Waƙar Debora da Barak
1 A wannan rana Debora da Barak, ɗan Abinowam, suka raira wannan waka,
2 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Isra’ilawa suka ƙudura su yi yaƙi.
Mutane suka sa kansu da farin ciki.
Alhamdu lillahi!
3 Ku kasa kunnenku ya ku sarakuna,
Ku lura, ya ku hakimai,
Zan raira waƙa in yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji,
Allah na Isra’ila.
4 Ya Ubangiji, sa’ad da ka bar duwatsun Seyir,
Sa’ad da ka fito daga jihar Edom,
Ƙasa ta girgiza,
Ruwan sama ya zubo daga sararin sama,
I, gizagizai suka kwararo da ruwa.
5 Duwatsu suka girgiza a gaban Ubangijin Sina’i,
A gaban Ubangiji, Allah na Isra’ila.
6 A zamanin Shamgar ɗan Anat, a zamanin Yayel,
Ayarori suka daina bi ta ƙasar,
Matafiya suka bi ta ƙananan hanyoyi.
7 Garuruwan Isra’ila, ba kowa ciki,
Ba kowa ciki, sai da na zo.
Na zo kamar uwa ga Isra’ila,
8 Sa’ad da Isra’ilawa suka zaɓi baƙin alloli,
Sai ga yaƙi a ƙasar.
Ba a ga garkuwa ko mashi
A wurin mutum dubu arba’in na Isra’ila ba.
9 Zuciyata tana wajen shugabannin yaƙi na Isra’ila,
Da mutanen da suka ba da kansu da farin ciki.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
10 Ku ba da labari,
Ku da kuke haye da fararen jakuna,
Kuna zaune a shimfiɗu,
Ku da dole ku tafi da ƙafa duk inda za ku.
11 Ku kasa kunne! Da hayaniya mutane a bakin rijiyoyi
Suna ba da labarin nasarar Ubangiji,
Wato nasarar jama’ar Isra’ila!
Sa’an nan jama’ar Ubangiji
Suna tahowa daga biranensu.
12 Ki ja gaba, ke Debora, ki ja gaba!
Ki ja gaba! Ki raira waƙa, ki ja gaba!
Ka ci gaba, kai Barak,
Ɗan Abinowam, ka tasa kamammunka gaba!
13 Sa’an nan amintattu sun zo wurin shugabanninsu,
Jama’ar Ubangiji suka zo wurina a shirye domin yaƙi.
14 Daga Ifrraimu mutane suka gangaro zuwa kwari,
Bayan kabilar Biliyaminu da mutanenta.
Daga Makir shugabannin sojoji suka zo,
Daga Zabaluna kuma jarumawa suka gangaro.
15 Shugabannin Issaka suna tare da Debora,
Hakika, Issaka ya zo, Barak kuma ya zo,
Suka bi bayansu zuwa kwari.
Amma kabilar Ra’ubainu ta rarrabu,
Ba su shawarta su zo ba.
16 Don me suka tsaya daga baya tare da tumaki?
Don su saurari makiyaya na kiran garkuna?
Hakika kabilar Ra’ubainu ta rarrabu,
Ba su shawarta su zo ba.
17 Kabilar Gad suna tsaya a gabashin Urdun,
Kabilar Dan kuma ta tsaya a wuraren kiwo.
Kabilar Ashiru ta zauna a bakin teku,
Sun zauna a gefen teku.
18 Amma mutanen Zabaluna da na Naftali
Suka kasai da ransu a bakin dāga.
19 Sarakuna suka zo, suka yi yaƙi a Ta’anak,
A rafin Magiddo.
Sarakunan Kan’ana suka yi yaƙi,
Amma ba su kwashe azurfa ba.
20 Daga sama, taurari suka yi yaƙi,
Suna gilmawa a sararin sama
Suka yi yaƙi da Sisera.
21 Ambaliyar Kishon ta kwashe su,
Wato tsohon Kogin Kishon.
Zan yi gaba, in yi gaba da ƙarfi!
22 Sa’an nan dawakai sun yi ta rishi
Suna ƙwaƙular ƙasa da kofatansu.
23 Mala’ikan Ubangiji ya ce,
“Ka la’anta Meroz,
Ka la’anta mazauna cikinta sosai,
Gama ba su kawo wa Ubangiji gudunmawa ba,
Su zo su yi yaƙi kamar sojoji dominsa.”
24 Wadda ta fi kowa sa’a daga cikin mata, sai Yayel,
Matar Eber, Bakene,
Wadda ta fi kowa sa’a daga cikin matan da suke a alfarwai.
25 Sisera ya roƙi ruwan sha,
Sai ta ba shi madara,
Ta kawo masa kindirmo a kyakkyawar ƙwarya.
26 Ta ɗauki turken alfarwa a hannunta,
Ta riƙe guduma a guda hannun,
Ta bugi Sisera, kansa ya fashe,
Ta kwankwatse kansa, ya ragargaje.
27 Ya fāɗi a gwiwoyinta,
Ya fāɗi ƙasa, yana kwance shiru a ƙafafunta.
A ƙafafunta ya sunkuya ya fāɗi,
Ya fāɗi matacce har ƙasa.
28 Mahaifiyar Sisera ta duba ta tagogi,
Ta leƙa ta kariyar taga, ta ce,
“Me ya sa karusarsa ta yi jinkirin zuwa?
Don me dawakansa ba su komo da wuri ba?”
29 ‘Yan matanta mafi hikima suka amsa mata,
Ita kuwa ta yi nanatawa, tana cewa,
30 “Nema suke kurum su sami ganima, su raba,
Yarinya ɗaya ko biyu domin kowane soja,
Tufafi masu tsada domin Sisera,
Rinannun tufafi masu ado domin sarauniya.”
31 Ta haka, ya Ubangiji ka sa maƙiyanka su mutu,
Amma abokanka su haskaka kamar fitowar rana!
Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba’in.