Samson a Gaza
1 Daga can Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa, sai ya shiga wurinta.
2 Aka faɗa wa mutanen Gaza, Samson yana nan. Suka kewaye wurin, suka yi fakonsa a ƙofar garin dukan dare. Suka yi shiru dukan dare, suka ce wa junansu, “Za mu jira sai gari ya waye sa’an nan mu kashe shi.”
3 Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakar dare. Sa’an nan ya tashi ya kama ƙyauren ƙofar birnin, da madogarai biyu na ƙofar, ya tumɓuke su. Ya saɓe su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da yake a gaban Hebron.
Samson da Delila
4 Bayan wannan kuma sai ya kama ƙaunar wata mace mai suna Delila a kwarin Sorek.
5 Shugabannin Filistiyawa, su biyar suka je wurinta suka ce mata, “Ki yi masa kirsa, don ki san dalilin irin ƙarfin nan nasa, da kuma yadda za mu yi maganinsa, mu ɗaure shi don mu rinjaye shi. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu da ɗari (1,100).”
6 Delila kuwa ta ce wa Samson, “Ina roƙonka ka faɗa mini inda babban ƙarfin nan naka yake, da kuma yadda za a ɗaure ka ka rasa kuzari.”
7 Samson ya ce mata, “Idan an ɗaure ni da sababbin tsarkiyoyi guda bakwai, waɗanda ba su bushe ba, to, sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”
8 Sai shugabannin Filistiyawa suka kawo wa Delila sababbin tsarkiyoyi guda bakwai waɗanda ba su bushe ba. Ta kuwa ɗaure shi da su.
9 Tana kuwa da mutane a laɓe cikin wani ɗaki, sai ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da jin haka, sai ya katse tsarkiyoyi kamar zare idan an sa masa wuta. Asirin ƙarfinsa kuwa bai sanu ba.
10 Delila kuma ta ce wa Samson, “Ga shi, ka yi mini ba’a, ka ruɗe ni. Ina roƙonka, ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.”
11 Ya ce mata, “Idan suka ɗaure ni da sababbin igiyoyi waɗanda ba a yi amfani da su ba, to, zan rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”
12 Sai Delila ta ɗauki sababbin igiyoyi, ta ɗaure shi da su, sa’an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa na zuwa kanka, Samson!” Amma ya katse igiyoyin da ta ɗaure shi da su kamar silin zare. Mutanen kuwa na nan laɓe a wani ɗaki.
13 Delila ta ce wa Samson, “Har yanzu dai, ka maishe ni shashasha, kana ta ruɗina. Ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.”
Ya ce mata, “Idan kin saƙa tukkwayen bakwai waɗanda suke kaina haɗe da zare, kika buga da akwasha sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”
14 Sa’ad da yake barci, Delila ta saƙa tukkwayen nan bakwai da suke kansa haɗe da zare, ta buga da akwasha, sa’an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da ya farka daga barcin, sai ya tumɓuke akwashar, da zaren.
15 Delila ta ce masa, “Ƙaƙa za ka ce kana ƙaunata, alhali kuwa ba na a zuciyarka? Sau uku ke nan ka maishe ni shashasha, ba ka faɗa mini inda ƙarfin nan naka yake ba.”
16 Sa’ad da ta fitine shi yau da gobe da yawan maganganunta, ta tunzura shi, sai ransa ya ɓaci kamar zai mutu.
17 A ƙarshe ya faɗa mata ainihin gaskiyar, ya ce mata, “Ba a taɓa aske gashin kaina ba, gama ni keɓaɓɓe ga Ubangiji ne tun daga cikin uwata. Idan aka yi mini aski, to, ƙarfina zai rabu da ni, in zama marar ƙarfi kamar kowa.”
18 Sa’ad da Delila ta gane ya faɗa mata ainihin gaskiya, sai ta aika a kirawo shugabannin Filistiyawa tana cewa, “A wannan karo ku zo, domin ya faɗa mini ainihin gaskiyar.” Shugabannin Filistiyawa kuwa suka zo wurinta da kuɗi a hannu.
19 Ta kuwa sa shi ya yi barci a cinyoyinta, sai ta kira wani mutum, ta sa shi ya aske tukkwayen nan bakwai waɗanda suke kansa. Sa’an nan ta yi ƙoƙari ta sa ya harzuƙa, amma ƙarfinsa ya rabu da shi.
20 Ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!”
Sai ya farka daga barcinsa, ya ce, “Zan fita kamar yadda na saba yi koyaushe, in miƙe jikina.” Ashe, bai sani ba, Ubangiji ya rabu da shi.
21 Filistiyawa fa suka kama shi, suka ƙwaƙule idanunsa, suka gangara da shi zuwa Gaza. Suka ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Ya yi ta niƙa a kurkuku.
22 Amma gashin kansa ya fara tohowa.
Samson ya Mutu
23 Shugabannin Filistiyawa kuwa suka taru domin su miƙa babbar hadaya ga allahnsu, Dagon. Suka raira waƙa, suka ce, “Allahnmu ya ba da Samson, maƙiyinmu a hannunmu!”
24 Da mutane suka gan shi, sai suka raira waƙar yabon allahnsu, suna cewa, “Allahnmu ya ba da maƙiyinmu a hannunmu, wanda ya fallasa ƙasarmu, ya kashe mutanenmu da yawa.”
25 Sa’ad da suke ta farin ciki, sai suka ce, “A kawo Samson ya yi mana wasa.” Sai suka kawo Samson daga kurkuku, ya kuwa yi wasa a gabansu. Suka sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙai.
26 Samson kuwa ya ce wa yaron da yake jagoransa, “Bari in taɓa ginshiƙan da suke ɗauke da gidan nan, domin in jingina.”
27 Gidan kuwa yana cike da mutane mata da maza. Shugabannin nan biyar na Filistiyawa suna wurin. Akwai mutum dubu uku mata da maza, a kan benen da suka zo kallon wasan Samson.
28 Sa’an nan Samson ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ka tuna da ni, ina roƙonka, ka ƙarfafa ni sau ɗayan nan kaɗai, don in ɗauki fansa a kan Filistiyawa saboda idona biyu da suka ƙwaƙule mini.”
29 Sai Samson ya kama ginshiƙai biyu da suke a tsakiya, waɗanda suke ɗauke da gidan. Ya riƙe su da hannunsa biyu, ɗaya a kowane hannu, sa’an nan ya jingina jikinsa a kansu,
30 ya yi kuwwa ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Ya sunkuya da iyakar ƙarfinsa. Ɗakin kuwa ya faɗa a kan shugabannin da dukan mutanen da suke a cikin ɗakin. Mutanen da Samson ya kashe a rasuwarsa sun fi waɗanda ya kashe sa’ad da yake da rai.
31 ‘Yan’uwansa da dukan danginsa, suka gangara, suka ɗauki gawarsa, suka binne a kabarin Zora da Eshtawol. Samson ya shugabanci Isra’ilawa shekara ashirin.