L. KID 27

Roƙon ‘Ya’yan Zelofehad Mata

1 Sai ‘ya’yan Zelofehad, mata, ɗan Hefer ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa, ɗan Yusufu, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada. Sunayen ‘ya’ya, matan ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

2 Da suka tafi, suka tsaya a gaban Musa da Ele’azara, firist, da gaban shugabanni, da dukan taron jama’a, suka ce,

3 “Mahaifinmu ya rasu cikin jeji. Ba ya cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Ubangiji. Ya rasu saboda alhakin zunubinsa. Ga shi, ba shi da ‘ya’ya maza.

4 Don me za a tsame sunan mahaifinmu daga cikin zuriyar iyalinsa saboda ba shi da ɗa? In ka yarda, muna roƙonka ka ba mu gādo tare da ‘yan’uwan mahaifinmu.”

5 Musa ya kai maganarsu a gaban Ubangiji.

6 Ubangiji ya ce wa Musa,

7 “Maganar ‘ya’yan Zelofehad, mata, daidai ce, saika ba su gādo tare da ‘yan’uwan mahaifinsu. Za ka sa gādon mahaifinsu ya zama nasu.

8 Sai kuma ka shaida wa Isra’ilawa, ka ce, ‘Idan mutum ya rasu ba shi da ɗa,sai ‘yarsa ta ci gādonsa.

9 Idan kuwa ba shi da ‘ya, sai a ba ‘yan’uwansa gādonsa.

10 Idan kuma ba shi da ‘yan’uwa, sai a ba ‘yan’uwan mahaifinsa gādonsa.

11 Idan kuma ba shi da su, sai a ba danginsa na kusa su mallaka, wannan zai zama umarni da ka’ida ga Isra’ilawa kamar yadda ni, Ubangiji na umarce ka.’ ”

An Zaɓi Joshuwa ya Gāji Musa

12 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Hau bisa kan Dutsen Abarim, ka dubi ƙasa wadda na ba Isra’ilawa.

13 Bayan da ka gan ta, za ka mutu kamar yadda Haruna ya yi,

14 domin ba ku yi biyayya da umarnina ba a jejin Zin. Lokacin da dukan jama’a suka yi mini gunaguni a Meriba, ba ku nuna ikona mai tsarki a gabansu ba.” (Wannan shi ne ruwan Meriba na Kadesh a jejin Zin.)

15 Musa kuwa ya ce wa Ubangiji,

16 “Bari Ubangiji Allah na ruhohin dukan ‘yan adam ya shugabantar da mutum a kan taron jama’ar,

17 mutumin da zai shugabance su cikin yaƙi, don kada taron jama’ar Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyaya.”

18 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Joshuwa, ɗan Nun, mutumin da ya dace, ka ɗibiya masa hannuwanka,

19 ka sa shi ya tsaya a gaban Ele’azara, firist, da gaban dukan taron, sa’an nan ka keɓe shi a gabansu.

20 Ka danƙa masa ikonka don taron jama’ar Isra’ila su yi masa biyayya.

21 Zai dogara ga Ele’azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele’azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama’ar Isra’ila cikin al’amuransu.”

22 Musa kuwa ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya ɗauki Joshuwa, ya sa shi ya tsaya a gaban Ele’azara, firist, da gaban dukan taron.

23 Ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya keɓe shi kamar yadda Ubangiji ya umarta.