1 Sai Bal’amu ya ce wa Balak, “Ka gina mini bagadai guda bakwai a nan, ka kawo mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”
2 Balak ya yi yadda Bal’amu ya faɗa masa. Balak da Bal’amu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.
3 Sai Bal’amu ya ce wa Balak, “Tsaya kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa zan tafi can, in ga ko Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Ya kuwa tafi wani faƙo a kan tudu.
Bal’amu ya sa wa Isra’ila Albarka
4 Da Ubangiji ya sadu da Bal’amu, sai Bal’amu ya ce wa Ubangiji, “Na riga na shirya bagadai bakwai, na kuwa miƙa bijimi guda da rago guda a kan kowane bagade.”
5 Ubangiji kuwa ya sa magana a bakin Bal’amu ya ce, “Koma wurin Balak, ka faɗa masa abin da na faɗa maka.”
6 Sai ya koma wurin Balak, ya same shi da dukan dattawan Mowab suna tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa.
7 Bal’amu kuwa ya faɗi jawabinsa, ya ce
“Tun daga Aram Balak ya kawo ni,
Shi Sarkin Mowab ne daga gabashin duwatsu.
‘Zo, la’anta mini Yakubu,
Zo, ka tsine wa Isra’ila!’
8 Ƙaƙa zan iya la’anta wanda Allah bai la’antar ba?
Ƙaƙa zan iya tsine wa wanda Ubangiji bai tsine wa ba?
9 Gama daga kan duwatsu na gan su,
Daga bisa kan tuddai na hange su,
Jama’a ce wadda take zaune ita kaɗai,
Sun sani sun sami albarka fiye da sauran al’ummai.
10 Wa zai iya ƙidaya yawan Isra’ilawa da suke kamar ƙura?
Yawansu ya fi gaban lasaftawa.
Bari ƙarshena ya zama kamar ɗaya daga cikin mutane Allah,
Bari in mutu cikin salama kamar adalai.”
11 Sai Balak ya ce wa Bal’amu, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka domin ka la’anta abokan gābana, ga shi, sai albarka kake sa musu!”
12 Bal’amu kuwa ya ce, “Ai, ba tilas ne in hurta abin da Ubangiji ya sa a bakina ba?”
13 Sai Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su. Waɗanda suka fi kusa kaɗai ne za ka gani, amma ba za ka iya ganinsu duka ba. Ka la’anta mini su daga can.”
14 Ya kuwa kai shi saurar Zofim a bisa Dutsen Fisga. Sa’an nan ya gina bagadai bakwai, ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.
15 Sai Bal’amu ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa in tafi in sadu da Ubangiji a can.”
16 Ubangiji kuwa ya sadu da Bal’amu ya sa masa magana a baka, ya ce, “Koma wurin Balak ka faɗa masa abin da na faɗa maka.”
17 Sai Bal’amu ya koma wurin Balak ya same shi yana tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa tare da dattawan Mowab. Balak kuwa ya ce masa, “Me Ubangiji ya faɗa?”
18 Sai Bal’amu ya faɗi jawabinsa, ya ce,
“Tashi, Balak, ka ji,
Ka kasa kunne gare ni, ya ɗan Ziffor.
19 Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya,
Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba.
Zai cika dukan abin da ya alkawarta,
Ya hurta, ya kuwa cika.
20 Ga shi, an umarce ni in sa albarka.
Ya sa albarka, ba zan iya janye ta ba.
21 Bai ga mugunta ga Yakubu ba,
Bai kuma ga wahala a Isra’ilawa ba.
Ubangiji Allahnsu yana tare da su,
Suna sowar murna domin shi sarkinsu ne.
22 Allah ne ya fisshe shi daga Masar,
Ya yi yaƙi dominsu kamar kutunkun ɓauna.
23 Ba wata maitar da za ta cuci Yakubu,
Ba kuwa sihirin da zai cuci Isra’ilawa.
Yanzu za a ce, ‘Duba irin abin da Allah ya yi domin Yakubu, wato Isra’ilawa!’
24 Ga shi, jama’ar Isra’ila tana kama da ƙaƙƙarfan zaki,
Ba zai kwanta ba sai ya cinye ganimarsa.
Ya lashe jinin waɗanda ya kashe.”
25 Sai Balak ya ce wa Bal’amu, “Kada ka la’anta su, kada kuma ka sa musu albarka.”
26 Bal’amu kuwa ya amsa wa Balak, ya ce, “Ban faɗa maka ba, duk abin da Ubangiji ya faɗa, shi ne zan yi?”
27 Sai Balak ya ce wa Bal’amu, “In ka yarda ka zo in kai ka wani wuri, watakila Allah zai yarda ka la’anta mini su a can.”
28 Balak kuwa ya kai Bal’amu a ƙwanƙolin Dutsen Feyor wanda yake fuskantar hamada.
29 Sai Bal’amu ya ce wa Balak, “Ka gina mini bagadai bakwai, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”
30 Balak ya yi yadda Bal’amu ya faɗa masa. Ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.