Yahuza da Saminu sun Ci Adoni-bezek
1 Bayan da Joshuwa ya rasu, jama’ar Isra’ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan’aniyawa?”
2 Sai Ubangiji ya ce, “Yahuza ne zai tafi, ga shi, na ba da ƙasar a gare shi.”
3 Yahuza kuwa ya ce wa Saminu ɗan’uwansa, “Ka zo tare da ni a wurin da aka ba ni rabon gādona don mu yaƙi Kan’aniyawa, ni kuma zan tafi tare da kai a wurin da aka ba ka rabon gādonka.” Saminu ya tafi tare da shi.
4 Yahuza ya tafi, Ubangiji kuwa ya ba da Kan’aniyawa da Ferizziyawa a gare su, suka kashe mutum dubu goma daga cikinsu a Bezek.
5 Suka iske Adoni-bezek a can, suka yi yaƙi da shi, suka kuma ci Kan’aniyawa da Ferizziyawa.
6 Sai Adoni-bezek ya gudu, amma suka bi shi, suka kama shi. Suka yanyanke manyan yatsotsinsa na hannu da na ƙafa.
7 Ya kuma ce, “Sarakuna saba’in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.
Kabilar Yahuza ta Ci Urushalima da Hebron
8 Mutanen Yahuza kuwa suka yaƙi Urushalima, suka ci ta, suka karkashe mutanenta, suka kuma cinna mata wuta.
9 Bayan wannan suka gangara kuma, suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, da Negeb, da filayen kwari.
10 Suka kuma tafi su yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a Hebron wadda a dā ake kira Kiriyat-arba. Suka kashe Sheshai, da Ahiman, da Talmai.
Otniyel ya Ci Birnin Debir ya Auri Aksa
11 Daga can suka tafi su yaƙi Debir wadda a dā ake kira Kiriyat-Sefer.
12 Kalibu ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat-Sefer da yaƙi har ya ci ta, zan ba shi ‘yata Aksa aure.”
13 Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu ya ci birnin da yaƙi, Kalibu kuwa ya ba shi ‘yarsa Aksa aure.
14 Da ta zo wurinsa, ta iza shi ya roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”
15 Sai ta amsa masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ka ba ni maɓuɓɓugan ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugan tuddai da na kwari.
Yawan Wuraren da Yahuza da Biliyaminu Suka Ci
16 Zuriyar Bakene, surukin Musa kuwa suka fita tare da mutanen Yahuza daga birnin dabino, wato Yariko, suka tafi jejin Yahuda da take a Negeb kudu da Arad. A can suka zauna tare da Amalekawa.
17 Yahuza kuwa da ɗan’uwansa, Saminu, suka tafi suka bugi Kan’aniyawan da suke zaune a Zefat. Suka la’anta birnin, suka hallaka shi, suka sāke wa birnin suna Horma, wato hallakarwa.
18 Yahuza kuma ya ci Gaza da karkararta, da Ashkelon da karkararta, da Ekron da karkararta.
19 Ubangiji kuwa yana tare da Yahuza, ya mallaki ƙasar tuddai, amma bai iya korar waɗanda suke zaune a fili ba, domin suna da karusan ƙarfe.
20 Aka ba Kalibu Hebron kamar yadda Musa ya faɗa. Shi kuwa ya kori ‘ya’yan Anak, maza, su uku, a can.
21 Amma mutanen Biliyaminu ba su kori Yebusiyawan da suke zaune a Urushalima ba domin haka Yebusiyawa suka yi zamansu tare da mutanen Biliyaminu a Urushalima har wa yau.
Kabilar Yusufu ta Ci Betel
22 Jama’ar kabilar Yusufu kuwa suka haura don su yaƙi Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su.
23 Suka aika a leƙi asirin Betel wadda a dā ake kira Luz.
24 Sai ‘yan leƙen asirin ƙasar suka ga wani mutum yana fitowa daga cikin birnin, suka ce masa, “Muna roƙonka ka nuna mana hanyar shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.”
25 Ya kuwa nuna musu, suka shiga suka kashe dukan mutanen birnin, amma suka bar mutumin da iyalinsa duka.
26 Sai mutumin ya tafi ƙasar Hittiyawa, ya gina birni, ya sa masa suna Luz, haka ake kiran birnin har wa yau.
Yawan Wuraren da Manassa da Ifraimu suka Ci
27 Kabilar Manassa ba su kori waɗanda suke zaune a Bet-sheyan, da Ta’anak, da Dor, da Ibleyam, da Magiddo, da garuruwan da suke kusa da su ba, amma Kan’aniyawa suka yi kanekane cikin ƙasar.
28 Sa’ad da Isra’ilawa suka yi ƙarfi, suka sa Kan’aniyawa su yi aikin gandu, amma ba su kore su ba.
29 Mutanen Ifraimu kuma ba su kori Kan’aniyawan da suke zaune cikin Gezer ba, amma Kan’aniyawa suka yi zamansu a Gezer tare da su.
Yawan Wuraren da sauran Kabilai Suka Ci
30 Mutanen Zabaluna ma ba su kori mazaunan Kattat da na Nahalal ba, amma Kan’aniyawa suka zauna tare da su, suna yi musu aikin gandu.
31 Haka kuma mutanen Ashiru ba su kori mazaunan Akko, da na Sidon, da Alab, da Akzib, da Helba, da Afek, da Rehob ba.
32 Amma Ashirawa suka yi zamansu tare da Kan’aniyawan ƙasar, gama ba su kore su ba.
33 Mutanen Naftali ma ba su kori mazaunan Bet-shemesh, da na Bet-anat ba, amma suka zauna tare da Kan’aniyawan ƙasar, duk da haka mazaunan Bet-shemesh da na Bet-anat suka zama masu yi musu aikin gandu.
34 Amoriyawa suka matsa wa Danawa, suka angaza su cikin ƙasar tuddai, ba su yarda musu su zauna a filayen ba.
35 Amoriyawa kuwa suka nace su zauna a Heres, da Ayalon, da Shalim. Amma mutanen kabilar Yusufu suka mallake su har suka zama masu yi musu aikin gandu.
36 Iyakar Amoriyawa ta nausa ta kan hawan Akrabbim daga Sela zuwa gaba.