Dokar Kisan Aure
1 “Idan mutum ya sami wata mata ya aura, amma idan ba ta gamshe shi ba saboda ya iske wani abu marar kyau game da ita, har ya ba ta takardar saki a hannunta, ya sallame ta daga gidansa,
2 ta kuwa fita gidansa, idan ta je ta auri wani mutum dabam,
3 idan shi kuma ya ƙi ta, ya ba ta takardar saki a hannunta, ya sallame ta daga gidansa, ko kuma idan ya mutu ne,
4 to, kada mijinta na fari wanda ya sake ta, ya sāke aurenta, tun da yake ta ƙazantu. Gama wannan abar ƙyama ce a wurin Ubangiji. Kada ku jawo alhaki a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda.
5 “Idan mutum ya yi sabon aure, kada ya tafi yaƙi tare da sojoji, ko kuma a sa shi kowane irin aiki. Sai ya huta a gida har shekara ɗaya saboda gidansa, don ya faranta wa matar da ya auro zuciya.”
Waɗansu Dokoki
6 “Kada mutum ya karɓi jinginar dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa, gama yin haka karɓar jinginar rai ne.
7 “Idan aka iske mutum yana satar danginsa Ba’isra’ile don ya maishe shi bawansa, ko ya sayar da shi, sai a kashe ɓarawon. Ta haka za ku kawar da mugunta daga tsakiyarku.
8 “Game da ciwon kuturta, sai ku lura ku bi daidai da yadda firistoci na Lawiyawa suka umarce ku, ku yi. Sai ku kiyaye, ku aikata yadda na umarce su.
9 Ku tuna da abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Maryamu a lokacin da kuka fito daga Masar.
10 “Idan kun ba maƙwabcinku rance na kowane iri, kada ku shiga gidansa don ku ɗauki jingina.
11 Sai ku tsaya a waje, mutumin da kuka ba shi rancen zai kawo muku jinginar.
12 Amma kada ku yarda abin da aka jinginar ya kwana a wurinku idan mutumin matalauci ne.
13 Sai ku mayar masa da shi a faɗuwar rana domin ya yi barci yafe da rigarsa ya gode muku. Yin haka zai zama muku adalci a wurin Ubangiji Allahnku.
14 “Kada ku zalunci ɗan ƙodago wanda yake matalauci, ko shi danginku ne, ko kuwa baƙon da yake zaune a garuruwan ƙasarku.
15 Sai ku biya shi hakkinsa a ranar da ya yi aikin, kafin faɗuwar rana, gama shi matalauci ne, zuciyarsa tana kan abin hakkinsa, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har ya zama laifi a gare ku.
16 “Kada a kashe ubanni maimakon ‘ya’ya, kada kuma a kashe ‘ya’ya maimakon ubanni. Amma za a kashe mutum saboda laifin da ya aikata.
17 “Kada ku karkatar da shari’ar baƙo ko maraya. Kada kuma ku karɓi mayafin matar da mijinta ya rasu abin jingina.
18 Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku ya fanshe ku daga can, saboda haka ina umartarku ku yi wannan.
19 “Idan kun manta da wani dami a gona lokacin girbin amfanin gona, kada ku koma ku ɗauko. Ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan aikin hannuwanku.
20 Sa’ad da kuka kakkaɓe ‘ya’yan zaitunku, kada ku sāke bin rassan kuna kakkaɓewa, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske.
21 Sa’ad da kuka girbe gonar inabinku kada kuma ku yi kala, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske.
22 Sai ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, don haka nake umartarku ku yi wannan.”