Mika da Kabilar Dan
1 A kwanakin nan ba sarki a Isra’ila. A wannan lokaci kuwa kabilar Dan suna ta neman yankin ƙasar da za su samu, su zauna. Gama har yanzu ba su sami nasu gādon ƙasa tare da sauran kabilar Isra’ila ba.
2 Sai Danawa suka zaɓi mutum biyar jarumai daga kabilarsu, suka aike su daga Zora da Eshtawol, su tafi leƙen asirin ƙasar, su bincike ta. Suka kuwa tafi zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka sauka a gidan Mika.
3 Sa’ad da suke a gidan Mika ɗin, sai suka ji muryar saurayin nan, Balawe, suka tsaya suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kuma kake yi a nan?”
4 Ya ce musu, “Mun yi yarjejeniya da Mika, in yi masa aikin firist, shi kuma ya biya ni.”
5 Suka ce masa, “In ka yarda ka roƙar mana Allah ko tafiyarmu na da sa’a.”
6 Firist ɗin ya ce musu, “Kada ku damu, Ubangiji yana tare da ku a tafiyarku.”
7 Saboda haka mutanen nan biyar suka tashi, suka zo Layish, suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa. Ba su da rigima, natsattsu ne, ba su jayayya da kowa, suna da wadata. Suna nesa da Sidoniyawa, ba su sha’anin kome da kowa.
8 Da mutanen nan biyar suka koma wurin ‘yan’uwansu a Zora da Eshtawol, sai ‘yan’uwan suka tambaye su labarin tafiyarsu.
9 Suka ce, “Ku tashi, mu tafi mu fāɗa musu, gama mun ga ƙasar tana da ni’ima ƙwarai. Kada ku zauna ku ɓata lokaci, ku shiga ku mallake ta!
10 Idan kuka je za ku tarar da mutane suna zama a sake. Ƙasar kuwa babba ce, tana da dukan abin da ɗan adam yake bukata.”
11 Mutum ɗari shida daga kabilar Dan suka yi shirin yaƙi, suka kama hanya daga Zora da Eshtawol.
12 Suka tafi suka kafa sansani a yammacin Kiriyat-yeyarim, birni ne a Yahudiya. Saboda haka ake kiran wurin Mahanedan, wato sansanin Dan, har wa yau.
13 Daga can suka wuce zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka zo gidan Mika.
14 Mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar Layish, suka ce wa abokan tafiyarsu, “Ko kun san akwai gunkin itace cikin gidajen nan? Akwai kuma gunki na zubi, da kan gida, da falmaran dominsu. Me ya kamata mu yi musu?”
15 Sai suka juya zuwa gidan Mika, inda saurayin nan Balawe yake, suka gaishe shi.
16 Danawa ɗari shida ɗin da suka yi shirin yaƙi, suka tsaya a bakin ƙofa.
17 Amma mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar suka shiga kai tsaye, suka ɗauki gunkin da aka yi da itace, da falmaran, da kan gida, da gunki na zubi. Firist ɗin kuwa ya tsaya a bakin ƙofa tare da mutum ɗari shida ɗin nan masu shirin yaƙi.
18 Sa’ad da mutum biyar ɗin nan suka shiga gidan Mika suka ɗauki falmaran, da sassaƙaƙƙen gunki, da kan gida, da gunki na zubi, sai firist ɗin ya ce musu, “Me kuke yi?”
19 Suka ce masa, “Yi mana shiru, kame bakinka. Ka biyo mu, ka zama firist namu da mai ba mu shawara. Bai fi kyau ka zama firist na kabilar Isra’ila ba, da a ce ka zama na gidan mutum guda kawai?”
20 Da firist ɗin ya ji haka, sai ya yi murna, ya ɗauki falmaran da kan gida da sassaƙaƙƙen gunki, ya tafi tare da su.
21 Suka juya, suka tafi da ‘ya’yansu da dabbobinsu, da mallakarsu.
22 Sa’ad da suka yi ‘yar tazara daga gidan Mika sai aka kira maƙwabtan Mika, suka je suka ci wa Danawa.
23 Suka yi wa Danawa tsawa. Da suka waiga, sai suka ce wa Mika, “Me ya faru? Me ya kawo waɗannan ‘yan iska?”
24 Mika kuwa ya ce musu, “Kun kwashe allolina da na yi, da firist ɗina, me ya rage mini kuma? Sa’an nan ku ce mini, ‘Me ya faru?’ ”
25 Danawa kuma suka ce masa, “Kada ka kuskura ka ce kome, idan ba haka ba mutanen nan za su harzuƙa, da kai da iyalinka duka ku rasa rayukanku.”
26 Sa’an nan Danawa suka kama hanyarsu. Da Mika ya ga dai sun fi ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gida.
27 Da Danawa suka ɗauke gumakan da Mika ya yi, da firist ɗinsa, sai suka je Layish inda suka sami mutane suna zamansu a huce. Suka hallaka su, suka ƙone birnin.
28 Ba wanda zai ceci mutanen Layish, gama suna nesa da Sidon, ba su kuma sha’ani da kowa. A kwari guda ne da Bet-rehob. Danawa kuwa suka sāke gina birnin, suka zauna a ciki.
29 Suka sa wa birnin suna Dan, ɗan Yakubu. Kafin wannan lokaci kuwa ana kiran birnin Layish ne.
30 Danawa fa suka kafa gunkin domin su yi masa sujada. Jonatan, ɗan Gershom, ɗan Musa, shi da ‘ya’yansa maza, suka zama firistocin Danawa, har zuwa ranar da aka kwashe mutanen zuwa bauta.
31 Haka fa suka kafa gunkin Mika har duk lokacin da alfarwar Ubangiji take a Shilo.