Gumakan Mika
1 Akwai wani mutum a ƙasar tudu ta Ifraimu, da ake kira Mika.
2 Shi ne ya ce wa mahaifiyarsa, “Sa’ad da aka sace miki tsabar azurfan nan dubu da ɗari ɗaya (1,100), kin hurta la’ana a kan ɓarayin, na kuwa ji ki. To, ga shi, azurfar na wurina, ni na ɗauka.”
Sai mahaifiyarsa ta ce, “Allah ya sa maka albarka, ɗana.”
3 Ya mayar wa mahaifiyarsa da azurfar dubu da ɗari (1,100). Mahaifiyarsa ta ce, “Domin kada la’anar ta kama ɗana, ina ba da wannan azurfa ga Ubangiji da zuciya ɗaya. Ana iya sassaƙa gunki a kuma yi na zubi saboda haka zan ba ka ita.”
4 Da ya mayar mata da azurfar, ta ɗibi azurfa ɗari biyu ta ba maƙerin azurfa, shi kuwa ya sassaƙa gunki ya kuma yi na zubi. Aka ajiye su a gidan Mika.
5 Mika kuwa yana da ɗakin gumaka. Ya yi gumaka, da falmaransu, da kan gida. Ya keɓe ɗaya daga cikin ‘ya’yansa maza domin ya zama firist nasa.
6 A wannan lokaci ba sarki a Isra’ila, kowa yana ta yin yadda ya ga dama.
7 Akwai wani saurayi Balawen da yake zama a Baitalami ta Yahudiya.
8 Saurayin kuwa ya yi ƙaura daga Baitalami. Sa’ad da yake tafiya sai ya iso gidan Mika, a ƙasar tudu ta Ifraimu.
9 Mika ya tambaye shi, “Daga ina ka zo?”
Ya ce, “Ni Balawe ne na Baitalami ta Yahudiya, ina neman wurin da zan zauna.”
10 Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni, ka zama mai ba ni shawara, da kuma firist, ni kuwa zan riƙa ba ka azurfa goma, da tufafi, da abin zaman gari kowace shekara.”
11 Balawen kuwa ya yarda ya zauna tare da Mika. Ya kuwa zama kamar ɗa ga Mika.
12 Mika kuma ya naɗa shi ya zama firist ɗinsa. Ya kuwa zauna a gidansa.
13 Sa’an nan Mika ya ce, “Yanzu na sani Ubangiji zai sa mini albarka, da yake na sami Balawe ya zamar mini firist.”