Ubangiji zai Ba su Nama
1 Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai, wutarsa ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone wani gefe na zangon.
2 Sai mutanen suka yi ta yi wa Musa kuka, Musa kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu.
3 Aka sa wa wurin suna Tabera, wato matoya, domin wutar Ubangiji ta yi ƙuna a cikinsu.
4 Tattarmukan da suke cikinsu kuwa suka faye kwaɗayin nama, har Isra’ilawa ma da kansu suka fara gunaguni suna cewa, “Wa zai ba mu nama mu ci?
5 Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, da su kakamba, wato wani irin kayan lambu ne mai yaɗuwa, da guna, da sāfa, da albasa, da tafarnuwa.
6 Yanzu ranmu ya yi yaushi, ba wani abu, sai dai wannan manna muke gani.”
7 Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuwa kamar na ƙāro ne.
8 Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa, ko kuwa su daka, su dafa, su yi waina da ita. Dandanar wainar tana kamar wadda aka yi da mai.
9 Manna takan zubo tare da raɓa da dad dare a zangon.
10 Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko’ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar alfarwarsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai.
11 Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Don me ka wahalar da bawanka? Me ya sa ban sami tagomashi a gare ka ba, da ka jibga wahalar dukan mutanen nan a kaina?
12 Ni na ɗauki cikinsu? Ko kuwa ni ne na haife su, har da za ka ce mini, ‘Ka ɗauke su a ƙirjinka, kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka rantse za ka bai wa kakanninsu?’
13 A ina zan samo nama da zan ba wannan jama’a duka? Gama suna ta gunaguni a gabana, suna cewa, ‘Ba mu nama mu ci.’
14 Ba zan iya ɗaukar nawayar mutanen nan ni kaɗai ba, gama nauyin ya fi ƙarfina.
15 Idan haka za ka yi da ni, ina roƙonka ka kashe ni, idan na sami tagomashi a gare ka, don kada in rayu in ga wannan baƙin ciki.”
16 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tattaro mini mutum saba’in daga cikin dattawan Isra’ila waɗanda aka sani su ne dattawa da shugabannin jama’ar, ka kawo su a alfarwa ta sujada, ka sa su tsaya tare da kai.
17 Ni kuwa zan sauko, in yi magana da kai a can. Zan ɗiba daga cikin ruhun da yake cikinka, in ba su. Su kuma za su ɗauki nawayar jama’ar tare da kai, domin kada ka ɗauki nawayar kai kaɗai.
18 Ka ce wa jama’ar, su tsarkake kansu don gobe, za su ci nama, gama Ubangiji ya ji gunagunin da suka yi, da suka ce, ‘Wa zai ba mu nama mu ci? Ai, zama cikin Masar ya fi mana.’ Domin haka Ubangiji zai ba su nama, za su kuwa ci.
19 Ba ma don kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko ashirin kaɗai za su ci ba.
20 Amma har wata guda cur. Za su ci har ya gundure su, ya zama musu abin ƙyama saboda sun ƙi Ubangiji wanda yake tare da su, suka yi gunaguni a gabansa , suna cewa, ‘Me ya sa ma, muka fito Masar?’ ”
21 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutum dubu ɗari shida (600,000) ne suke tafe tare da ni, ga shi kuwa, ka ce za ka ba su nama, za su ci har wata guda cur.
22 Za a yanyanka musu garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu, don su ishe su? Ko kuwa za a tattara musu dukan kifayen teku don su ishe su?”
23 Sai Ubangiji ya amsa wa Musa, “Ikon Ubangiji ya gaza ne? Yanzu za ka gani ko maganata gaskiya ce, ko ba gaskiya ba ce.”
Shugabanni sun yi Annabci
24 Musa kuwa ya fita, ya faɗa wa jama’a maganar Ubangiji, ya kuma tattara dattawa saba’in daga cikin jama’ar, ya sa su tsaya kewaye da alfarwar.
25 Sa’an nan Ubangiji ya sauko cikin girgije, ya yi masa magana, ya kuma sa ruhun da yake kansa, ya zama a kan dattawan nan saba’in. Sa’ad da ruhun ya zauna a kansu sai suka yi annabci, amma daga wannan kuma ba su ƙara yi ba.
26 Akwai mutum biyu da suka ragu a zangon, sunan ɗayan Eldad, ɗayan kuwa Medad. Ruhun kuma ya zauna a kansu gama suna cikin dattawan nan da aka lasafta, amma ba su fita zuwa alfarwa ba, sai suka yi annabci a zangon.
27 Sai wani saurayi ya sheƙa a guje ya faɗa wa Musa, ya ce, “Ga Eldad da Medad suna nan suna annabci a cikin zangon.”
28 Joshuwa ɗan Nun, mai yi wa Musa barantaka, ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun, ya ce, “Ya shugabana, Musa, ka hana su.”
29 Amma Musa ya ce masa, “Kishi kake yi domina? Da ma jama’ar Ubangiji duka annabawa ne, har ma ya sa Ruhunsa a cikinsu!”
30 Sai Musa da dattawan Isra’ila suka koma zango.
Ubangiji ya Aiko da Makware
31 Sai iska ta huro daga wurin Ubangiji, ta koro makware daga teku, ta bar su birjik kusa da zango, misalin nisan tafiyar yini guda ta kowace fuska. Tsayin tashinsu daga ƙasa misalin kamu biyu ne.
32 Sai mutane suka tashi suka yi ta tattara makware dukan wannan yini, da dukan dare, har kashegari duka. Wanda ya tattara kaɗan, ya tara garwa metan. Suka shanya abinsu kewaye da zangon.
33 Tun suna cikin cin naman, sai Ubangiji ya husata da mutanensa, ya bugi jama’a da annoba mai zafi.
34 Don haka aka sa wa wurin suna Kibrot-hata’awa, wato makabarta, gama a can ne aka binne mutanen nan makwaɗaita.
35 Daga Kibrot-hata’awa mutanen suka yi tafiya zuwa Hazerot, a can suka sauka.