Mutane suka yi Yaji
1 Sai dukan taron jama’a suka yi kuka da babbar murya dukan dare saboda wahala.
2 Dukan Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suke ce, “Da ma mun mutu a ƙasar Masar, ko kuwa a wannan jeji.
3 Me ya sa Ubangiji ya kawo mu a wannan ƙasa, mu mutu da takobi? Matanmu da ƙanananmu za su zama ganima. Ba zai fi mana kyau, mu koma Masar ba?”
4 Sai suka ce wa juna, “Bari mu shugabantar da wani, mu koma Masar.”
5 Sa’an nan Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban dukan taron jama’ar Isra’ilawa.
6 Sai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne waɗanda suke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu.
7 Suka ce wa dukan taron jama’ar Isra’ilawa, “Ƙasar da muka ratsa ta don mu leƙi asirinta, ƙasa ce mai kyau ƙwarai da gaske.
8 Idan Ubangiji yana jin daɗinmu zai kai mu a wannan ƙasa da take cike da yalwar abinci, ya ba mu ita.
9 Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji, kada kuwa ku ji tsoron mutanen ƙasar. Za mu ci su ba wuya, Ubangiji kuma zai lalatar da gumakansu da suke kāre su. Ubangiji kuwa yana tare da mu, kada ku ji tsoronsu.”
10 Amma taron jama’a suka ce za su jajjefe su da duwatsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutanen Isra’ila daga cikin alfarwa ta sujada.
11 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su raina ni? Har yaushe za su ƙi gaskata ni, ko da yake na aikata alamu a tsakiyarsu?
12 Zan kashe su da annoba, in raba su da gādonsu. Zan yi wata al’umma da kai, wadda za ta fi su girma da iko.”
13 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji, gama ka fitar da mutanen daga cikinsu da ƙarfin ikonka.
14 Za su kuwa faɗa wa mutanen wannan ƙasa, gama sun riga sun ji, kai, ya Ubangiji, kana cikin tsakiyar jama’ar nan wadda kake bayyana kanka gare ta fuska da fuska. Girgijenka kuma yana tsaye a kansu, kakan kuma yi musu jagora da al’amudin wuta.
15 Idan kuwa ka kashe jama’ar nan gaba ɗaya, sai al’umman da suka ji labarinka, su ce,
16 ‘Domin Ubangiji ya kāsa kai jama’ar nan zuwa cikin ƙasar da ya rantse zai ba su, don haka ya kashe su a cikin jeji.’
17 Yanzu fa, ya Ubangiji, ina roƙonka ka sa ikonka ya zama da girma kamar yadda ka alkawarta cewa,
18 ‘Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, kana gafarta mugunta da laifi, amma ba za ka ƙyale mai laifi ba, gama kakan ɗora wa ‘ya’ya alhakin muguntar iyaye, har tsara ta uku da ta huɗu.’
19 Ina roƙonka ka gafarta muguntar wannan jama’a saboda ƙaunarka mai girma, kamar yadda kake gafarta musu tun daga Masar har zuwa yanzu.”
20 Sai Ubangiji ya ce, “Saboda maganarka na gafarta.
21 Amma, hakika, na rantse da zatina, kamar yadda ɗaukakata za ta cika duniya duka,
22 dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba,
23 ba za su ga ƙasar da na rantse zan ba kakanninsu ba. Duk waɗanda suka raina ni, ba za su ga ƙasar ba,
24 sai dai bawana Kalibu da yake ruhunsa dabam ne, gama ya bi ni sosai.
25 Yanzu fa, tun da yake Amalekawa da Kan’aniyawa suna zaune a kwarin, gobe sai ku juya ku nufi wajen jejin ta hanyar Bahar Maliya.”
Ubangiji ya Hukunta Jama’ar saboda Gunaguni
26 Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna,
27 “Har yaushe wannan mugun taron jama’a zai yi ta gunaguni a kaina? Na ji gunagunin da Isra’ilawa suka yi a kaina.
28 Sai ka faɗa musu cewa, ‘Ni Ubangiji na rantse da zatina, abin da kuka sanar da ni zan yi muku.
29 Gawawwakin waɗanda suka yi gunaguni a kaina za su fādi cikin jejin nan. Dukan waɗanda aka ƙidaya, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba,
30 ba wanda zai shiga ƙasar da na rantse ta zama wurin zamanku, sai Kalibu, ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.
31 Amma ‘yan ƙanananku, waɗanda kuka ce za su zama ganima, su ne zan kai su cikin ƙasar, za su san ƙasar da kuka raina.
32 Amma ku, gawawwakinku za su fāɗi a jejin.
33 ‘Ya’yanku za su yi yawo a jeji shekara arba’in, za su sha wahala saboda rashin bangaskiyarku, har mutuminku na ƙarshe ya mutu a jejin.
34 Bisa ga kwanakin nan arba’in da kuka leƙi asirin ƙasar, haka za ku ɗauki alhakin zunubanku shekara arba’in, gama kowane kwana a maimakon shekara yake. Ta haka za ku sani ban ji daɗin abin da kuka yi ba.
35 Ni Ubangiji na faɗa, hakika, haka zan yi da wannan mugun taron jama’ar da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su ƙare ƙaƙaf a wannan jeji, a nan za su mutu.’ ”
36 Mutanen da Musa ya aika su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama’a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar,
37 mutanen nan da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta kashe su a gaban Ubangiji.
38 Sai dai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne, kaɗai ne ba za su mutu ba daga cikin waɗanda suka tafi leƙen asirin ƙasar.
Ƙoƙarin Cin Ƙasar na Farko ya Kāsa
39 Da Musa ya faɗa wa Isra’ilawa abin da Ubangiji ya ce, sai jama’a suka yi baƙin ciki ƙwarai.
40 Suka tashi da sassafe, suka hau kan tudu, suna cewa, “Ga shi, a shirye muke mu tafi wurin da Ubangiji ya ambata, gama mun yi kuskure.”
41 Amma Musa ya ce, “Me ya sa kuke karya umarnin Ubangiji? Yin haka ba zai kawo nasara ba.
42 Kada ku haura domin kada ku sha ɗibga a gaban maƙiyanku, gama Ubangiji ba ya tare da ku.
43 Gama akwai Amalekawa da Kan’aniyawa a gabanku, za su kashe ku da takobi domin kun bar bin Ubangiji, don haka Ubangiji ba zai kasance tare da ku ba.”
44 Amma sai suka yi izgili, suka haura kan tudun, amma akwatin alkawari da Musa ba su bar zangon ba.
45 Sai Amalekawa da Kan’aniyawa, mazauna a kan tudun, suka gangaro, suka ci su, suka runtume su har Harma, wato hallakarwa.