Yefta ya Ceci Isra’ilawa daga Hannun Ammonawa
1 Yefta mutumin Gileyad ne, shi kuwa jarumi ne, amma mahaifiyarsa karuwa ce. Gileyad ne mahaifinsa.
2 Matar Gileyad ta haifa masa ‘ya’ya maza. Sa’ad da suka yi girma, sai suka kori Yefta, suka ce masa, “Ba za ka ci gādo a gidan mahaifinmu ba, gama kai ɗan wata mace ne.”
3 Sai Yefta ya gudu daga wurin ‘yan’uwansa, ya zauna a ƙasar Tob. ‘Yan iska kuwa suka taru wurin Yefta, sukan tafi yawo tare da shi.
4 Ana nan sai Ammonawa suka kai wa Isra’ilawa yaƙi.
5 Da haka ta auku, sai shugabannin Gileyad suka tafi su komo da Yefta daga ƙasar Tob.
6 Suka ce wa Yefta, “Ka zo, ka zama shugabanmu don mu yi yaƙi da Ammonawa.”
7 Amma Yefta ya ce wa dattawan Gileyad, “Ba ku kuka ƙi ni, kuka kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuka zo wurina a lokacina da kuke shan wahala?”
8 Sai dattawan Gileyad suka amsa masa, “Abin da ya sa muka zo wurinka yanzu, shi ne domin ka tafi tare da mu ne mu yi yaƙi da Ammonawa, ka kuma zama shugaban dukan jama’ar Gileyad.”
9 Yefta kuwa ya ce musu, “Idan kuka koma da ni gida domin in yi yaƙi da Ammonawa, idan Ubangiji ya ba da su a hannuna, to, zan zama shugabanku.”
10 Suka amsa suka ce wa Yefta, “Ubangiji shi ne shaida tsakaninmu, lalle za mu yi maka kamar yadda ka ce.”
11 Yefta kuwa ya tafi tare da dattawa Gileyad. Su kuwa suka naɗa shi shugabansu da sarkin yaƙinsu. Yefta kuwa ya faɗi dukan abin da yake zuciyarsa a gaban Ubangiji a Mizfa.
12 Yefta kuwa ya aiki jakadu wurin Sarkin Ammonawa da cewa, “Me ya haɗa ka da ni, da ka zo ƙasata da yaƙi?”
13 Sarkin Ammonawa ya amsa wa jakadun Yefta cewa, “Domin lokacin da Isra’ilawa suna tahowa daga Masar sun ƙwace mini ƙasa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa Kogin Urdun. Yanzu sai ka mayar mini da ita cikin lumana.”
14 Yefta kuma ya sāke aike da jakadu wurin Sarkin Ammonawa,
15 tare da amsa, ya ce, “Isra’ilawa ba su ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba.
16 Amma sa’ad da suka baro Masar, sun bi ta jeji zuwa Bahar Maliya, suka zo Kadesh.
17 Sa’an nan suka aike da jakadu wurin Sarkin Edom, su roƙe shi ya bar su su wuce ta ƙasarsa. Amma Sarkin Edom bai yarda ba. Suka kuma aika wa Sarkin Mowab, shi ma bai yarda ba, don haka Isra’ilawa suka zauna a Kadesh.
18 “Sa’an nan suka ci gaba da tafiya ta cikin hamada. Suka zaga ƙasar Edom da ta Mowab. Da suka kai gabashin ƙasar Mowab, sai suka yi zango a bakin Kogin Arnon, amma ba su haye kogin ba, gama shi ne iyakar ƙasar Mowab.
19 Sa’an nan Isra’ilawa suka aike da jakadu wurin Sihon Sarkin Heshbon ta Amoriyawa, suka roƙe shi, suka ce, ‘Ka yarda mana mu wuce ta ƙasarka.’
20 Amma Sihon bai amince wa Isra’ilawa su bi ta ƙasarsa, su wuce ba. Ya kuwa tattara mutanensa, ya kafa sansaninsa a Yahaza, ya yi yaƙi da Isra’ilawa.
21 Ubangiji Allah na Isra’ila kuwa ya ba da Sihon da mutanensa duka ga Isra’ilawa, suka ci su da yaƙi. Suka kuwa mallaki dukan ƙasar Amoriyawa da mazaunan ƙasar.
22 Suka mallaki dukan ƙasar Amoriyawa tun daga Kogin Arnon har zuwa Kogin Yabbok, tun kuma daga jeji zuwa Kogin Urdun.
23 To, ai, ka ga Ubangiji Allah na Isra’ila ne ya kori Amoriyawa saboda jama’ar Isra’ila. To, yanzu so kake ka ƙwace mana?
24 Kai ba za ka mallaki abin da Kemosh, allahnka, ya ba ka mallaka ba? Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya mallakar mana, za mu mallake shi.
25 Kana zaton ka fi Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab? Ka ji ya taɓa hamayya da Isra’ilawa? Ko kuwa ka ji ya taɓa yin yaƙi da su?
26 Shekara ɗari uku Isra’ilawa suka yi zamansu a Heshbon da ƙauyukanta, da Arower da ƙauyukanta, da dukan biranen da suke a gefen Kogin Arnon, me ya sa ba ka ƙwace su tun a wancan lokaci ba?
27 Don haka ni ban yi maka laifi ba, kai ne kake yi mini laifi da kake yaƙi da ni. Ubangiji ne alƙali yau, zai shara’anta tsakanin Isra’ilawa da Ammonawa.”
28 Amma Sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika masa ba.
29 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko wa Yefta, sai ya tashi ratsa Gileyad da Manassa zuwa Mizfa ta Gileyad, daga can ya haura zuwa wurin Ammonawa.
30 Yefta kuwa ya yi wa’adi ga Ubangiji, ya ce, “Idan dai ka ba da Ammonawa a hannuna,
31 duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don ya tarye ni, sa’ad da na komo daga yaƙin Ammonawa da nasara, zai zama na Ubangiji, zan kuwa miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”
32 Yefta ya haye zuwa wurin Ammonawa domin ya yi yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannunsa.
33 Ya karkashe su da mummunan kisa tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-keramim. Ya cinye biranensu guda ashirin. Da haka Ammonawa suka sha kāshi a hannun Isra’ilawa.
‘Yar Yefta
34 Da Yefta ya koma gidansa a Mizfa, sai ga ‘yarsa, tilo ta fito da kiɗa da rawa don ta tarye shi. Ita ce kaɗai ‘yarsa, banda ita ba shi da ɗa ko ‘ya.
35 Sa’ad da ya gan ta sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Kaito, ‘yata, kin karya mini gwiwa, kin zamar mini babban dalilin wahala. Na riga na yi wa’adi ga Ubangiji, ba kuwa zan iya warware shi ba.”
36 Sai ta ce masa, “Baba, idan ka riga ka yi wa’adi ga Ubangiji, sai ka yi da ni bisa ga wa’adinka, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa, abokan gābanka.”
37 Ta kuma ce masa, “Ina so ka yardar mini in tafi kan duwatsu ni da ƙawayena in yi makokin budurcina har wata biyu.”
38 Sai ya ce mata, “Tafi.” Ya sallame ta, ta tafi har wata biyu ɗin. Ita da ƙawayenta kuwa suka yi makokin budurcinta a kan duwatsu.
39 Bayan wata biyu, sai ta koma wurin mahaifinta, shi kuwa ya yi abin da ya yi wa Ubangiji wa’adi. Ta rasu ba ta taɓa sanin namiji ba. Wannan kuwa ya zama al’ada a cikin Isra’ila,
40 wato matan Isra’ilawa sukan fita kowace shekara su yi makoki kwana huɗu don ‘yar Yefta, mutumin Gileyad.