Rut a Gonar Bo’aza
1 Na’omi tana da wani dangin mijinta, Elimelek, sunansa Bo’aza, shi kuwa attajiri ne.
2 Sai Rut, mutuniyar Mowab, ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi, in yi kalan hatsi a gonar wanda ya yarda in yi.”
Na’omi ta ce mata, “Ki tafi, ‘yata.”
3 Rut ta tafi wata gona, tana bin bayan masu girbi, tana kala. Ta yi sa’a kuwa ta fāɗa a gonar Bo’aza, dangin Elimelek.
4 Sai ga Bo’aza ya zo daga Baitalami, ya ce wa masu girbi, “Salamu alaikun.”
Suka amsa, “Alaika salamu.”
5 Sa’an nan Bo’aza ya tambayi baransa da yake shugaban masu girbin, ya ce, “’Yar wace ce wannan?”
6 Baran ya ce, “Ita ‘yar Mowab ce wadda ta zo tare da Na’omi daga ƙasar Mowab.
7 Ita ce ta ce mana, ‘In kun yarda, ku bar ni in bi bayan masu girbin, ina kala.’ Haka ta yi ta kala tun da sassafe har yanzu ba hutu, sai dai ‘yar shaƙatawar da ta yi kaɗan.”
8 Sa’an nan sai Bo’aza ya ce wa Rut, “Kin ji, ‘yata, kada ki bar wannan gona ki tafi wata gona domin kala, amma ki riƙa bin ‘yan matan gidana.
9 Ki kula da gonar da suke girbi, ki bi su. Ga shi, na riga na umarci barorina kada su dame ki. Sa’ad da kika ji ƙishirwa, sai ki tafi ki sha ruwa a tuluna, wanda barorin suka ɗebo.”
10 Sai Rut ta rusuna har ƙasa, ta ce masa, “Me ya sa na sami tagomashi a gare ka, har da za ka kula da ni, ni da nake baƙuwa?”
11 Amma Bo’aza ya ce mata, “An faɗa mini dukan abin da kika yi wa surukarki tun lokacin da mijinki ya rasu, da yadda kika bar iyayenki da ƙasarku, kika zo wurin mutanen da ba ki taɓa saninsu ba a dā.
12 Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda kika zo neman mafaka gare shi, ya sāka miki da cikakken lada saboda abin da kika yi.”
13 Rut ta ce, “Shugaba, kā yi mini alheri ƙwarai, gama kā ta’azantar da ni, kā yi wa baiwarka maganar alheri, ko da yake ni ba ɗaya daga cikin barorinka ba ce.”
14 Da lokacin cin abinci ya yi, sai Bo’aza ya kira Rut, ya ce, “Zo nan ki ci abinci, ki riƙa tsoma lomarki a ruwan inabin da aka surka.” Sai ta zo, ta zauna kusa da masu girbin. Shi kuwa ya ba ta tumun hatsi. Ta ci, ta ƙoshi har ta bar saura.
15 Sa’ad da ta tashi, za ta yi kala, sai Bo’aza ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku bar ta, ta yi kala a tsakanin tarin dammunan, kada ku hana ta.
16 Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.”
17 Ta yi ta kala a gonar har yamma. Ta sussuka abin da ta kalata, ta sami tsaba wajen garwa biyu.
18 Ta ɗauka, ta koma gari, ta nuna wa surukarta abin da ta kalato. Ta kuma kawo mata sauran abincin da ta ci ta ƙoshi har ta rage.
19 Surukarta kuma ta ce mata, “A ina kika yi kala yau? A gonar wa kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga wannan mutum wanda ya kula da ke.”
Sai ta faɗa mata sunan mutumin da ta yi kala a gonarsa, ta ce, “Sunan mutumin da na yi kala a gonarsa yau, Bo’aza.”
20 Na’omi ta ce wa Rut, “Ubangiji wanda bai daina nuna alheri ga masu rai da marigayan ba, ya sa masa albarka.” Ta ƙara da cewa, “Ai, mutumin, shi danginmu ne na kusa.”
21 Rut kuma, mutuniyar Mowab, ta ce, “Banda wannan ma, ya ce mini, ‘Ki riƙa bin barorina, har lokacin da suka gama mini girbin.’ ”
22 Sa’an nan Na’omi ta ce wa Rut, “Madalla, ‘yata, ki riƙa bin ‘yan matan gidansa, kada ki tafi wata gona dabam.”
23 Sai ta riƙa bin ‘yan matan gidan Bo’aza. Ta yi ta kala har aka gama girbin sha’ir da na alkama, tana zaune tare da surukarta, wato Na’omi.