L. FIR 15

Ƙazanturwar Namiji ko Mace

1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka’idodi

2 domin jama’ar Isra’ila. Duk lokacin da wani namiji yake ɗiga daga al’aurarsa, ƙazantacce ne.

3 Ko al’aurar tana ɗiga ko ta daina shi dai ƙazantacce ne.

4 Kowane gado da mai ɗigan ya kwanta a kai ya ƙazantu, da kowane abu da ya zauna a kai ya ƙazantu.

5 Duk wanda ya taɓa gadonsa, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

6 Duk wanda kuma ya zauna a kan kowane abin da mai ɗigar ya zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

7 Wanda kuma ya taɓa jikin mai ɗigar, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

8 Idan mai ɗigar ya tofar da yau a kan wanda yake da tsabta, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

9 Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu.

10 Duk wanda ya taɓa kowane abin da yake ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har maraice, duk kuma wanda ya ɗauki wannan abu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

11 Duk wanda kuma mai ɗigar ya taɓa da hannunsa da bai wanke ba, sai wanda aka taɓa ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

12 Kaskon da mai ɗigar ya taɓa, sai a fasa shi, amma idan akushi ne sai a wanke shi da ruwa.

13 Sa’ad da mai ɗigar ya warke, sai ya ƙidaya ranaku bakwai don tsarkakewarsa, ya wanke tufafinsa, ya yi wanka a ruwa mai gudu, zai tsarkaka.

14 A kan rana ta takwas zai kawo kurciyoyi biyu, ko ‘yan tattabarai biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada, ya ba firist.

15 Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa.

16 Idan maniyyin mutum ya zubo, sai ya wanke jikinsa duka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

17 Kowace riga ko fatar da maniyyin ya taɓa, sai a wanke da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

18 Idan mutum ya kwana da mace, sai su yi wanka da ruwa, sun ƙazantu har maraice.

19 Sa’ad da mace take haila irin ta ka’ida, za ta ƙazantu har kwana bakwai, duk wanda ya taɓa ta kuwa zai ƙazantu har maraice.

20 Duk abin da ta kwana a kai a lokacin rashin tsarkinta zai ƙazantu, haka kuma abin da ta zauna a kai zai ƙazantu.

21 Wanda kuma ya taɓa gadonta, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

22 Haka kuma duk wanda ya taɓa kowane abin da ta zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

23 Ko gado ne, ko kuma kowane abin da ta zauna a kai, sa’ad da wani ya taɓa shi zai ƙazantu har maraice.

24 Idan kuma wani ya kwana da ita, rashin tsarkinta zai shafe shi. Zai zama marar tsarki har kwana bakwai. Kowane gado da ya kwanta a kai zai ƙazantu.

25 Idan zubar jinin hailar macen ya yi kwanaki da yawa, ko kuwa kwanakin hailarta sun zarce ka’ida, a duk kwanakin zubar jininta za ta lizima cikin rashin tsarki daidai kamar lokacin hailarta.

26 Kowane gado da ta kwanta a kai a kwanakin zubar jininta, zai zama ƙazantacce, daidai kamar lokacin hailarta. Kowane abin da ta zauna a kai zai ƙazantu kamar a lokacin hailarta.

27 Wanda duk ya taɓa waɗannan abubuwa zai ƙazantu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

28 Bayan da hailarta ta tsaya, za ta ƙidaya kwanaki bakwai, bayan haka za ta tsarkaka.

29 A rana ta takwas sai ta kawo ‘yan kurciyoyi biyu, ko ‘yan tattabarai, a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada.

30 Firist ɗin zai miƙa ɗaya hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda rashin tsarkinta.

31 Ta haka za ka tsarkake jama’ar Isra’ila daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da alfarwata wadda take tsakiyarsu.

32 Waɗannan su ne ka’idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi, ƙazantacce ne.

33 Haka kuma wadda take haila, da kowane namiji ko mace, da yake ɗiga, da namijin da ya kwana da mace marar tsarki.