1 “Idan kun ga ɓataccen san wani, ko tunkiyarsa, to, kada ku ƙyale shi, amma lalle sai ku komar da shi ga mai shi.
2 Idan mutumin ba kusa da ku yake zaune ba, ko kuma ba ku san shi ba, to, sai ku kawo dabbar a gidanku, ta zauna a wurinku, har lokacin da mutumin ya zo ya shaida ta, sa’an nan ku ba shi.
3 Haka nan kuma za ku yi da jakinsa, da riga, da kowane abin wani da ya ɓace, ku kuwa kuka tsinta. Faufau, kada ku ƙyale su.
4 “Idan kun ga jakin wani ko sansa ya faɗi a hanya, kada ku ƙyale shi, sai ku taimake shi ku tashe shi.
5 “Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata. Duk mai yin haka, abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.
6 “Idan kuna tafiya a hanya, kun ga sheƙar tsuntsu a itace, ko a ƙasa, da ‘ya’yanta, ko da ƙwayaye a ciki, uwar kuma tana kwance bisa ‘ya’yan ko ƙwayayen, kada ku kama uwar duk da ‘ya’yan.
7 Sai ku bar uwar ta tafi, amma kun iya kwashe ‘ya’yan. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.
8 “Sa’ad da kuka gina sabon gida, sai ku ja masa rawani don kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya fāɗi daga bisa.
9 “Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku don kada abin da kuka shuka da amfanin gonar inabinku su zama haramiyarku.
10 “Kada ku haɗa sa da jaki su yi huɗa tare.
11 “Kada ku sa rigar da aka saƙa da ulu garwaye da lilin.
12 “Sai ku yi wa rigar da kukan sa tuntu huɗu, tuntu ɗaya a kowace kusurwa.
Dokoki a kan Hana Lalata
13 “Idan mutum ya auri mace, ya shiga wurinta, sa’an nan ya ƙi ta,
14 yana zarginta da cewa ta yi abin kunya, yana ɓata mata suna a fili, yana cewa, ‘Na auri wannan mata, amma sa’ad da na kusace ta, sai na iske ita ba budurwa ba ce,’
15 sai mahaifinta da mahaifiyarta su kawo shaidar budurcin yarinyar a gaban dattawan garin a dandalin ƙofar garin.
16 Sai mahaifinta ya ce wa dattawan, ‘Na ba wannan mutum ‘yata aure, amma ya ƙi ta.
17 Yana zarginta da aikata abin kunya, ya ce, bai iske ‘yarmu budurwa ba. Amma ga shaidar budurcin ‘yata.’ Sai su shimfiɗa tsalala a gaban dattawan.
18 Sai dattawan garin su kama mutumin su yi masa bulala,
19 su ci shi tara shekel ɗari na azurfa, su ba mahaifin yarinyar, gama a fili mutumin ya ɓata sunan budurwar cikin Isra’ila. Za ta zama matarsa, ba shi da iko ya sake ta muddin ransa.
20 “Idan aka tabbatar zargin gaskiya ne, ba a kuma ga shaidar budurcinta ba,
21 sai a kai yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, sa’an nan mutanen garin su jajjefe ta da duwatsu har ta mutu, don ta yi aikin wauta cikin Isra’ila, gama ta yi karuwanci a gidan mahaifinta. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.
22 “Idan aka iske wani yana kwance da matar wani, sai a kashe dukansu biyu, wato mutumin da matar. Haka za ku kawar da mugunta daga Isra’ila.
23 “Idan a cikin gari wani ya iske budurwar da ake tashinta, ya kwana da ita,
24 sai a kawo su, su biyu ɗin, a dandalin ƙofar gari, ku jajjefe su da duwatsu har su mutu, don yarinyar tana cikin gari, amma ba ta yi kururuwa a taimake ta ba, don kuma mutumin ya ɓata budurwar maƙwabcinsa. Da haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.
25 “Amma idan a saura wani ya fāɗa wa yarinyar da ake tashinta, har ya kwana da ita ƙarfi da yaji, sai a kashe wannan mutum.
26 Amma ita yarinyar ba za a yi mata kome ba, domin ba ta yi laifin da ya isa mutuwa ba, gama wannan shari’a daidai take da ta mutumin da ya faɗa wa maƙwabcinsa ya kashe shi.
27 Gama sa’ad da ya same ta a saura, ita wadda ake tashinta ta yi kururuwa, amma ba wanda zai cece ta.
28 “Idan wani ya iske yarinyar da ba a tashinta, ya kama ta, ya kwana da ita, aka kuwa same su,
29 to, sai wanda ya kwana da ita ya ba mahaifinta shekel hamsin na azurfa, ita kuwa za ta zama matarsa, gama ya ci mutuncinta. Ba zai sake ta ba muddin ransa.
30 “Kada mutum ya auri matar mahaifinsa, kada kuma ya kware fatarinta, gama na mahaifinsa ne.”