Yefta da Mutanen Ifraimu
1 Mutanen Ifraimu suka yi gangami suka haye zuwa Zafon da shirin yaƙi. Suka ce wa Yefta, “Me ya sa ka haye zuwa yaƙi da Ammonawa, amma ba ka kira mu mu tafi tare da kai ba? To, yanzu za mu ƙone ka da gidanka.”
2 Amma Yefta ya amsa musu, ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya da Ammonawa, na kira ku don ku cece ni, amma ba ku cece ni daga hannunsu ba.
3 Sa’ad da na ga ba ku cece ni ba, sai na yi kasai da raina, na haye don in yi karo da Ammonawa. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna. Me ya sa kuka zo yau don ku yi yaƙi da ni?”
4 Sa’an nan Yefta ya tara dukan mutanen Gileyad, suka yi yaƙi da mutanen Ifraimu, suka ci su.
Mutanen Ifraimu suka ce musu, “Ku mutanen Gileyad masu neman mafaka ne a cikin Ifraimu da Manassa!”
5 Mutanen Gileyad suka hana mutanen Ifraimu hayewa ta mashigan Kogin Urdun. Idan wani mutumin Ifraimu gujajje ya ce, “Ku bar ni in haye.”
Sai mutanen Gileyad su tambaye shi, “Kai mutumin Ifraimu ne?”
Idan ya ce, “A’a,”
6 sai su ce masa, to, ka ce, “Shibbolet,” sai mutum ya ce, “Sibbolet,” gama ba ya iya faɗa daidai. Sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Mutanen Ifraimu da aka kashe a lokacin su dubu arba’in da dubu biyu (42,000) ne.
7 Yefta mutumin Gileyad ya shugabanci Isra’ilawa shekara shida, sa’an nan ya rasu. Aka binne shi a garinsu, wato Gileyad.
Ibzan, da Elon, da Abdon Sun Shugabanci Isra’ilawa
8 Bayan Yefta, sai Ibzan, mutumin Baitalami ya shugabanci Isra’ilawa.
9 Yana da ‘ya’ya maza talatin, da ‘ya’ya mata talatin. Ya aurar da ‘ya’yansa mata ga wata kabila, ya kuma auro wa ‘ya’yansa maza ‘yan mata daga wata kabila. Ya shugabanci Isra’ilawa shekara bakwai.
10 Sa’an nan ya rasu, aka binne shi a Baitalami.
11 Bayansa kuma, sai Elon mutumin Zabaluna ya shugabanci Isra’ilawa shekara goma.
12 Sa’an nan ya rasu, aka binne shi a Ayalon a ƙasar Zabaluna.
13 Bayan Elon kuma, sai Abdon, ɗan Hillel, mutumin Firaton, ya shugabanci Isra’ilawa.
14 Yana da ‘ya’ya maza arba’in, da jikoki maza talatin, suna hawan jakai saba’in. Abdon ya shugabanci Isra’ilawa shekara takwas.
15 Sa’an nan ya rasu, aka binne shi a Firaton ta ƙasar Ifraimu a tudun Amalekawa.