Iyakokin Ƙasar
1 Ubangiji ya ba Musa
2 waɗannan umarnai domin jama’ar Isra’ila. Sa’ad da suka shiga ƙasar Kan’ana ga yadda iyakokin ƙasashensu za su zama.
3 Iyakar ƙasarsu daga wajen kudu ta miƙa tun daga wajen jejin Zin, har zuwa iyakar Edom. Iyakarsu kuwa ta wajen kudu za ta fara daga ƙarshen Tekun Gishiri wajen gabas.
4 Sa’an nan kuma za ta nausa ta nufin hawan Akrabbim, ta ƙetare zuwa Zin, ta dangana da kudancin Kadesh-barneya, sa’an nan ta miƙa zuwa Hazar’addar, ta zarce ta bi ta Azemon.
5 Iyakar za ta nausa daga Azemon zuwa rafin Masar, ta fāɗa bahar.
6 Bahar Rum ita ce iyakarsu ta wajen yamma.
7 Iyakarsu a wajen arewa kuwa ita ce tun daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor.
8 Daga Dutsen Hor iyakar za ta bi zuwa Hamat ta tsaya a Zedad.
9 Iyakar za ta miƙa har zuwa Zifron, ta tsaya a Hazar-enan, wannan ita ce iyakarsu a wajen arewa.
10 Iyakarsu a wajen gabas za ta tashi tun daga Haza-enan har zuwa Shefam.
11 Sa’an nan za ta gangara daga Shefam zuwa Ribla wajen gabashin Ayin. Za ta kuma gangara har ta kai Tekun Galili a wajen gabas.
12 Iyakar kuma za ta gangara har zuwa Urdun, ta tsaya a Tekun Gishiri. Wannan ita ce ƙasarsu da iyakokinta kewaye da ita.
13 Sai Musa ya ce wa Isra’ilawa, “Wannan ita ce ƙasar da za ku gāda ta hanyar jefa kuri’a. Ƙasar da Ubangiji ya umarta a ba kabilai tara da rabi.
14 Gama kabilar Ra’ubainu da ta Gad da kuma rabin kabilar Manassa sun riga sun karɓi nasu gādo.
15 Kabilan nan biyu da rabi sun karɓi nasu gādo a wancan hayin Urdun a gabashin Yariko.”
Shugabannin da za su Rarraba Kasa
16 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
17 “Ga sunayen mutanen da za su taimake ka raba gādon ƙasar, Ele’azara firist, da Joshuwa ɗan Nun.
18 Za ka kuma ɗauki shugaba ɗaya daga kowace kabila don su raba gādon ƙasar.
19 Waɗannan su ne sunayen mutanen, Kalibu ɗan Yefunne daga kabilar Yahuza.
20 Shemuyel ɗan Ammihud daga kabilar Saminu.
21 Elidad ɗan Kislon daga kabilar Biliyaminu.
22 Bukki ɗan Yogli daga kabilar Dan.
23 Na wajen Yusufu, Haniyel ɗan Efod daga kabilar Manassa,
24 da Kemuwel ɗan Shiftan daga kabilar Ifraimu.
25 Elizafan ɗan Farnak daga kabilar Zabaluna.
26 Faltiyel ɗan Azzan daga kabilar Issaka.
27 Ahihud ɗan Shelomi daga kabilar Ashiru.
28 Fedahel ɗan Ammihud daga kabilar Naftali.”
29 Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba wa jama’ar Isra’ila gādon ƙasar Kan’ana.