L. KID 15

Ka’idodin Yin Hadayu

1 Ubangiji ya ba Musa

2 waɗannan ka’idodi domin Isra’ilawa su kiyaye su a ƙasar da zai ba su.

3 Sa’ad da za su yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji daga cikin garken shanu, ko na tumaki da awaki, ko hadaya ta ƙonawa ce, ko ta cika wa’adi ce, ko ta yardar rai ce, ko ta ƙayyadaddun idodinsu ce, don a ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji,

4 sai shi wanda ya kawo hadayar ga Ubangiji, ya kuma kawo hadaya ta gari, humushin garwa guda kwaɓaɓɓe da rubu’in moɗa na mai.

5 Ya kuma shirya hadaya ta sha, rubu’in moɗa ta ruwan inabi domin kowane ɗan rago na hadaya ta ƙonawa.

6 Idan kuwa da rago ne, a shirya hadaya ta gari humushi biyu na garwa, a kwaɓa da sulusin moɗa na mai.

7 Za a kuma miƙa hadaya ta sha da sulusin moɗa na ruwan inabi, don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

8 Idan kuwa da bijimi ne za a yi hadaya ta ƙonawar, ko sadaka domin cika wa’adi, ko ta salama ga Ubangiji,

9 sai a miƙa hadaya ta gari tare da bijimin, humushi uku na garwar gari kwaɓaɓɓe da rabin moɗa na mai.

10 Za a kuma miƙa hadaya ta sha da rabin moɗa na ruwan inabi. Hadaya ce da akan yi da wuta, mai yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

11 Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago,ko ɗan rago,ko bunsuru.

12 Bisa ga yawan abin da aka shirya, haka za a yi da kowannensu bisa ga adadinsu.

13 Haka dukan waɗanda suke ‘yan ƙasa za su yi in za su ba da hadayar da akan yi da wuta don yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

14 Idan baƙon da yake baƙunci a cikinsu ko ko wane ne da yake tare da su a dukan zamanansu, yana so ya ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, sai ya yi kamar yadda suke yi.

15 Ka’ida ɗaya ce domin taron jama’a da kuma baƙin da yake zaune tare da su. Ka’ida ce madawwamiya a dukan zamanansu. Kamar yadda suke a gaban Ubangiji, haka kuma baƙon da yake baƙunci a cikinsu yake.

16 Ka’ida ɗaya ce umarni kuma ɗaya ne domin su da baƙin da yake baƙunci a cikinsu.

17 Ubangiji ya ba Musa

18 waɗannan ka’idodi domin Isra’ilawa su kiyaye a ƙasar da zai ba su.

19 Sa’ad da suke cin amfaninta, sai su miƙa hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji.

20 Daga cikin ɓarzajjen hatsinsu na nunan fari sai su yi wainar da za su ɗaga don yin hadaya da amfanin masussuka.

21 Daga cikin ɓarzajjen hatsinsu na nunan fari, sai su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa a dukan zamanansu.

22 Amma idan sun yi kuskure, ba su kiyaye dukan umarnan nan waɗanda Ubangiji ya faɗa wa Musa ba,

23 wato duk dai abin da ubangiji ya umarta ta bakin Musa tun daga ranar da Ubangiji ya ba da umarnan, har zuwa dukan zamanansu,

24 idan jama’a sun yi kuskure da rashin sani, sai su miƙa maraƙi don yin hadaya ta ƙonawa don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Su kuma ba da hadaya ta gari, da hadaya ta sha tare da maraƙin bisa ga ka’idar. Za su kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi.

25 Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama’ar Isra’ilawa, za a kuwa gafarta musu kuskuren, domin sun kawo hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi ga Ubangiji saboda kuskurensu.

26 Za a gafarta wa dukan taron jama’ar Isra’ilawa da baƙon da yake baƙunci a cikinsu, kuskuren da suka yi.

27 Idan bisa ga kuskure wani mutum ya yi zunubi, sai ya ba da ‘yar akuya bana ɗaya ta yin hadaya don zunubi.

28 Firist kuwa zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin da ya yi kuskuren, gama ya yi zunubi ba da saninsa ba, za a kuwa gafarta masa.

29 Ka’idarsu ɗaya ce a kan wanda ya yi kuskure, ko Ba’isra’ile ne, ko baƙon da yake baƙunci a cikinsu.

30 Amma mutumin da ya yi laifi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙo ne, ya sāɓi Ubangiji, sai a kashe shi,

31 gama ya raina maganar Ubangiji, ya karya umarninsa. Hakika za a kashe mutumin nan, alhakin zunubinsa, yana wuyansa.

Jajjefewar Wanda ya Ɓata Ranar Asabar

32 Sa’ad da Isra’ilawa suke jeji, sai aka iske wani yana tattara itace a ranar Asabar.

33 Sai suka kai shi wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama’a.

34 Aka sa shi a gidan waƙafi domin ba a bayyana abin da za a yi da shi ba tukuna.

35 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “A kashe mutumin, dukan taron jama’a za su jajjefe shi da duwatsu a bayan zangon.”

36 Dukan taron jama’a suka kai shi bayan zangon, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Dokoki a kan Tuntayen Riguna

37 Ubangiji ya umarci Musa ya ce,

38 “Ka faɗa wa Isra’ilawa su yi wa shafin rigunansu tuntaye a dukan zamananku. A kan kowane tuntu, su sa shuɗin zare.

39 Tuntu zai zama musu abin dubawa don su riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji su aikata su, don kada su bi son zuciyarsu, da sha’awar idanunsu yadda suka taɓa yi.

40 Da haka za su riƙa tunawa, su aikata dukan umarnaina su zama tsarkakakku gare ni.

41 Gama ni ne Ubangiji Allahnku, na fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”