Debora da Barak sun Ci Sisera
1 Bayan rasuwar Ehud, Isra’ilawa suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji.
2 Ubangiji kuwa ya yarda Yabin Sarkin Kan’ana, wanda yake mulkin Hazor ya ci su da yaƙi. Sisera, wanda yake zaune a Haroshet ta al’ummai, shi ne shugaban sojojin Yabin.
3 Sa’an nan jama’ar Isra’ila suka yi kuka ga Ubangiji suna neman taimako, gama Yabin yana da karusai ɗari tara na ƙarfe, ya kuma tsananta wa Isra’ilawa, ya mugunta musu shekara ashirin. Isra’ilawa kuwa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.
4 Debora, matar Lafidot, ita ce annabiya. Tana hukuncin Isra’ilawa.
5 Ta zauna a gindin giginyar Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Isra’ilawa sukan haura zuwa wurinta don ta yi musu shari’a.
6 Sai ta aika a kirawo Barak, ɗan Abinowam, daga birnin Kedesh a ƙasar Naftali. Ta ce masa, “Ubangiji Allah na Isra’ila ya ba ka wannan umarni, ya ce, ‘Ka tafi ka tara mutanenka a Dutsen Tabor, ka kuma ɗauki mutum dubu goma (10,000), daga kabilar Naftali da ta Zabaluna.
7 Ni kuwa zan jawo Sisera, shugaban sojojin Yabin, da karusansa, da ƙungiyoyin sojojinsa ya yi karo da kai a Kogin Kishon, zan kuwa bashe shi a hannunka.’ ”
8 Barak ya ce mata, “Idan za ki tafi tare da ni, zan tafi, amma idan ba za ki tafi tare da ni ba, ni ma ba zan tafi ba.”
9 Sai ta ce masa, “Hakika zan tafi tare da kai, amma darajar wannan tafiya ba za ta zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Debora kuwa ta tashi, ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh.
10 Barak kuwa ya kirawo kabilar Zabaluna da ta Naftali zuwa Kedesh. Mutum dubu goma (10,000) suka rufa masa baya, Debora kuwa ta haura tare da shi.
11 Eber, Bakene kuwa, ya ware daga Keniyawa, zuriyar Hobab, surukin Musa, ya kafa alfarwarsa can nesa wajen oak a Za’anannim wanda yake kusa da Kedesh.
12 Aka faɗa wa Sisera cewa, Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa Dutsen Tabor.
13 Sai Sisera ya tattaro karusansa na ƙarfe duka guda ɗari tara, da dukan mutanen da suke tare da shi, tun daga Haroshet ta al’ummai, har zuwa Kogin Kishon.
14 Debora ta ce wa Barak, “Tashi! Gama wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka, gama Ubangiji yana bi da kai!” Sai Barak ya gangaro daga Dutsen Tabor da mutum dubu goma (10,000) biye da shi.
15 Ubangiji kuwa ya sa Barak ya yi kaca-kaca da Sisera, da karusansa duka, da rundunar mayaƙansa duka da takobi. Sisera kuwa ya sauka daga karusarsa, ya gudu da ƙafa.
16 Amma Barak ya runtumi karusan da rundunar har zuwa Haroshet ta al’ummai. Aka kashe dukan rundunar Sisera da takobi, ba wanda ya tsira.
17 Amma Sisera ya gudu da ƙafa zuwa alfarwar Yayel matar Eber, Bakene, gama akwai jituwa tsakanin Yabin Sarkin Hazor da gidan Eber, Bakene.
18 Sai Yayel ta fito, ta taryi Sisera, ta ce masa, “Shigo nan, ubangijina, kada ka ji tsoro.” Ya kuwa bi ta zuwa cikin alfarwa, ta ɓoye shi bayan labule.
19 Ya ce mata, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa kaɗan in sha, gama ina jin ƙishi.” Ta kuwa buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, ta kuma lulluɓe shi.
20 Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar alfarwar, idan wani ya zo ya tambaye ki, ‘Ko akwai wani a nan?’ Sai ki ce, ‘Babu.’ ”
21 Amma Yayel, matar Eber, ta ɗauki turken alfarwa da guduma, ta yi sanɗa zuwa wurinsa, ta kafa masa turken a gindin kunne, ya zarce har ƙasa, a sa’ad da yake sharar barcin gajiya. Ya kuwa mutu.
22 Barak kuwa yana bin sawun Sisera. Da Yayel ta gan shi, sai ta fita, ta tarye shi, ta ce masa, “Ka zo, zan nuna maka inda mutumin da kake nema yake.” Ya shiga alfarwarta, sai ga Sisera nan kwance matacce da turke a gindin kunnensa.
23 A wannan rana Allah ya fatattaki Yabin Sarkin Kan’ana, a gaban Isra’ilawa.
24 Isra’ilawa suka yi ta tsananta wa Yabin Sarkin Kan’ana har suka hallaka shi.