ZAB 35

Addu’ar Kuɓuta daga Maƙiya

1 Ka yi hamayya da masu hamayya da ni, ya Ubangiji,

Ka yi faɗa da masu faɗa da ni!

2 Ɗauki garkuwa da makamanka, ka zo ka taimake ni.

3 Ka daga mashin yaƙinka sama, da gatarinka,

Ka yi gaba da masu fafarata.

Ka faɗa mini kai ne Mai Cetona!

4 Ka sa a kori waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni, a kunyatar da su!

Ka sa waɗanda suke mini maƙarƙashiya su juya da baya, su ruɗe!

5 Ka sa su zama kamar tattakar da iska take kwashewa,

Kamar waɗanda mala’ikan Ubangiji yake korarsu!

6 Ka sa hanyarsu ta duhunta, ta yi santsi,

A sa’ad da mala’ikan Ubangiji yake fyaɗe su ƙasa!

7 Suka kafa mini tarko ba dalili,

Sun kuma haƙa rami mai zurfi don in faɗa ciki.

8 Amma kafin su farga, hallaka za ta kama su.

Tarkunan da suka kafa za su kama su,

Su kuma fāɗa cikin ramin da suka haƙa!

9 Sa’an nan zan yi murna saboda Ubangiji,

Zan yi murna, gama ya cece ni.

10 Da zuciya ɗaya zan ce wa Ubangiji,

“Ba wani kamarka!

Kakan kāre marasa ƙarfi daga masu ƙarfi,

Talaka da matalauci kuma daga azzalumai!”

11 Mugaye suna ba da muguwar shaida a kaina,

Suna kai ƙarata a kan laifofin da ban san kome a kansa ba.

12 Sun sāka mini alheri da mugunta,

Cike nake da nadama.

13 Amma sa’ad da suke ciwo, nakan sa tufafin makoki,

Na ƙi cin abinci,

Na yi addu’a da kaina a sunkuye,

14 Kamar yadda zan yi wa aboki ko ɗan’uwa addu’a.

Ina tafe a takure saboda makoki,

Kamar wanda yake makoki domin mahaifiyarsa.

15 Sa’ad da nake shan wahala,

Murna suke yi duka,

Sun kewaye ni, suna ta yi mini dariya,

Baƙi sun duke ni, suna ta buguna.

16 Suka wahalshe ni, suka yi mini dariya,

Suna hararata da ƙiyayya.

17 Sai yaushe, za ka duba, ya Ubangiji?

Ka kuɓutar da ni daga farmakinsu,

Ka ceci raina daga waɗannan zakoki!

18 Sa’an nan zan yi maka godiya a gaban babban taron jama’a.

Zan yabe ka a gaban babban taro.

19 Kada ka bar maƙiyana, maƙaryatan nan, su ga fāɗuwata!

Kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili,

Su ƙyaface ni, su yi murna saboda baƙin cikina!

20 Ba su yin maganar zumunci,

A maimakon haka sukan ƙaga ƙarairayi a kan masu ƙaunar limana.

21 Sukan zarge ni da kakkausan harshe,

Su ce, “Mun ga abin da ka yi!”

22 Amma kai, ya Ubangiji ka ga wannan.

Saboda haka kada ka ƙyale su, ya Ubangiji,

Kada ka yi nisa!

23 Ka tashi, ya Ubangiji, ka kāre ni.

Ya Allah ka tashi, ka bi mini hakkina.

24 Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, ka shaida rashin laifina,

Kada ka bar maƙiyana su ƙyaface ni, ya Allahna!

25 Kada ka bar su su ce wa kansu,

“Madalla! Da ma abin da muke so ke nan!”

Kada ka bar su su ce,

“Mun rinjaye shi!”

26 Ka sa waɗanda suka ƙyaface ni a wahalata,

A rinjaye su, su ruɗe.

Ka sa waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni,

Su sha kunya da wulakanci!

27 Ka sa waɗanda suke murna da kuɓutata

Su yi ta sowa ta murna, suna cewa,

“Ubangiji mai girma ne!

Yana murna da cin nasarar bawansa!”

28 Sa’an nan zan yi shelar adalcinka,

Dukan yini kuwa zan yi ta yabonka.