Abin da Za a Yi da Nunan Fari da Zaka
1 “Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda, kuka mallake ta, kuka zauna cikinta,
2 to, sai ku keɓe nunan fari na dukan amfanin ƙasa wanda kuka shuka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Ku sa cikin kwando, ku tafi inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa.
3 Ku je wurin firist wanda yake aiki a lokacin, ku ce, ‘Yau, na sakankance a gaban Ubangiji Allahnka, cewa na shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninmu zai ba mu.’
4 “Sa’an nan firist ya karɓi kwandon daga gare ku ya sa shi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku.
5 Sa’an nan kuma sai ku hurta waɗannan kalmomi a gaban Ubangiji Allahnku, ku ce, ‘Ubana Ba’aramiye ne, mayawaci a dā. Ya gangara zuwa Masar yana da jama’a kima, ya yi baƙunci a wurin. Amma a can ya zama al’umma mai girma, mai iko, mai yawa.
6 Masarawa suka wulakanta mu, suka tsananta mana, suka bautar da mu.
7 Amma muka yi kuka ga Ubangiji Allah na kakanninmu. Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya ga azabarmu, da wahalarmu, da zaluncin da ake yi mana.
8 Sai Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantsensa mai ƙarfi, mai iko, tare da bantsoro, da alamu, da mu’ujizai.
9 Ubangiji ya kawo mu nan, ya ba mu ƙasar nan, ƙasar da take mai yalwar abinci.
10 Ga shi, yanzu mun kawo nunan fari na amfanin ƙasar, da kai, ya Ubangiji, ka ba mu.’
“Sai ku ajiye shi a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi sujada a gaban Ubangiji Allahnku.
11 Ku yi murna kuma, ku da Lawiyawa, da baƙin da suke zaune tare da ku, saboda dukan alherin da Ubangiji Allah ya yi muku, ku da gidanku.
12 “Sa’ad da kuka gama fitar da zakarku ta amfanin gona a shekara ta uku, wadda take shekara ta fid da zaka, sai ku ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu, don su ci, su ƙoshi a cikin garuruwanku.
13 Sa’an nan za ku ce a gaban Ubangiji Allahnku, ‘Na fitar da tsattsarkan kashi daga cikin gidana na ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu bisa ga umarnin da ka yi mini. Ban karya wani umarninka ba, ban kuwa manta da su ba.
14 Ban ci kome daga cikin zakar sa’ad da nake baƙin ciki ba, ban kuma fitar da kome daga cikinta ba sa’ad da nake da ƙazanta, ban kuma miƙa wa matattu kome daga cikinta ba. Na yi biyayya da muryar Ubangiji Allahna, na aikata dukan abin da ka umarce ni.
15 Ka duba ƙasa daga Sama, daga wurin zamanka mai tsarki, ka sa wa jama’arka, Isra’ila, albarka duk da ƙasar da ka ba mu, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda ka rantse wa kakanninmu.’ ”
Tsattsarkar Jama’a ta Ubangiji
16 “Yau Ubangiji Allahnku yana umartarku ku kiyaye waɗannan dokoki da farillai. Sai ku lura ku aikata su da dukan zuciyarku da dukan ranku.
17 Yau kun shaida, cewa Ubangiji shi ne Allahnku, za ku yi tafiya cikin tafarkunsa, za ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da farillansa, za ku kuma yi masa biyayya.
18 Yau kuma Ubangiji ya shaida, cewa ku ne jama’arsa ta musamman, kamar yadda ya alkawarta muku. Ku kuwa za ku kiyaye dukan umarnansa.
19 Shi kuwa zai ɗaukaka ku ku zama abin yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al’umman da ya yi. Za ku zama jama’a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku kamar yadda ya faɗa.”