Al’adar Makokin da Aka Hana
1 “Ku ‘ya’ya ne ga Ubangiji Allahnku, kada ku yi wa jikinku zāne, kada kuma ku yi wa kanku sanƙo saboda wani wanda ya rasu.
2 Gama ku keɓaɓɓun mutane ne na Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku kuwa ya zaɓo ku daga cikin dukan al’umman duniya ku zama mutanensa, wato abin gādonsa.”
Halattattun Dabbobi da Haramtattu
3 “Kada ku ci abin da yake haram.
4 Ga dabbobin da za ku ci, da saniya, da tunkiya, da akuya,
5 da mariri, da barewa, da mariya, da mazo, da makwarna, da gada, da ɓauna, da ragon dutse.
6 Za ku iya cin kowace dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take tuƙa.
7 Amma duk da haka cikin waɗanda suke tuƙa, da waɗanda suke da rababben kofato ba za ku ci raƙumi, da zomo, da rema ba, ko da yake suna tuƙa, amma ba su da rababben kofato. Haram ne su a gare ku.
8 Ba kuma za ku ci alade ba, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa. Haram ne shi a gare ku. Kada ku ci naman irin waɗannan dabbobi, ko ku taɓa mushensu.
9 “Daga dukan irin abin da yake zaune a ruwa za ku iya cin duk abin da yake da ƙege da ɓamɓaroki.
10 Kada ku ci duk irin abin da ba shi da ƙege ko ɓamɓaroki, gama haram yake a gare ku.
11 “Kuna iya cin dukan halattattun tsuntsaye.
12 Amma waɗannan tsuntsaye ne ba za ku ci ba, mikiya, da gaggafa, da ungulun kwakwa,
13 da duki, da buga zabi, da kowace irin shirwa,
14 da kowane irin hankaka,
15 da jimina, da ƙururu, da bubuƙuwa, da kowane irin shaho,
16 da mujiya, da babbar mujiya, da ɗuskwi,
17 da kwasakwasa, da ungulu, da dimilmilo,
18 da zalɓe, da kowane irin jinjimi, da katutu, da yaburbura.
19 “Dukan ‘yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe haram ne a gare ku, kada ku ci su.
20 Za ku iya cin duk abin da yake da fikafikai in dai shi halattacce ne.
21 “Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama’a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku.
“Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”
Dokar Zakar
22 “Ku fitar da zakar dukan amfanin da kuka shuka a gonarku kowace shekara.
23 Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da ‘yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada.
24 Idan ya zamana wurin ya yi muku nisa, har ba za ku iya kai zakar a wurin ba, saboda wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa ya yi muku nisa sa’ad da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka,
25 to, sai ku sayar da zakar, ku tafi da kuɗin wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa,
26 ku kashe kuɗin a kan duk abin da kuke so, ko sa ne, ko tunkiya, ko ruwan inabi, ko abin sha mai gafi, ko dai duk irin abin da ranku yake so. Nan za ku yi liyafa a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi murna tare da iyalan gidanku.
27 “Amma fa, kada ku manta da Balawen da yake garuruwanku gama ba shi da gādo kamarku.
28 A ƙarshen kowace shekara uku, sai ku kawo dukan zakar abin da kuka girbe a wannan shekara, ku ajiye a ƙofofinku.
29 Sa’an nan sai Balawe, da yake shi ba shi da gādo kamarku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune a garuruwanku, su zo, su ci, su ƙoshi, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka cikin dukan aikin da hannunku zai yi.”