Za a Rubuta Dokoki a Dutsen Ebal
1 Musa da dattawan Isra’ila suka umarci jama’a, suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai waɗanda na umarce ku da su yau.
2 Bayan da kuka haye Urdun, kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku kakkafa manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa.
3 Sai ku rubuta kalmomin wannan shari’a a kansu daidai lokacin da kuka haye ku shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta wa kakanninku.
4 Sa’ad da kuka haye Urdun ɗin sai ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal bisa ga umarnin da na yi muku yau. Ku yi musu shafe da farar ƙasa.
5 Can za ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a taɓa sassaƙa su da baƙin ƙarfe ba.
6 Sai ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a sassaƙa ba. A bisa wannan bagade za ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku.
7 Za ku kuma miƙa hadayu na salama ku ci a wurin, ku yi ta murna a gaban Ubangiji Allahnku.
8 Sai ku rubuta dukan kalmomin waɗannan dokoki su fita sosai bisa duwatsun nan.”
9 Sai Musa da Lawiyawan da suke firistoci, suka ce wa Isra’ilawa, “Ku ji. Yau kun zama jama’ar Ubangiji Allahnku.
10 Sai ku saurari muryar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye umarnansa, da dokokinsa waɗanda muke umartarku da su yau.”
La’ana a kan Dutsen Ebal
11 A wannan rana kuma Musa ya umarci jama’a, ya ce,
12 “Sa’ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama’a albarka, wato kabilar Saminu, da ta Lawi, da ta Yahuza, da ta Issaka, da ta Yusufu, da ta Biliyaminu.
13 Waɗannan za su tsaya a bisa kan Dutsen Ebal don su la’anta, wato kabilar Ra’ubainu, da ta Gad, da ta Ashiru, da ta Zabaluna, da ta Dan, da ta Naftali.
14 Sa’an nan Lawiyawa za su ta da murya, su ce wa dukan Isra’ilawa:
15 “ ‘La’ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana’a, ya kafa ta a ɓoye.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’
16 “ ‘La’ananne ne wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’
17 “ ‘La’ananne ne wanda ya ci iyakar maƙwabcinsa.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’
18 “ ‘La’ananne ne wanda ya karkatar da makaho daga hanya.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’
19 “ ‘La’ananne ne wanda ya yi wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa ta gaske shari’a ta rashin gaskiya.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’
20 “ ‘La’ananne ne wanda ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya buɗe fatarin matar mahaifinsa.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’
21 “ ‘La’ananne ne wanda ya kwana da dabba.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’
22 “ ‘La’ananne ne wanda ya kwana da ‘yar’uwarsa, wato ‘yar mahaifinsa, ko ‘yar mahaifiyarsa.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’
23 “ ‘La’ananne ne wanda ya kwana da surukarsa.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’
24 “ ‘La’ananne ne wanda ya buge maƙwabcinsa daga ɓoye.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!”
25 “ ‘La’ananne ne wanda aka yi ijara da shi don ya kashe marar laifi.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’
26 “ ‘La’ananne ne wanda bai yi na’am da kalmomin dokokin nan don ya yi aiki da su ba.’
“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’ ”