L. KID 30

Doka a kan Wa’adodin Mata

1 Musa ya kuma ce wa shugabannin kabilan Isra’ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.”

2 Idan mutum ya yi wa’adi ga Ubangiji, ko kuwa ya rantse zai yi wani abu, ko kuwa ba zai yi wani abu ba, to, kada ya warware maganarsa, amma sai ya aikata abin da bakinsa ya hurta.

3 Idan kuma mace ta yi wa’adi ga Ubangiji, ta kuma ɗaure kanta da rantsuwa tun tana yarinya a gidan mahaifinta,

4 idan mahaifinta ya ji wa’adinta da rantsuwarta wadda ta ɗaure kanta da su, bai ce mata kome ba, to, sai wa’adinta da rantsuwarta su tabbata.

5 Amma idan mahaifinta ya ji, ya nuna rashin yarda, to, wa’adinta da rantsuwarta ba za su tsaya ba, Ubangiji kuwa zai gafarce ta domin mahaifinta bai yardar mata ba.

6 Idan kuwa ta yi aure lokacin da take da wa’adi ko kuwa rantsuwar da ta yi da garaje,

7 idan mijinta ya ji wa’adin ko rantsuwar amma bai ce mata kome ba a ranar da ya ji, to, sai wa’adinta da rantsuwarta su tabbata.

8 Amma idan mijinta bai goyi bayanta a ranar da ya ji ba, to, sai wa’adinta da rantsuwarta su warware, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.

9 Mace wadda mijinta ya rasu ko sakakkiya, dole ta cika wa’adin da ta yi, da kowane alkawari, za su tabbata.

10 Idan macen aure ta yi wa’adi ko alkawari ba za ta yi wani abu ba,

11 idan mijinta ya ji, amma bai ce mata kome ba, to, sai wa’adinta da kowace irin rantsuwarta su tabbata.

12 Amma idan mijinta ya hana ta a ranar da ya ji, to, sai ta bari. Mijinta ya hana ta ɗaukar wa’adin, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.

13 Mijinta yana da iko ya tabbatar, ko kuwa ya rushe kowane wa’adi da kowane irin alkawarin da ta ɗauka.

14 Idan mijinta ya yi shiru, bai ce mata kome ba, to, dole ta cika kowane abu da ta yi wa’adi da wanda kuma ta ɗauki alkawarinsa. Shirun da ya yi ya yardar mata.

15 Amma idan ya ji, sa’an nan daga baya ya hana ta, to, zai sha hukunci a maimakon matar.

16 Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya ba Musa a kan wa’adodin matar aure da na wadda ba ta yi aure ba, wato matar da take zaune a gidan mahaifinta.