1 “Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari’a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin,
2 idan mai laifin ya cancanci bulala, sai alƙali ya sa shi ya kwanta ƙasa, a bulale shi a gabansa daidai yawan bulalar da ta dace da irin laifin da ya yi.
3 Za a iya yi masa bulala arba’in, amma kada ta fi haka, don kada a ci gaba da bugunsa fiye da haka, har ya zama rainanne a idonku.
4 “Kada ku yi wa takarkari takunkumi sa’ad da yake tattaka hatsinku.”
Gādon Aure
5 “Idan ‘yan’uwa suna zaune wuri ɗaya tare, in ɗayansu ya rasu bai haihu ba, to, kada matar marigayin ta auri wani baƙo wanda yake ba a cikin dangin mijin ba. Sai ɗan’uwan mijinta ya zo wurinta, ya aure ta, ya yi mata abin da ya kamaci ɗan’uwan miji ya yi.
6 Ɗan farin da za ta haifa, zai zama magajin marigayin don kada a manta da sunansa cikin Isra’ila.
7 Amma idan mutum ya ƙi ya auri matar ɗan’uwansa, marigayi, sai matar ta tafi wurin dattawa a dandalin ƙofar gari, ta ce, ‘Ɗan’uwan mijina, marigayi, ya ƙi wanzar da sunan ɗan’uwansa cikin Isra’ila, gama ya ƙi yi mini abin da ya kamaci ɗan’uwan marigayi, ya yi.’
8 Sai dattawan garin su kira mutumin, su yi masa magana. Idan ya nace, yana cewa, ‘Ba na so in aure ta,’
9 sai matar ɗan’uwansa, marigayi, ta tafi wurinsa a gaban dattawan, ta kwaɓe takalmin ƙafarsa, ta tofa masa yau a fuskarsa, ta ce, ‘Haka za a yi wa wanda ya ƙi kafa gidan ɗan’uwansa.’
10 Za a kira sunan gidansa cikin Isra’ila, ‘Gidan wanda aka kwaɓe masa takalmi.’ ”
Waɗansu Dokoki
11 “Idan mutane biyu suna faɗa da juna, idan matar mutum ɗaya daga cikinsu ta zo don ta taimaki mijinta, idan ta kama marainan wancan mutum da hannunta,
12 sai ku yanke hannunta, kada ku ji tausayi.
13 “Kada ku riƙe ma’aunin nauyi iri biyu a jakarku, wato babba da ƙarami.
14 Kada kuma ku ajiye mudu iri biyu a gidanku, wato babba da ƙarami.
15 Sai ku kasance da ma’aunin nauyi da mudu masu kyau don ku daɗe a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.
16 Gama duk wanda yake aikata irin waɗannan abubuwa, da dukan marasa gaskiya, abin ƙyama ne su ga Ubangiji Allahnku.”
A Karkashe dukan Amalekawa
17 “Ku tuna da abin da Amalekawa suka yi muku a hanya, lokacin da kuka fito daga Masar.
18 Yadda suka yi muku kwanto a hanya, suka fāɗa muku ta baya, suka karkashe waɗanda suka gaji tiɓis. Ba su ko ji tsoron Allah ba.
19 Domin haka sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa daga dukan magabtanku da suke kewaye da ku a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, abar gādo, to, sai ku shafe Amalekawa daga duniya, don kada a ƙara tunawa da su. Kada fa ku manta.”