Aka Hukunta Maryamu
1 Sai Maryamu da Haruna suka zargi Musa saboda mace, Bahabashiya, wadda ya aura.
2 Suka ce, “Da Musa kaɗai ne, Ubangiji ya yi magana, bai yi magana da mu kuma ba?” Ubangiji kuwa ya ji.
3 (Musa dai mai tawali’u ne ƙwarai, fiye da kowane mutum a duniya.)
4 Farat ɗaya sai Ubangijiya ce wa Musa, da Haruna, da Maryamu, “Ku uku, ku tafi zuwa alfarwa ta sujada.” Sai su uku suka tafi.
5 Ubangiji kuwa ya zo cikin al’amudin girgije, ya tsaya a ƙofar alfarwar, ya yi kira, “Haruna! Maryamu!” Su biyu fa suka gusa gaba.
6 Ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa! Idan akwai annabawa a cikinku, nakan bayyana gare su cikin wahayi, in kuma yi magana da su ta cikin mafarki.
7 Ba haka nake magana da bawana Musa ba, na sa shi ya lura da dukkan jama’ata Isra’ila.
8 Nakan yi magana da shi fuska da fuska a sarari, ba a duhunce ba. Yakan kuma ga zatina. Me ya sa ba ku ji tsoron zargin bawana Musa ba?”
9 Ubangiji kuwa ya husata da su, ya rabu da su.
10 Sa’ad da al’amudin girgijen ya tashi daga kan alfarwar, sai ga Maryamu ta kuturce, fari fat kamar auduga. Da Haruna ya juya wajen Maryamu, ya ga ta zama kuturwa.
11 Sai ya ce wa Musa, “Ya shugabana, ina roƙonka, kada ka hukunta mu saboda wannan zunubi, mun yi aikin wauta.
12 Na roƙe ka kada ka bari ta zama kamar matacce wanda rabin jikinsa ruɓaɓɓe ne a lokacin da aka haife shi.”
13 Sai Musa ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ya Allah, ka warkar da ita.”
14 Amma ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata yau a fuskarta, ba za ta ji kunya har kwana bakwai ba? Bari a fitar da ita a bayan zangon kwana bakwai, bayan haka a shigar da ita.”
15 Aka fitar da Maryamu a bayan zangon har kwana bakwai. Jama’ar kuwa ba su ci gaba da tafiya ba, sai da aka shigar da Maryamu a zangon.
16 Bayan wannan jama’a suka tashi daga Hazerot suka sauka a jejin Faran.