Waɗanda Za a Ware daga Cikin Taron Jama’a
1 “Duk wanda aka dandaƙe ko wanda aka yanke gabansa ba zai shiga taron jama’ar Ubangiji ba.
2 “Shege ba zai shiga taron jama’ar Ubangiji ba. Har tsara ta goma zuriyarsa ba za su shiga taron jama’ar Ubangiji ba.
3 “Kada Ba’ammone ko Bamowabe ya shiga taron jama’ar Ubangiji. Har tsara ta goma ta zuriyarsu ba za su shiga taron jama’ar Ubangiji ba.
4 domin ba su zo sun tarye ku, su kawo muku abinci da ruwa ba sa’ad da kuke a hanyarku, lokacin da kuka fito daga Masar. Ga shi kuma, sun yi ijara da Bal’amu ɗan Beyor daga Fetor ta Mesofatamiya ya zo ya la’anta ku.
5 Amma Ubangiji Allahnku ya ƙi saurarar Bal’amu, sai Ubangiji ya juyar da la’anar ta zama muku albarka saboda Ubangiji Allahnku yana ƙaunarku.
6 Har abada kada ku nemar musu zaman lafiya ko wadata.
7 “Kada ku ji ƙyamar Ba’edome gama shi danginku ne. Kada kuma ku ji ƙyamar Bamasare don kun yi baƙunci a ƙasarsa.
8 ‘Ya’yansu tsara ta uku, za su iya shiga taron jama’ar Ubangiji.”
Kiyaye Sansanin Yaƙi da Tsabta
9 “Sa’ad da kuka kafa sansani don ku yi yaƙi da magabtanku, sai ku kiyaye kanku daga kowane mugun abu.
10 Idan wani a cikinku ya ƙazantu saboda ya zubar da maniyyi da dare, to, sai ya fita daga sansanin, kada ya koma sansanin.
11 Amma da maraice, sai ya yi wanka da ruwa, ya koma sansani sa’ad da rana ta faɗi.
12 “Za ku keɓe wani wuri a bayan sansani inda za ku riƙa zagayawa.
13 Sai ku ɗauki abin tona ƙasa tare da makamanku. Lokacin da za ku zagaya garin yin najasa, sai ku tsuguna ku tona rami da abin tona ƙasa sa’an nan ku rufe najasar da kuka yi.
14 Gama Ubangiji Allahnku yakan yi yawo cikin sansaninku don ya cece ku, ya ba da magabtanku cikin hannunku. Saboda haka dole ku tsabtace sansaninku don kada Ubangiji ya iske wata ƙazanta a cikinku, ya rabu da ku.”
Waɗansu Dokoki
15 “Kada ku ba da bawan da ya tsere, ya zo gare ku, ga ubangijinsa.
16 Zai zauna a wurinku. Sai ya zauna tare da ku, a wurin da ya zaɓa cikin garuruwanku inda ya fi so. Kada ku dame shi.
17 “Kada Isra’ilawa mata da maza su shiga ƙungiyar karuwanci na addini.
18 Kada ku kawo kuɗin da aka samu ta wurin karuwanci, ko kuɗin da aka samu ta wurin yin luɗu a Haikalin Ubangiji don biyan wa’adin da kuka riga kuka yi, gama wannan abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.
19 “Kada ku ba danginku rance da ruwa, ko rancen kuɗi ne, ko na abinci, ko na kowane irin abu da akan ba da shi da ruwa.
20 Kun iya ba baƙo rance da ruwa, amma kada ku ba danginku rance da ruwa don Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan abin da za ku yi a ƙasar da kuke shiga, ku kuma mallake ta.
21 “Idan kun yi wa Ubangiji Allahnku wa’adi, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama Ubangiji Allahnku zai neme shi a gare ku, ba kuwa zai zama zunubi a gare ku ba.
22 Idan kun nisanci yin wa’adi, ba zai zama zunubi gare ku ba.
23 Sai ku cika duk abin da kuka faɗa da bakinku, gama da yardarku ne kuka yi wa Ubangiji Allahnku wa’adi wanda kuka alkawarta.
24 “Sa’ad da kuka shiga gonar inabin maƙwabcinku, kuna iya cin ‘ya’yan inabin, har ku ƙoshi yadda kuke so, amma kada ku sa wani a jakarku.
25 Sa’ad da kuka shiga hatsin maƙwabcinku da yake tsaye, kun iya ku yi murmuren tsabar da hannunku, amma kada ku sa wa hatsin maƙwabcinku lauje.”