumin da ya tsokani Isra’ilawa.
22 Sa’an nan Joshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon, ku kawo mini waɗannan sarakuna biyar da suke a kogon.”
23 Suka yi haka nan, suka kawo masa sarakunan nan biyar daga cikin kogon, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon.
24 Da suka kawo sarakunan a wurin Joshuwa, sai Joshuwa ya kirawo dukan Isra’ilawa, sa’an nan ya ce wa shugabannin mayaƙa, waɗanda suka tafi tare da shi, “Ku matso kusa, ku taka wuyan sarakunan nan.” Suka kuwa zo kusa, suka taka wuyansu.
25 Sai Joshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, gama haka Ubangiji zai yi da dukan abokan gābanku waɗanda za ku yi yaƙi da su.”
26 Sa’an nan Joshuwa ya buga su, ya kashe su, ya kuma rataye kowane ɗayansu a bisa itace. Suka yini a rataye har maraice.
27 Amma sa’ad da rana take faɗuwa, Joshuwa ya umarta, aka saukar da gawawwakinsu daga bisa itatuwan, aka jefa su cikin kogon inda suka ɓuya. Sa’an nan suka rufe bakin kogon da manyan duwatsu. Har wa yau suna nan.
28 A wannan rana kuwa Joshuwa ya ci Makkeda da yaƙi, ya kashe mutanenta da sarkinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Ya yi wa Sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa Sarkin Yariko.
29 Joshuwa ya zarce, da shi da dukan Isra’ilawa zuwa Libna, suka yi yaƙi da Libna.
30 Ubangiji ya bashe ta da sarkinta a hannun Isra’ilawa, suka kuwa buge ta da takobi, da kowane mutum da yake cikinta, ba su rage kowa cikinta ba. Suka yi wa sarkinta kamar yadda suka yi wa Sarkin Yariko.
31 Joshuwa kuma ya zarce daga Libna, da shi da Isra’ilawa duka , zuwa Lakish, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata.
32 Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra’ilawa suka cinye ta da yaƙi cikin kwana biyu. Suka bugi kowane mutum da yake cikinta da takobi kamar yadda suka yi wa Libna.
33 Horam, Sarkin Gezer kuwa, ya kawo wa Lakish gudunmawa, Joshuwa kuwa ya buge shi tare da mutanensa, har ba wanda ya ragu.
34 Joshuwa kuma ya zarce tare da dukan Isra’ilawa daga Lakish zuwa Eglon, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata.
35 A ran nan suka cinye ta, suka buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi. Ya hallakar da su a wannan rana kamar yadda ya yi wa Lakish.
36 Joshuwa kuma ya haura tare da dukan Isra’ilawa daga Eglon zuwa Hebron, suka auka mata.
37 Suka cinye ta, suka buge ta, da sarkinta, da garuruwanta, da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta.
38 Sai Joshuwa ya juya tare da dukan Isra’ilawa zuwa Debir, ya auka mata.
39 Ya cinye ta da yaƙi, da sarkinta, da garuruwanta. Ya buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Kamar yadda ya yi wa Hebron, da Libna da sarkinta, haka kuma ya yi wa Debir da sarkinta.
40 Haka nan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarta.
41 Joshuwa kuma ya cinye su da yaƙi tun daga Kadesh-barneya har zuwa Gaza, da dukan ƙasar Goshen har zuwa Gibeyon.
42 Joshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya, gama Ubangiji Allah na Isra’ila ya yi yaƙi domin Isra’ilawa.
43 Sa’an nan Joshuwa ya komo tare da dukan Isra’ilawa zuwa zango a Gilgal.