An Rarraba Ƙasar Kan’ana ta Hanyar Kuri’a
1 Waɗannan su ne karkasuwar gādon da Isra’ilawa suka karɓa a ƙasar Kan’ana, wanda Ele’azara, firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin iyalan kabilan Isra’ila suka ba su.
2 Kabilan nan tara da rabi sun karɓi nasu rabon gādo ta hanyar jefa kuri’a, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
3 Gama Musa ya riga ya ba kabilan nan biyu da rabi nasu gādo a wancan hayin Kogin Urdun wajen gabas, amma bai ba Lawiyawa rabon gādo ba.
4 Jama’ar Yusufu kuwa kabila biyu ce, wato Manassa da Ifraimu. Ba a kuma ba Lawiyawa rabon gādo a ƙasar ba, sai dai an ba su biranen da za su zauna, da filayen da za su yi kiwon garkensu.
5 Jama’ar Isra’ila fa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, suka rarraba ƙasar ta hanyar kuri’a.
An Ba Kalibu Hebron
6 Mutanen Yahuza suka je wurin Joshuwa a Gilgal, sa’an nan Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, “Ka dai san maganar da Ubangiji ya yi wa Musa, mutumin Allah, a Kadesh-barneya a kaina.
7 Ina da shekara arba’in sa’ad da Musa bawan Ubangiji ya aike ni daga Kadesh-barneya don in leƙi asirin ƙasar. Na kuma kawo masa ainihin rahoton yadda yake a zuciyata.
8 Amma ‘yan’uwana da muka tafi tare, sun karya zukatan jama’ar, amma ni na bi Ubangiji Allahna da aminci.
9 Musa kuwa ya rantse a wannan rana ya ce, ‘Hakika duk inda ƙafafunka suka taka a ƙasan nan zai zama gādonka, kai da ‘ya’yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahnka sosai!’
10 Ga shi kuwa, Ubangiji ya kiyaye ni har wa yau, kamar yadda ya faɗa, shekara arba’in da biyar ke nan, tun lokacin da Ubangiji ya faɗa wa Musa wannan magana, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a jeji. Ga shi yau ni mai shekara tamanin da biyar ne.
11 Ga shi kuwa, har wa yau ina da ƙarfi kamar ran da Musa ya aike ni. Kamar yadda ƙarfina yake a dā, haka yake a yanzu domin yaƙi, da kuma kai da kawowa.
12 Saboda haka sai ka ba ni ƙasar tuddai da Ubangiji ya ambata a ranan nan, gama a wannan rana ka ji yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu, mai yiwuwa ne Ubangiji zai kasance tare da ni, in kore su kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”
13 Joshuwa ya sa wa Kalibu, ɗan Yefunne, albarka. Ya ba shi Hebron ta zama gādonsa.
14 Domin haka Hebron ta zama gādon Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, har wa yau, domin ya bi Ubangiji Allah na Isra’ila sosai.
15 A dā sunan Hebron Kiriyat-arba ne. Arba kuwa babban mutum ne cikin gwarzayen. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.