L. FIR 23

Ƙayyadaddun Idodi

1 Ubangiji ya ba Musa

2 waɗannan ka’idodi domin ƙayyadaddun idodi sa’a da Isra’ilawa za su taru domin yin sujada.

3 Cikin kwanaki shida za a yi aiki, amma a rana ta bakwai za a huta ɗungum, gama ranar Asabar ce, tsattsarka. Ko kaɗan ba za a yi aiki a ranar ba a duk inda suke, amma ku yi taruwa ta sujada gama ranar Asabar ta Ubangiji ce.

4 Su yi waɗannan idodi a ƙayyadaddun lokatai.

Idin Ƙetarewa da na Abinci Marar Yisti

5 Da maraice a rana ta goma sha huɗu ga watan fari, ita ce ranar Idin Ƙetarewa ta Ubangiji.

6 Sa’an nan kuma sha biyar ga watan za a yi bikin idin abinci marar yisti na Ubangiji. Za su ci abinci marar yisti har kwana bakwai.

7 Za su yi muhimmin taro a rana ta fari. Ba za su yi aiki mai wuya a ranar ba.

8 A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa kowace rana ga Ubangiji. Za su kuma yi muhimmin taro a rana ta bakwai ɗin. Ba za su yi aiki mai wuya ba.

9 Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

10 lokacin da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, sai su kawo wa firist dami na fari na amfanin gonakinsu.

11 Firist ɗin zai kaɗa damin hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, don a karɓe su. Firist zai kaɗa hadayar a kashegarin Asabar.

12 A ranar da suka miƙa hadaya ta kaɗawa, za su kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da ɗan rago bana ɗaya marar lahani.

13 Tare da wannan hadaya kuma, za su miƙa hadaya ta gari, humushi biyu na garwar gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Za su kuma miƙa hadaya ta sha da ruwan inabi kwalaba ɗaya.

14 Kada su ci sabon hatsin, wanda aka tuma, ko ɗanyensa, ko wanda aka yi gurasa da shi sai sun kawo hadayarsu ta sabon hatsi ga Allah. Za su kiyaye wannan ka’ida, da su da dukan zuriyarsu, har dukan zamanai masu zuwa.

Idin Girbi

15 Za su ƙidaya mako bakwai daga kashegarin Asabar da suka kawo damin hadaya ta kaɗawa domin miƙa wa Ubangiji.

16 Kwana hamsin za su ƙirga zuwa kashegarin Asabar ta bakwai ɗin. Sa’an nan sai su kawo hadaya ta sabon hatsi ga Ubangiji.

17 Za su kawo malmala biyu na abinci da za a kaɗa daga inda suke domin a miƙa su ga Ubangiji. Za a yi malmalan da rabin garwar gari mai laushi. Za a sa wa garin yisti, sa’an nan a toya. Hadaya ta ‘ya’yan fari ke nan ga Ubangiji.

18 Za su kuma miƙa ‘yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani, da bijimi ɗaya, da raguna biyu tare da abincin. Za a yi hadaya ta ƙonawa da su ga Ubangiji, tare da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, wato, hadaya ta ƙonawa da wuta, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

19 Za su miƙa hadaya ta zunubi da bunsuru ɗaya, da ‘yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya don hadaya ta salama.

20 Firist zai kaɗa su tare da abinci na nunan fari domin hadaya ta kaɗawa, da ‘yan ragunan nan biyu a gaban Ubangiji. Za su zama tsarkakakku ga Ubangiji domin a ba firist.

21 A ranar fa za su yi shela don a yi muhimmin taro. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Wannan doka ce gare su har abada a inda suke duka.

22 Sa’ad da suka girbe amfanin gonakinsu, ba za su girbe har da gyaffan gonakinsu ba, ba kuma za su yi kalar amfanin gonakinsu ba. Za su bar wa matalauta da baƙi. Shi ne Ubangiji Allahnsu.

Idin Sabuwar Shekara

23 Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

24 ya ce wa Isra’ilawa su mai da rana ta fari ga wata na bakwai ta zama ranar hutu musamman, sa’ad da za su ji busar ƙaho, sai su taru domin yin sujada.

25 Ba za su yi aiki mai wuya ba. Za su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.

Ranar Kafara

26 Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

27 rana ta goma ga watan bakwai za ta zama rana ta yin kafara da lokacin yin muhimmin taro. Kada su ci abinci a ranar, su taru su yi sujada, su miƙa hadaya taƙonawa ga Ubangiji.

28 Ba za su yi aiki a wannan rana ba, gama rana ce ta yin kafara dominsu.

29 Duk wanda ya ci abinci a wannan rana ba za a lasafta shi ɗaya daga cikin jama’ar Allah ba.

30 Duk kuma wanda ya yi aiki a wannan rana, Ubangiji kansa zai kashe shi.

31 Wannan ka’ida ta shafi dukan zuriyarsu a duk inda suke.

32 Daga faɗuwar ranar tara ga watan, har zuwa faɗuwar ranar goma ga watan, su kiyaye wannan ta zama ranar hutu musamman. A wannan lokaci ba wanda zai ci abinci.

Idin Bukkoki

33 Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce ya faɗa wa Isra’ilawa, cewa,

34 a rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi Idin Bukkoki kwana bakwai saboda Ubangiji.

35 Za a yi muhimmin taro na sujada a rana ta fari. Ba za su yi aiki ba.

36 A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. A rana ta takwas kuma sai su yi muhimmin taro na sujada, su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Rana ce ta yin sujada, kada su yi aiki.

37 Waɗannan su ne ƙayyadaddun idodi na Ubangiji da za su riƙa yi domin sujada. Za su miƙa hadayu ga Ubangiji, wato, hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da ta sadakoki, da hadayu na sha. Za a miƙa kowace hadaya a ranarta.

38 Waɗannan idodi ƙari ne a kan lokatan sujada da aka saba, hadayun kuma ƙari ne a kan kyautan da aka saba bayarwa, kamar su hadaya don cika wa’adi, da hadaya ta yardar rai da suke bayarwa ga Ubangiji.

39 A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai, bayan da sun gama tattara amfanin gonakinsu, sai su yi idi ga Ubangiji har kwana bakwai. Rana ta fari, da rana ta takwas za su zama muhimman ranakun hutawa.

40 A ranar sai su ɗibi ‘ya’yan itatuwa masu kyau, da rassan dabino, da kauraran rassan itatuwa masu ganye, da itacen wardi na rafi, sa’an nan su nuna bangirma gaban Ubangiji Allahnsu har kwana bakwai.

41 Za su yi idin nan ga Ubangiji har kwana bakwai. Wannan ka’ida ce a gare su har abada.

42 Za su zauna cikin bukkoki har kwana bakwai. Duk ‘yan ƙasa waɗanda suke Isra’ilawa za su zauna cikin bukkoki.

43 Don zuriyarsu ta sani Ubangiji ya sa Isra’ilawa su zauna cikin bukkoki, sa’ad da ya fito da su daga ƙasar Masar. Shi ne Ubangiji Allahnsu.

44 Haka kuwa Musa ya sanar wa mutanen Isra’ila da ƙayyadaddun idodin Ubangiji.