1 Mutanen Ifraimu suka ce wa Gidiyon, “Me ke nan ka yi mana, da ba ka kirawo mu lokacin da ka tafi yaƙi da Madayanawa ba?” Suka yi masa gunaguni ƙwarai.
2 Amma ya ce musu, “Yanzu, me na yi fiye da ku? Ai, kalar inabin Ifraimu ta fi dukan girbin Abiyezer, wato ɗan abin da kuka yi ya fi wanda kabilata ta yi nesa.
3 Ga shi, Allah ya ba da Oreb da Ziyib sarakunan Madayanawa a gare ku. To, me na yi wanda ya fi naku?” Da ya faɗi haka, sai suka huce.
Nasara ta Ƙarshe a kan Madayanawa
4 Da Gidiyon ya zo Urdun sai ya haye tare da mutum ɗari uku ɗin nan da suke tare da shi. Ko da yake sun gaji, duk da haka suka yi ta runtumar magabta.
5 Gidiyon ya ce wa mutanen Sukkot, “Ina roƙonku, ku ba mutanen da suke tare da ni abinci, gama sun gaji, ga shi kuwa, ina runtumar Zeba da Zalmunna, sarakunan Madayanawa.”
6 Shugabannin Sukkot kuwa suka ce, “Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka abinci?”
7 Gidiyon ya ce, “To, sa’ad da Ubangiji ya ba da Zeba da Zalmunna a hannuna, zan tsattsaga jikinku da ƙayayuwan jeji.”
8 Daga can ya tafi Feniyel, ya roƙe su yadda ya roƙi mutanen Sukkot. Mutanen Feniyel kuma suka amsa masa daidai yadda mutanen Sukkot suka amsa masa.
9 Sai Gidiyon ya ce wa mutanen Feniyel, “Sa’ad da na dawo cikin salama, zan rushe wannan hasumiya.”
10 Zeba da Zalmunna kuwa suna Karkor tare da rundunarsu, mutum wajen dubu goma sha biyar (15,000), waɗanda suka ragu daga cikin rundunar mutanen gabas, gama an kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000), masu takuba.
11 Gidiyon kuwa ya bi ta hanyar gefen hamada wadda take gabas da Noba da Yogbeha, ya faɗa wa rundunar, ta yadda ba su zato.
12 Zeba da Zalmunna, sarakunan nan biyu na Madayana suka gudu, amma ya bi su, ya kamo su. Ya sa dukan rundunarsu ta gigice.
13 Sa’an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya komo daga yaƙin ta hanyar hawan Heres.
14 Gidiyon ya kama wani saurayi na Sukkot, ya yi masa tambayoyi. Shi kuwa ya rubuta masa sunayen sarakuna da na dattawan Sukkot, mutum saba’in da bakwai.
15 Sa’an nan ya zo wurin mutanen Sukkot ya ce musu, “To, ga Zeba da Zalmunna waɗanda kuka yi mini ba’a saboda su, kuna cewa, ‘Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka da suka gaji abinci?’ To, ga su!”
16 Ya kama dattawan garin Sukkot ya hukunta su da ƙayayuwa.
17 Ya kuma rushe hasumiyar Feniyel, ya karkashe mutanen birnin.
18 Sa’an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka kashe a Tabor?”
Suka amsa, “Kamar yadda kake, haka suke. Suna kama da ‘ya’yan sarki.”
19 Gidiyon ya ce musu, “Su ‘yan’uwana ne, mahaifiyarmu ɗaya. Da ba ku kashe su ba, da ba zan kashe ku ba.”
20 Ya ce wa Yeter, ɗan farinsa, “Tashi, ka kashe su.” Amma saurayin bai zare takobinsa ba, gama yana jin tsoro domin shi yaro ne.
21 Sai Zeba da Zalmunna suka ce, “Tashi da kanka, ka kashe mu, gama yadda mutum yake haka kuma ƙarfinsa yake.” Gidiyon kuwa ya tashi ya kashe Zeba da Zalmunna. Ya kwance kayan ado daga wuyan raƙumansu.
Sauran Ayyukan Gidiyon
22 Sa’an nan mutanen Isra’ila suka ce wa Gidiyon, “Ka yi mulkinmu, kai da ‘ya’yanka, da jikokinka, gama ka cece mu daga hannun Madayanawa.”
23 Gidiyon ya ce musu, “Ba zan yi mulkinku ba, ɗana kuma ba zai yi mulkinku ba, Ubangiji ne zai yi mulkinku.”
24 Ya ci gaba ya ce, “Ina roƙon kowannenku ya ba ni ‘yan kunne daga cikin ganimar da ya kwaso.” (Gama Madayanawa suna da ‘yan kunne na zinariya, gama su mutanen hamada ne.)
25 Suka ce, “Lalle, za mu ba ka su.” Nan da nan suka shimfiɗa mayafi, kowa ya zuba ‘yan kunnen da ya kwaso ganima.
26 Nauyin ‘yan kunnen zinariya da ya roƙa ya kai shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), banda kayan ado, da na rataye-rataye, da tufafin shunayya waɗanda sarakunan Madayanawa suke sawa, banda ɗan gaba da yake a wuyan raƙumansu.
27 Gidiyon kuwa ya yi gunki da zinariyar, ya ajiye a birninsa, wato Ofra. Isra’ilawa kuma suka bar bin Allah, suka tafi can domin su yi wa gunkin sujada, ya zama tarko ga Gidiyon da iyalinsa.
28 Da haka Isra’ilawa suka mallaki Madayanawa har ba su zamar musu barazana ba. Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba’in a zamanin Gidiyon.
Mutuwar Gidiyon
29 Gidiyon kuwa ya tafi ya zauna a gidansa na kansa.
30 Yana kuma da ‘ya’ya maza saba’in, gama yana da mata da yawa.
31 Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take a Shekem, ta haifi masa ɗa, ya sa masa suna Abimelek.
32 Sa’an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya rasu da kyakkyawan tsufa. Aka binne shi a kabarin Yowash mahaifinsa, a Ofra, birnin kabilar Abiyezer.
33 Bayan rasuwar Gidiyon, sai Isra’ilawa suka sāke yin rashin aminci ga Allah, suka yi wa Ba’al sujada. Suka yi Ba’al-berit ya zama allahnsu.
34 Suka daina bauta wa Ubangiji Allahnsu, wanda ya cece su daga magabtan da suke kewaye da su.
35 Ba su kuwa sāka wa iyalin Gidiyon da alheri ba, saboda dukan alherin da ya yi wa Isra’ilawa.