Jawabin Joshuwa na Bankwana a Shekem
1 Joshuwa kuma ya tara dukan kabilan Isra’ila a Shekem, ya kuma kira dattawa, da shugabanni, da alƙalai, da jarumawan Isra’ila. Suka hallara a gaban Allah.
2 Joshuwa kuwa ya ce wa mutane duka, “Ga abin da Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘A zamanin dā kakanninku, su Tera, mahaifin Ibrahim, da Nahor, suna zaune a hayin Yufiretis. Suka bauta wa gumaka.
3 Sai na ɗauki kakanku Ibrahim daga wancan hayin Kogi, na kawo shi ƙasar Kan’ana, na sa zuriyarsa ta yawaita. Na ba shi Ishaku.
4 Ishaku kuma na ba shi Yakubu da Isuwa. Na kuma ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir, ya mallake ta, amma Yakubu da ‘ya’yansa suka gangara zuwa Masar.
5 Na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masar da annobai ta wurin abin da na yi a cikinta daga baya kuma na fisshe ku.
6 Na kuwa fitar da kakanninku daga Masar. Da suka zo Bahar Maliya, sai Masarawa suka fafari kakanninku da karusai da mahayan dawakai har zuwa teku.
7 A sa’ad da suka yi mini kuka, na sa duhu a tsakaninsu da Masarawa, na sa teku ta shafe Masarawa. Da idonku kun ga abin da na yi wa Masar, kuka kuma zauna a jeji da daɗewa.
8 Sa’an nan na kawo ku a ƙasar Amoriyawa, waɗanda suka zauna a wancan hayin Urdun, waɗanda kuma suka yi yaƙi da ku, na kuwa ba da su gare ku, na hallaka su, kuka mallaki ƙasarsu.
9 Haka kuma Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya tashi ya yi yaƙi da Isra’ila, har ya gayyaci Bal’amu, ɗan Beyor, ya zo ya la’anta ku.
10 Amma ban saurari Bal’amu ba, saboda haka ya sa muku albarka, ta haka na cece ku daga hannunsa.
11 Da kuka haye Urdun, kuka zo Yariko, mutanen Yariko kuwa suka yi yaƙi da ku, haka kuma Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Kan’aniyawa da Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, amma na ba da su a gare ku.
12 Na kuma aiki zirnako a gabanku, waɗanda suka kori sarakunan nan biyu na Amoriyawa daga gabanku. Ba takobinku, ko bakanku ya kore su ba.
13 Na ba ku ƙasar da ba ku yi wahala a kanta ba, da biranen da ba ku gina ba, ga shi, kuna zaune a ciki, kuna kuma cin ‘ya’yan inabi, da na zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba.’
14 “To fa, ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa da sahihanci da aminci, ku yi watsi da gumakan da kakanninku suka bauta wa a hayin Kogin Yufiretis, da cikin Masar.
15 Idan ba ku da nufi ku bauta wa Ubangiji, to, yau sai ku zaɓi wanda za ku bauta wa, ko gumakan da kakanninku suka bauta wa a wajajen hayin Kogin Yufiretis, ko kuma gumakan Amoriyawa waɗanda kuke zaune a ƙasarsu, amma ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.”
16 Jama’a kuwa suka amsa suka ce, “Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji, har a ce mu bauta wa gumaka.
17 Gama Ubangiji Allahnmu ne ya fisshe mu da kakanninmu daga ƙasar Masar, a gidan bauta. Shi ne wanda ya aikata manyan alamu a idonmu, ya kuma kiyaye mu a dukan hanyar da muka bi, da cikin dukan al’umman da muka ratsa.
18 Ubangiji kuwa ya kore mana dukan Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar, domin haka za mu bauta wa Ubangiji, gama shi ne Allahnmu.”
19 Amma Joshuwa ya ce wa mutanen, “Ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, gama shi Allah mai tsarki ne, mai kishi kuma, ba kuwa zai gafarta laifofinku da zunubanku ba.
20 Idan kun rabu da Ubangiji, kun bauta wa gumaka, sai ya juyo ya wulakanta ku, ya hallaka ku, ko da yake ya riga ya nuna muku alheri.”
21 Jama’a kuwa suka ce wa Joshuwa, “A’a, mu dai za mu bauta wa Ubangiji ne.”
22 Joshuwa kuma ya ce wa mutanen, “Ku ne shaidun kanku da kanku, kun zaɓi Ubangiji don ku bauta masa.”
Sai suka ce, “I, mu ne shaidu.”
23 Joshuwa ya ce, “To, ku kawar da gumakan da suke cikinku, ku sa zuciyarku ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.”
24 Jama’a suka ce wa Joshuwa, “Za mu bauta wa Ubangiji Allahnmu, za mu kuma yi biyayya da muryarsa.”
25 A wannan rana, Joshuwa ya yi alkawari da jama’a a Shekem, ya kafa musu dokoki da ka’idodi.
26 Ya kuwa rubuta waɗannan kalmomi a littafin Shari’ar Ubangiji. Ya kuma ɗauki wani babban dutse, ya kafa a ƙarƙashin itacen oak a wuri mai tsarki na Ubangiji.
27 Sai ya ce wa jama’a, “Wannan dutse shi ne shaida a kanmu, gama ya ji dukan abin da Ubangiji ya faɗa mana, domin haka zai zama shaida a kanku, don kada ku yi wa Allahnku ƙarya.”
28 Joshuwa kuwa ya sallami jama’ar, kowane mutum ya koma wurin gādonsa.
Rasuwar Joshuwa da ta Ele’azara
29 Bayan waɗannan al’amura, sai Joshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya rasu yana da shekara ɗari da goma da haihuwa.
30 Suka binne shi a ƙasar gādonsa a Timnat-sera wadda take cikin karkarar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga’ash.
31 Isra’ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji a dukan zamanin Joshuwa, da dukan zamanin dattawan da suka wanzu bayansa, waɗanda suka san dukan ayyukan da Ubangiji ya aikata domin Isra’ilawa.
32 Kasusuwan Yusufu, waɗanda jama’ar Isra’ila suka kawo daga Masar, an binne su a Shekem a yankin ƙasar da Yakubu ya saya a bakin azurfa ɗari daga wurin ‘ya’yan Hamor mahaifin Shekem. Wurin ya zama gādon zuriyar Yusufu.
33 Ele’azara, ɗan Haruna kuma ya rasu, aka binne shi a Gebeya a garin ɗansa, Finehas, wanda aka ba shi a ƙasar tuddai ta Ifraimu.