Ƙidaya ta Biyu
1 Bayan annobar, sai Ubangiji ya ce wa Musa da Ele’azara, ɗan Haruna, firist,
2 “Ku ƙidaya dukan taron jama’ar Isra’ila tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba bisa ga gidajen ubanninsu. Ku ƙidaya duk wanda ya isa zuwa yaƙi a cikin Isra’ilawa.”
3 Sai Musa da Ele’azara, firist, suka yi musu magana a filayen Mowab daura da Yariko, suka ce,
4 “A ƙidaya mutane tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba kamar yadda Ubangiji ya umarta.”
Isra’ilawa waɗanda suka fita daga ƙasar Masar ke nan.
5 Ra’ubainu shi ne ɗan fari na Yakubu. ‘Ya’yan Ra’ubainu, maza, su ne Hanok, da Fallu,
6 da Hesruna, da Karmi.
7 Waɗannan yawansu ya kai dubu arba’in da uku da ɗari bakwai da talatin (43,730).
8 Fallu ya haifi Eliyab.
9 ‘Ya’yan Eliyab, maza su ne Yemuwel, da Datan, da Abiram. Datan da Abiram ne aka zaɓa daga cikin taron jama’ar, suna cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Musa da Haruna, har ma da Ubangiji.
10 Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora. Wuta kuma ta cinye sauran mutanen ƙungiyar, mutum ɗari biyu da hamsin suka mutu. Suka zama abin faɗakarwa.
11 Amma ‘ya’yan Kora ba su mutu ba.
12 ‘Ya’yan Saminu, maza, bisa ga iyalansu, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin,
13 da Zohar, da Shawul. Waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu.
14 Yawansu ya kai mutum dubu ashirin da biyu da ɗari biyu (22,200).
15 Zuriyar Gad bisa ga iyalansu, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni,
16 da Ezbon, da Eri,
17 da Arodi, da Areli.
18 Waɗannan su ne iyalan kabilar Gad. Yawan mutanensu ya kai dubu arba’in da ɗari biyar (40,500).
19 Kabilar Yahuza ke nan, (Er, da Onan, ‘ya’yan Yahuza sun mutu a ƙasar Kan’ana).
20 Sauran ‘ya’yansa bisa ga iyalansu su ne, Shela, da Feresa, da Zera,
21 da Hesruna, da Hamul.
22 Waɗannan su ne iyalan kabilar Yahuza. Yawan mutanensu ya kai dubu saba’in da shida da ɗari biyar (76,500).
23 Kabilar Issaka ke nan bisa ga iyalansu, da Tola, da Fuwa,
24 da Yashub, da Shimron.
25 Waɗannan su ne iyalan kabilar Issaka. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da huɗu da ɗari uku (64,300).
26 Kabilar Zabaluna ke nan bisa ga iyalansu, Sered, da Elon, da Yaleyel.
27 Waɗannan su ne iyalan kabilar Zabaluna. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da ɗari biyar (60,500).
28 Kabilar Yusufu ke nan bisa ga iyalansu, wato Manassa da Ifraimu.
29 Kabilar Manassa, su ne Makir ɗan Manassa. Makir ya haifi Gileyad wanda ya zama tushen zuriyar Gileyad.
30 ‘Ya’yan Gileyad, maza su ne Abiyezer, da Helek,
31 da Asriyel, da Shekem,
32 da Shemida, da Hefer.
33 Zelofehad, ɗan Hefer, ba shi da ‘ya’ya maza, sai dai ‘ya’ya mata. Sunayen ‘ya’yansa mata su ne Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.
34 Waɗannan su ne iyalan kabilar Manassa. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da biyu da ɗari bakwai (52,700).
35 Waɗannan su ne kabilar Ifraimu bisa ga iyalansu, Shutela, da Beker, da Tahat.
36 Iyalin Eran suna lasafta kansu, daga zuriyar Shutela ne.
37 Waɗannan su ne iyalan kabilar Ifraimu. Yawansu ya kai dubu talatin da biyu da ɗari biyar (32,500).
38 Kabilar Biliyaminu ke nan bisa ga iyalansu, Bela, da Ashbel, da Ahiram,
39 da Shuffim, da Huffim.
40 Iyalin Adar da na Na’aman suna lasafta kansu, su daga zuriyar Bela ne.
41 Waɗannan su ne ‘ya’yan Biliyaminu bisa ga iyalansu. Yawansu ya kai mutum dubu arba’in da biyar da ɗari shida (45,600).
42 Waɗannan su ne kabilar Dan bisa ga iyalansu, Hushim. Waɗannan su ne iyalan kabilar Dan.
43 Yawansu ya kai dubu sittin da huɗu da ɗari huɗu (64,400).
44 Kabilar Ashiru ke nan bisa ga iyalansu, Yimna, da Yishwi, da Beriya.
45 Iyalin Beriya kuwa sune Eber, da Malkiyel, suna lasafta kansu a zuriyar Beriya.
46 Sunan ‘yar Ashiru Sera.
47 Waɗannan su ne iyalan kabilar Ashiru. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da uku da ɗari huɗu (53,400).
48 Kabilar Naftali ke nan bisa ga iyalansu, Yezeyel, da Guni,
49 da Yezer, da Shallum.
50 Waɗannan su ne iyalan kabilar Naftali. Yawansu ya kai mutum dubu arba’in da biyar da ɗari huɗu (45,400).
51 Jimillar Isra’ilawa maza waɗanda aka ƙidaya, dubu ɗari shida da dubu ɗaya da ɗari bakwai da talatin (601,730).
An Raba Ƙasa ta Hanyar Kuri’a
52 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
53 “A raba wa waɗannan mutane gādon ƙasar bisa ga yawan kowace kabila.
54 Za ka ba babbar kabila babban rabo, ka ba ƙaramar kabila ƙaramin rabo. Kowace kabila za a ba ta gādo bisa ga yawanta.
55 Amma za a rarraba musu gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar kuri’a.
56 Za a rarraba gādo tsakanin manya da ƙananan kabilai ta hanyar kuri’a.”
Kabilar Lawi
57 Waɗannan su ne Lawiyawan da aka ƙidaya bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari.
58 Sauran iyalin Lawiyawa daga zuriyar Libni ne, da Hebron, da Mali, da Mushi, da Kora. Kohat shi ne mahaifin Amram,
59 wanda ya auri Yokabed ‘yar Lawi wadda aka haifa masa a Masar. Yokabed ta haifa wa Amram, Haruna, da Musa, da Maryamu, ‘yar’uwarsu.
60 Haruna yana da ‘ya’ya huɗu maza, Nadab, da Abihu, da Ele’azara, da Itamar.
61 Amma Nadab da Abihu sun mutu saboda sun miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji.
62 Mazan da aka ƙidaya daga mai wata guda zuwa gaba sun kai dubu ashirin da dubu uku (23,000). Ba a haɗa jimillarsu tare da ta sauran Isra’ilawa ba, da yake ba a ba su gādo tare da su ba.
Joshuwa da Kalibu kaɗai suka Ragu
63 Waɗannan su ne Isra’ilawa waɗanda Musa da Ele’azara, firist, suka ƙidaya a filayen Mowab wajen Kogin Urdun daura da Yariko.
64 Amma a cikin waɗannan da aka ƙidaya, ba wanda ya ragu daga Isra’ilawa waɗanda Musa da Haruna, firist, suka ƙidaya a jejin Sinai.
65 Gama Ubangiji ya riga ya yi magana a kansu, cewa lalle za su mutu a jeji. Ba wani mutumin da ya ragu daga cikinsu, sai dai Kalibu ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.