L. KID 22

Balak ya Sa a Kirawo masa Bal’amu

1 Isra’ilawa suka kama tafiya, suka yi zango a filayen Mowab a hayin Urdun daura da Yariko.

2 Balak ɗan Ziffor ya ga abin da Isra’ilawa suka yi wa Amoriyawa.

3 Sai Mowabawa suka firgita ƙwarai saboda yawan mutanen. Tsoron Isra’ilawa ya kama su.

4 Mowabawa kuwa suka ce wa dattawan Madayanawa, “Yanzun nan wannan taro zai lashe dukan abin da yake kewaye da mu kamar yadda sā yakan lashe ciyawar saura.” Don haka Balak ɗan Ziffor wanda yake sarautar Mowab a lokacin,

5 ya aiki manzanni zuwa wurin Bal’amu ɗan Beyor a Fetor, a ƙasar danginsa, wadda take kusa da kogin, su kirawo shi, su ce, “Ga mutane sun fito daga ƙasar Masar, sun mamaye ƙasar, ga shi, suna zaune daura da ni.

6 Ina roƙonka, ka zo yanzu, ka la’anta mini mutanen nan, gama sun fi ƙarfina, ko ya yiwu in ci su, in kore su daga ƙasar, gama na sani duk wanda ka sa wa albarka zai albarkatu,wanda kuwa ka la’anta, zai la’antu.”

7 Dattawan Mowab da na Madayana suka ɗauki kafin alkalami suka tafi wurin Bal’amu suka faɗa masa saƙon Balak.

8 Ya ce musu, “Ku kwana a nan, ni kuwa zan shaida muku abin da Ubangiji zai faɗa mini.” Sai dattawan Mowab suka zauna wurin Bal’amu.

9 Allah kuwa ya zo wurin Bal’amu ya ce masa, “Suwane ne mutanen da suke tare da kai?”

10 Sai Bal’amu ya ce wa Allah, “Ai, Balak ne ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya aiko ya ce mini,

11 ‘Ga jama’a sun fito daga Masar, sun mamaye ƙasar, ka zo, ka la’anta mini su, watakila zan iya yin yaƙi da su, in kore su!’ ”

12 Allah kuwa ya ce wa Bal’amu, “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa za ka la’anta su ba, gama albarkatattu ne su.”

13 Da safe Bal’amu ya tashi, ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, gama Ubangiji bai yarda mini in tafi tare da ku ba.”

14 Domin haka dattawan Mowab suka tashi, suka koma wurin Balak, suka ce masa, “Bal’amu bai yarda ya biyo mu ba.”

15 Sai Balak ya sāke aiken dattawa da yawa masu daraja fiye da na dā.

16 Suka je wurin Bal’amu, suka ce masa, “Ga abin da Balak ɗan Ziffor ya ce, ‘Kada ka bar wani abu ya hana ka zuwa wurina,

17 gama zan ɗaukaka ka ƙwarai, kome kuwa ka faɗa mini in yi, zan yi, ka zo ka la’anta mini wannan jama’a.’ ”

18 Amma Bal’amu ya amsa ya ce wa barorin Balak, “Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba.

19 Amma ina roƙonku ku kwana a nan yau har in san abin da Ubangiji zai faɗa mini.”

20 Sal Allah ya je wurin Bal’amu da dare, ya ce masa, “Idan mutanen nan sun zo kiranka ne, sai ka tashi, ka tafi tare da su, amma abin da na umarce ka kaɗai za ka yi.”

Mala’ika da Jakar Bal’amu

21 Da safe sai Bal’amu ya tashi ya yi wa jakarsa shimfiɗa, ya tafi tare da dattawan Mowab.

22 Allah kuwa ya husata don ya tafi, mala’ikan Ubangiji ya tsaya a hanya ya tarye shi. Shi kuwa yana tafe a bisa jakarsa tare da barorinsa biyu.

23 Da jakar ta ga mala’ikan Ubangiji yana tsaye kan hanya da takobi zare a hannunsa, sai ta kauce daga hanya, ta shiga saura. Bal’amu kuwa ya buge ta don ya komar da ita a hanyar.

24 Sai mala’ikan Ubangiji ya je, ya tsaya a inda hanyar ta yi matsatsi a tsakanin bangayen gonakin inabi.

25 Sa’ad da jakar ta ga mala’ikan Ubangiji, ta matsa a jikin bango, ta goge ƙafar Bal’amu ga bangon, sai ya sāke bugunta.

26 Mala’ikan Ubangiji kuma ya sha kanta, ya tsaya a ƙunƙuntaccen wuri inda ba wurin juyawa zuwa dama ko hagu.

27 Da jakar ta ga mala’ikan Ubangiji, sai ta kwanta a ƙafafun Bal’amu. Sai Bal’amu ya husata, ya bugi jakar da sandansa.

28 Ubangiji kuwa ya buɗe bakin jakar, ta ce wa Bal’amu, “Me na yi maka, da ka buge ni har sau uku?”

29 Bal’amu ya ce mata, “Domin kin shashantar da ni, da a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki.”

30 Sai jakar ta ce wa Bal’amu, “Ba ni ce jakarka ba wadda kake ta hawa dukan lokacin nan har zuwa yau? Na taɓa yi maka haka?”

Ya ce, “A’a.”

31 Ubangiji kuwa ya buɗe idanun Bal’amu, ya ga mala’ikan Ubangiji yana tsaye a hanya da takobi zāre a hannunsa. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki.

32 Mala’ikan Ubangiji kuwa ya ce masa, “Me ya sa ka bugi jakarka har sau uku? Na fito ne don inhana ka, gama hanyarka ba daidai ba ce a gabana.

33 Jakar ta gan ni, ta kauce mini har sau uku. Da ba ta kakuce mini ba, lalle da na kashe ka, in bar ta da rai.”

34 Sai Bal’amu ya ce wa mala’ikan Ubangiji, “Na yi zunubi, gama ban sa ka tsaya a hanya don ka tarye ni ba. Yanzu fa, idan ka ga mugun abu ne, to, sai in koma.”

35 Ubangiji kuwa ya ce wa Bal’amu, “Tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka shi kaɗai za ka faɗa.” Sai Bal’amu ya tafi tare da dattawan Balak.

Balak ya Marabci Bal’amu

36 Sa’ad da Balak ya ji Bal’amu ya zo, sai ya fito ya tarye shi a Ar, wato wani birni a bakin Kogin Arnon, a kan iyakar Mowab.

37 Sai Balak ya ce wa Bal’amu, “Ashe, ban aika a kirawo ka ba? Me ya sa ba ka zo wurina ba, sai yanzu? Ko ban isa in ɗaukaka ka ba ne?”

38 Bal’amu ya amsa wa Balak ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu! Ina da wani ikon yin wata magana ne? Maganar da Allah ya sa a bakina, ita zan faɗa, tilas.”

39 Sai Bal’amu ya tafi tare da Balak suka je Kiriyat-huzot.

40 Can Balak ya yi hadaya da shanu da tumaki, ya kuwa aika wa Bal’amu da dattawan da suke tare da shi.

41 Kashegari, sai Balak ya ɗauki Bal’amu ya kai shi kan Bamotba’al, daga can ya ga rubu’in mutanen.