‘Yan Leƙen Asirin Ƙasa
1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
2 “Ka aiki mutane su leƙi asirin ƙasar Kan’ana wadda nake ba Isra’ilawa. Daga kowace kabila na kakanninsu, ka zaɓi mutum guda wanda yake shugaba a cikinsu.”
3-15 Musa kuwa ya yi biyayya, daga jejin Faran ya aika da waɗannan shugabanni,
Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ra’ubainu.
Shafat ɗan Hori, daga kabilar Saminu.
Kalibu ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuza.
Igal ɗan Yusufu, daga kabilar Issaka.
Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Ifraimu.
Falti ɗan Rafu, daga kabilar Biliyaminu.
Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zabaluna.
Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manassa.
Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan.
Setur ɗan Maikel, daga kabilar Ashiru.
Nabi ɗan Wofsi,daga kabilar Naftali.
Geyuwel ɗan Maci,daga kabilar Gad.
16 Waɗannan su ne mutanen da Musa ya aika su leƙo asirin ƙasar. Amma Musa ya ba Hosheya, ɗan Nun, suna Joshuwa.
17 Sa’ad da Musa ya aike su leƙen asirin ƙasar Kan’ana, ya ce musu, “Ku haura, ku bi ta Negeb har zuwa ƙasar tuddai,
18 ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanenta ƙarfafa ne, ko raunana ne, ko su kima ne, ko kuwa suna da yawa,
19 ko ƙasa tasu mai ni’ima ce, ko babu, ko biranensu marasa garu ne, ko masu garu ne,
20 ko ƙasar tana da wadata,ko matalauciya ce, ko ƙasar kurmi ce, ko fili. Ku yi jaruntaka, ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Gama lokacin farkon nunan inabi ne.)
21 Sai suka haura, suka leƙo asirin ƙasar tun daga jejin Zin har zuwa Rehob kusa da Hamat.
22 Suka haura ta wajen Negeb, suka isa Hebron inda Ahimaniyawa, da Sheshaiyawa, da Talmaiyawa, zuriyar ƙarfafan mutanen da ake kira Anakawa suke zaune. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)
23 Da suka isa Kwarin Eshkol, sai suka datse reshe guda na nonon inabi da ‘ya’ya cunkus. Suka rataya a sanda, mutum biyu suka ɗauka a kafaɗunsu. Suka kuma kawo rumman da ɓaure.
24 Aka kira wurin Kwarin Eshkol, wato “nonon inabi,” saboda nonon inabi wanda ‘yan leƙen ƙasa suka yanko a wurin.
25 Bayan sun yi kwana arba’in suna leƙen asirin ƙasar, sai suka komo.
26 Suka zo wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama’ar Isra’ila a jejin Faran a Kadesh. Suka faɗa musu labarin tafiyarsu, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar da suka kawo.
27 Suka ce wa Musa, “Mun tafi ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana da yalwar abinci, ga kuma amfanin ƙasar.
28 Amma mazaunan ƙasar ƙarfafa ne, biranenta kuma manya ne, masu garu, banda wannan kuma, mun ga Anakawa a can.
29 Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan’aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.”
30 Amma Kalibu ya sa mutane su yi shiru a gaban Musa, ya ce, “Bari mu tafi nan da nan mu mallaki ƙasar, gama za mu iya cinta.”
31 Sai mutanen da suka tafi tare da shi suka amsa suka ce, “Ba za mu iya haurawa, mu kara da mutanen ba, gama sun fi mu ƙarfi.”
32 Haka suka kawo wa ‘yan’uwansu, Isra’ilawa, mugun rahoton ƙasa wadda suka leƙi asirinta, suka ƙara da cewa, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zaune a cikinta, dukan mutane kuma da muka gani a cikinta ƙatti ne.
33 Mun kuma ga manyan mutane a can, wato mutanen Anakawa da suka fito daga Nefilawa. Sai muka ga kanmu kamar fara ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”