1 “Ku saurara, ya ku sammai, gama zan yi magana,
Bari duniya ta ji maganar bakina.
2 Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama,
Maganata ta faɗo kamar raɓa,
Kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa,
Kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye.
3 Gama zan yi shelar sunan Ubangiji,
In yabi girman Allahnmu!
4 “Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne,
Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne.
Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi,
Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
5 Sun aikata mugunta a gabansa,
Su ba ‘ya’yansa ba ne saboda lalacewarsu,
Su muguwar tsara ce, karkatacciya,
6 Haka za ku sāka wa Ubangiji,
Ya ku wawaye, mutane marasa hikima?
Ba shi ne Ubanku, Mahaliccinku ba,
Wanda ya yi ku, ya kuma kafa ku?
7 “Ku fa tuna da kwanakin dā,
Ku yi tunani a kan shekarun tsararraki,
Ku tambayi mahaifanku, su za su faɗa muku,
Ku tambayi dattawanku, su kuma za su faɗa muku,
8 Sa’ad da Maɗaukaki ya ba al’ummai gādonsu,
Sa’ad da ya raba ‘yan adam,
Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra’ilawa.
9 Gama rabon Ubangiji shi ne jama’arsa,
Yakubu shi ne rabon gādonsa.
10 “Ya same shi daga cikin hamada,
A jeji marar amfani, inda namomi suke kuka.
Ya kewaye shi, ya lura da shi,
Ya kiyaye shi kamar ƙwayar idonsa.
11 Kamar gaggafar da take kaɗa fikafikanta a kan sheƙarta,
Tana rufe da ‘yan tsakinta,
Ta buɗe fikafikanta, ta kama su,
Ta ɗauke su a bisa kafaɗunta.
12 Ubangiji ne kaɗai ya bishe shi,
Ba wani baƙon allah tare da shi.
13 “Ya sa shi ya hau kan tuddai,
Ya ci amfanin ƙasa,
Ya sa shi ya sha zuma daga dutse,
Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara.
14 Ya sami kindirmo daga shanu,
Da madara daga garken tumaki da na awaki,
Da kitse daga ‘yan raguna, da raguna,
Da bijimai, da bunsurai daga Bashan,
Da alkama mafi kyau.
Ka sha ruwan inabi jaja wur, mai kyau.
15 “Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska,
Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul.
Ya rabu da Allahn da ya yi shi,
Ya raina Dutsen Cetonsa.
16 Suka sa shi kishi, saboda gumaka,
Suka tsokani fushinsa da abubuwan banƙyama.
17 Suka miƙa hadayu ga aljannun da ba Allah ba,
Ga gumakan da ba su sani ba,
Sababbin allolin da aka shigo da su daga baya,
Waɗanda kakanninku ba su ji tsoronsu ba.
18 Kun ƙi kula da Dutsen da ya haife ku,
Kun manta da Allahn da ya ba ku rai.
19 “Ubangiji ya gani, ya raina su,
Saboda tsokanar da ‘ya’yansa mata da maza suka yi masa.
20 Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata,
Zan ga yadda ƙarshensu zai zama.
Gama su muguwar tsara ce,
‘Ya’ya ne marasa aminci.
21 Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba,
Suka tsokani fushina da gumakansu,
Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba.
Zan tsokane su da wawanyar al’umma.
22 Gama fushina ya kama wuta,
Tana ci har ƙurewar zurfin lahira.
Za ta cinye duniya da dukan amfaninta,
Za ta kama tussan duwatsu.
23 “ ‘Zan tula musu masifu,
Zan ƙare kibauna a kansu,
24 Za su lalace saboda yunwa,
Zazzaɓi mai zafi, da muguwar annoba za su cinye su.
Zan aika da haƙoran namomi a kansu,
Da dafin abubuwa masu jan ciki.
25 Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su,
A cikin ɗakuna kuma tsoro,
Zai hallaka saurayi da budurwa,
Da mai shan mama da mai furfura.
26 Na ce, “Zan watsar da su,
In sa a manta da su cikin mutane.”
27 Amma saboda gudun tsokanar maƙiyi,
Kada abokan gābansu su zaci su ne suka ci nasara.
Ai, ni ne na yi wannan.’
28 “Gama su al’umma ce wadda ba ta yin shawara,
Ba su da ganewa.
29 Da suna da hikima, da sun gane wannan,
Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama!
30 Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu,
Mutum biyu kuma su kori zambar goma,
Sai dai Dutsensu ya sayar da su,
Ubangiji kuma ya bashe su?
31 Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne,
Ko abokan gabanmu ma sun san haka.
32 Kurangar inabinsu daga kurangar inabin Saduma ne
Da gonakin Gwamrata.
‘Ya’yan inabinsu dafi ne,
Nonnansu masu ɗaci ne.
33 Ruwan inabinsu dafin macizai ne.
Da mugun dafin kumurci.
34 “ ‘Wannan ba a jibge suke a rumbunana ba,
A ƙulle kuma a taskokina?
35 Sakayya da ɗaukar fansa nawa ne,
A lokacin ƙafarsu za ta zame,
Gama ranar masifarsu ta kusa,
Hallakarsu za ta zo da sauri.’
36 Ubangiji zai ɗauka wa jama’arsa fansa,
Zai ji ƙan bayinsa,
Sa’ad da ya ga ƙarfinsu ya kāsa,
Ba kuma wanda ya ragu, bawa ko ɗa.
37 Sa’an nan zai ce, ‘Ina gumakansu,
Dutse wanda suka nemi mafaka gare shi,
38 Waɗanda suka ci kitsen hadayunsu,
Suka sha ruwan inabin hadayarsu ta sha?
Bari su tashi su taimake ku,
Bari su zama mafaka!
39 “ ‘Ku duba fa, ni ne shi,
Ba wani Allah, banda ni,
Nakan kashe, in rayar,
Nakan sa rauni, nakan kuma warkar,
Ba wanda zai cece su daga hannuna.
40 Na ɗaga hannuna sama,
Na rantse da madawwamin raina,
41 Sa’ad da na wasa takobina mai walƙiya,
Na riƙe shi da hannuna don yin hukunci,
Zan ɗauki fansa a kan magabtana
Zan sāka wa maƙiyana.
42 Zan sa kibauna su bugu da jini,
Takobina zai ci nama,
Da jinin kisassu da na kamammu,
Da ƙoƙon kan shugabannin maƙiya.’
43 “Ya ku al’ummai, ku yabi jama’arsa,
Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu,
Zai ɗauki fansa a kan magabtansa,
Zai tsarkake ƙasar jama’arsa.”
Gargaɗin Musa na Ƙarshe
44 Sai Musa da Joshuwa ɗan Nun suka zo, suka hurta dukan kalmomin wannan waƙa a kunnen jama’a.
45 Sa’ad da Musa ya gama hurta waɗannan kalmomi ga Isra’ila,
46 ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci ‘ya’yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai.
47 Wannan ba magana kurum ba ce, amma ranku ne. Ta wurin wannan magana ce za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun zuwa ciki don ku mallake ta.”
An Yarda wa Musa Ya Hangi Ƙasar Kan’ana
48 A wannan rana ce Ubangiji ya ce wa Musa,
49 “Ka hau duwatsun Abarim, wato Dutsen Nebo wanda yake a ƙasar Mowab, daura da Yariko, ka duba ƙasar Kan’ana wadda zan ba Isra’ilawa su mallaka.
50 Za ka rasu a kan dutsen da za ka hau, za a kai ka wurin mutanen da suka riga ka gidan gaskiya, kamar yadda ɗan’uwanka, Haruna, ya rasu a Dutsen Hor, aka kai shi wurin mutanensa waɗanda suka riga shi gidan gaskiya.
51 Gama ba ku amince da ni ba a gaban mutanen Isra’ila a wurin ruwan Meriba ta Kadesh a jejin Zin a wannan lokaci, domin ba ku nuna tsarkina a gaban jama’ar Isra’ila ba.
52 Za ka ga ƙasar da nake ba jama’ar Isra’ila, amma ba za ka shiga cikinta ba.”