Mala’ikan Ubangiji a Bokim
1 Mala’ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim. Ya ce wa Isra’ilawa, “Ni na kawo ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba kakanninku. Na kuma ce, ‘Ba zan ta da madawwamin alkawarina da ku ba.
2 Ku kuma ba za ku yi alkawari da mazaunan ƙasar nan ba, amma za ku rurrushe bagadansu.’ Duk da haka ba ku yi biyayya da maganata ba. Me ke nan kuka yi?
3 Don haka na ce, ‘Ba zan kore muku su ba, amma za su zamar muku ƙaya, gumakansu kuwa za su zamar muku tarko.’ ”
4 Da mala’ikan Ubangiji ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, suka yi kuka mai zafi.
5 Saboda haka suka sa wa wuri suna Bokim, wato waɗanda suke kuka. Suka kuma miƙa sadakoki ga Ubangiji a wurin.
Rasuwar Joshuwa
6 Da Joshuwa ya sallami Isra’ilawa, kowane mutum ya tafi domin ya ɗauki gādonsa, don ya mallaki tasa ƙasa.
7 Isra’ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin Joshuwa, bayan rasuwarsa kuma suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin dattawan da suka ga dukan manyan ayyukan da Ubangiji ya yi domin Isra’ilawa.
8 Bawan Ubangiji, Joshuwa ɗan Nun, ya rasu yana da shekara ɗari da goma.
9 Suka binne shi a Timnat-sera a ƙasar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga’ash, a ƙasar gādonsa.
10 Dukan tsarar Joshuwa sun rasu, waɗanda suke tasowa kuwa suka manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra’ila.
Isra’ilawa sun bar Yi wa Ubangiji Sujada
11 Jama’ar Isra’ila kuwa suka yi wa Ubangiji zunubi, wato suka bauta wa gunkin nan mai suna Ba’al.
12 Suka bar yi wa Ubangiji Allah na kakanninsu sujada, wanda ya fisshe su daga ƙasar Masar. Suka fara yi wa allolin mutanen da suke zaune kewaye da su sujada. Suka rusuna wa allolin, da haka suka sa Ubangiji ya yi fushi.
13 Suka bar yi wa Ubangiji sujada suka bauta wa gumakan nan, wato Ba’al da Ashtarot.
14 Ubangiji kuwa ya husata da Isra’ilawa, ya bashe su ga waɗanda za su washe su. Ya sa magabtansu da suke kewaye da su suka sha ƙarfinsu, har ya zama Isra’ilawa ba su iya kāre kansu daga maƙiyansu ba.
15 A duk sa’ad da suka tafi yaƙi sai Ubangiji ya yi gāba da su kamar dai yadda ya faɗa. Saboda haka suka shiga wahala ƙwarai.
16 Sa’an nan Ubangiji ya naɗa musu mahukunta masu ƙarfi da suka cece su daga waɗanda suka washe su.
17 Duk da haka ba su kasa kunne ga mahukuntan ba. Suka yi wa Ubangiji ha’inci, suka yi wa waɗansu alloli sujada. Kakanninsu sun bi umarnin Ubangiji amma wannan tsara nan da nan suka bar yin haka ɗin.
18 Sa’ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan taimake shi, ya kuwa cece su daga abokan gāba dukan kwanakin mahukuncin. Gama Ubangiji ya ji ƙansu saboda nishinsu, da zaluncin da ake yi musu.
19 Amma idan mahukuncin ya rasu, sai su sāke kaucewa, su yi zunubi fiye da na kakanninsu. Suna bin gumaka, suna bauta musu, suna kuma yi musu sujada, ba su daina mugayen ayyukansu na rashin aminci da taurin zuciya ba.
20 Ubangiji kuwa ya husata da Isra’ilawa ya ce, “Saboda al’umman nan ta ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu, ba su yi biyayya da maganata ba,
21 don haka daga nan gaba ba zan ƙara kore musu wata al’umma daga cikin al’umman da Joshuwa ya rage kafin rasuwarsa ba.
22 Da haka ne zan jarraba Isra’ilawa, in gani ko za su mai da hankali su yi tafiya cikin hanyata, kamar yadda kakanninsu suka yi, ko kuwa ba za su yi ba.”
23 Don haka Ubangiji ya bar waɗannan al’ummai, bai kore su nan da nan ba, bai kuma ba da su ga Joshuwa ba.