Musa Ya Sa wa Kabilan Isra’ila Albarka
1 Wannan ita ce albarkar da Musa, mutumin Allah, ya sa wa Isra’ilawa kafin ya rasu.
2 Ya ce,
“Ubangiji ya taho daga Sina’i,
Daga Dutsen Faran kuma ya haskaka,
Ya taho tare da dubban tsarkakansa,
Da harshen wuta a damansa.
3 Hakika, yana ƙaunar jama’arsa,
Dukan tsarkaka suna a ikonka,
Suna biye da kai,
Suna karɓar umarninka.
4 Musa ya ba mu dokoki,
Abin gādo ga taron jama’ar Yakubu.
5 Ubangiji shi ne sarki a Yeshurun,
Sa’ad da shugabanni suka taru,
Dukan kabilan Isra’ila suka taru.
6 “Allah ya sa Ra’ubainu ya rayu, kada ya mutu,
Kada mutanensa su zama kaɗan.”
7 A kan Yahuza ya ce,
“Ka ji muryar Yahuza, ya Ubangiji,
Ka kawo shi wurin jama’arsa.
Ka yi yaƙi da ikonka dominsu,
Ka taimake shi a kan maƙiyansa.”
8 A kan Lawi ya ce,
“Ka ba Mai Tsarki Tumminka da Urim naka,
Shi wanda ka jarraba a Masaha,
Wanda ka yi jayayya da shi a ruwan Meriba,
9 Wanda ya ce wa mahaifinsa da mahaifiyarsa,
‘Ban kula da ku ba.’
Ya ce wa ‘yan’uwansa su ba nasa ba ne.
Ya kuma ƙyale ‘ya’yansa,
Domin sun kiyaye maganarka,
Sun riƙe alkawarinka.
10 Suna koya wa Yakubu farillanka,
Suna koya wa Isra’ila dokokinka.
Suna ƙona turare a gabanka,
Suna ƙona hadaya ta ƙonawa a bagadenka.
11 Ya Ubangiji ka inganta jaruntakarsu,
Ka karɓi aikin hannuwansu,
Ka murƙushe ƙarfin abokan gābansu,
Da waɗanda suke ƙinsu don kada su ƙara tashi.”
12 A kan Biliyaminu, ya ce,
“Shi ƙaunatacce na Ubangiji ne,
Yana zaune lafiya kusa da shi,
Ubangiji yana yi masa garkuwa dukan yini,
Yana zaune a kan kafaɗunsa.”
13 A kan Yusufu, ya ce,
“Ubangiji ya sa wa ƙasarsa albarka,
Da kyawawan kyautai daga sama, da raɓa,
Da ruwan da yake a ƙasa,
14 Da kyawawan kyautan da rana take bayarwa,
Da kyawawan kyautan da watanni suke bayarwa,
15 Da abubuwa mafi kyau na duwatsun dā,
Da kyawawan kyautai na madawwaman tuddai.
16 Da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta,
Da alherin wanda yake zaune a jeji.
Bari waɗannan kyautai su sauka a kan Yusufu,
A kan wanda yake keɓaɓɓe daga cikin ‘yan’uwansa.
17 Darajarsa kamar ta ɗan farin bijimi take,
Ƙahoninsa kamar na ɓauna suke,
Da su yake tunkwiyin mutane,
Zai tura su zuwa ƙurewar duniya,
Haka fa rundunan Ifraimu za su zama,
Haka kuma dubban Manassa za su zama.”
18 A kan Zabaluna ya ce,
“Ka yi murna da tafiye-tafiyenka, ya Zabaluna,
Kai kuma Issaka, cikin alfarwanka.
19 Za su kira mutane zuwa dutse,
Can za su miƙa hadayu masu dacewa,
Gama za su ɗebo wadatar tekuna,
Da ɓoyayyun dukiyar yashi.”
20 A kan Gad, ya ce,
“Mai albarka ne wanda ya fāɗaɗa Gad,
Gad yana sanɗa kamar zaki,
Yana yayyage hannu da ƙoƙon kai.
21 Zai zaɓar wa kansa wuri mai kyau,
Gama wurin ne aka keɓe wa shugaba.
Ya zo wurin shugabannin mutane,
Tare da Isra’ila, ya aikata adalcin Ubangiji,
Ya kiyaye farillansa.”
22 A kan Dan, ya ce,
“Dan ɗan zaki ne,
Mai tsalle daga Bashan.”
23 A kan Naftali, ya ce,
“Ya Naftali, ƙosasshe kake da alheri,
Cike kake da albarkar Ubangiji.
Sai ka mallaki tafki da wajen kudu.”
24 A kan Ashiru, ya ce,
“Ashiru mai albarka ne fiye da sauran ‘yan’uwansa,
Bari ya zama abin ƙauna ga ‘yan’uwansa,
Ya kuma tsoma ƙafarsa cikin mai.
25 Kurfanka na baƙin ƙarfe ne da tagulla,
Ƙarfinka ba zai rabu da kai ba muddin ranka.”
26 “Babu wani kamar Allahn Yeshurun,
Wanda yakan sauko daga Sama don ya cece ka,
Wanda ya sauko daga bisa da ɗaukakarsa.
27 Allah Madawwami, shi ne wurin zamanka,
Madawwaman damatsansa suna tallafarka,
Yana kore maka maƙiyanka,
Ya ce, ‘Ka hallaka su!’
28 Da haka Isra’ila yana zaune lafiya,
Zuriyar Yakubu tana zaune ita kaɗai
A ƙasa mai hatsi da ruwan inabi,
Wurin da raɓa take zubowa daga sama.
29 Mai farin ciki ne kai, ya Isra’ila!
Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta?
Ubangiji ne garkuwarku,
Shi ne kuma takobinku mai daraja.
Magabtanku za su yi muku fādanci,
Amma ku za ku tattake masujadansu.”