Joshuwa Ya Yi wa Jama’a Jawabi
1 An daɗe bayan da Ubangiji ya hutar da Isra’ilawa daga abokan gābansu waɗanda suke kewaye da su. Joshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa.
2 Sai Joshuwa ya kira Isra’ilawa duka, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, da jarumawansu, ya ce musu, “Yanzu na tsufa, shekaruna sun yi yawa,
3 kun dai ga abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan al’ummai duka saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku.
4 Ga shi kuma, na rarraba wa kabilanku ƙasashen al’umman da suka ragu, da na waɗanda na shafe su tsakanin Urdun da Bahar Rum wajen yamma.
5 Ubangiji Allahnku ne zai sa su gudu a gabanku, ya kore su daga ƙasar. Za ku mallaki ƙasarsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku.
6 Domin haka sai ku yi ƙarfin hali ƙwarai, ku riƙe, ku aikata dukan abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, kada ku kauce dama ko hagu,
7 domin kada ku yi cuɗanya da sauran al’umman da take zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu.
8 Amma ku manne wa Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi har wa yau.
9 Gama Ubangiji ya kori manyan al’ummai ƙarfafa daga gabanku, har wa yau ba mutumin da ya isa ya yi hamayya da ku.
10 Mutuminku guda zai runtumi mutum dubu nasu, tun da yake Ubangiji Allahnku ne yake yaƙi dominku, kamar yadda ya alkawarta muku.
11 Ku kula da kanku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku.
12 Gama idan kun kauce, kun koma da baya, kun haɗa kai da sauran al’umman nan da take tare da ku, har kuka yi aurayya da juna,
13 to, sai ku tabbata Ubangiji Allahnku ba zai dinga korar al’umman nan daga gabanku ba, za su zama muku azargiya, da tarko, da bulala a kwiyaɓunku, da ƙayayuwa a idanunku. Da haka za ku ƙare sarai daga cikin kyakkyawar ƙasan nan da Ubangiji Allahnku ya ba ku.
14 “A yanzu ina gaba da bin hanyar da kowa a duniya yakan bi, ku duka kuwa, a zukatanku da rayukanku, kun sani dukan abubuwan alheri da Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku sun tabbata, ba ɗayan da bai tabbata ba.
15 Amma kamar yadda Ubangiji Allahnku ya cika alkawaran da ya yi muku, haka nan kuma Ubangiji zai aukar muku da masifu, har ya hallaka ku daga ƙasan nan mai albarka da Ubangiji Allahnku ya ba ku.
16 Lokacin da kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku da ya umarce ku, kuka tafi kuka bauta wa gumaka, kuka sunkuya musu, to, Ubangiji zai yi fushi da ku, zai kuwa hallaka ku daga ƙasa mai albarka da aka ba ku.”