ZAB 43

Addu’ar Wanda Aka Kai Baƙuwar Ƙasa ala Tilas

1 Ya Allah, ka kuɓutar da ni,

Ka kiyaye al’amarina daga marasa tsoronka,

Ka cece ni daga ƙaryar mugaye!

2 Ya Allah, kai ne kake kāre ni,

Me ya sa ka yashe ni?

Me ya sa nake ta shan wahala saboda muguntar maƙiyana?

3 Ka aiko da haskenka, da gaskiyarka,

Bari su bishe ni,

Su kawo ni Sihiyona, tsattsarkan tudunka,

Su kawo ni Haikalinka, inda zatinka yake!

4 Sa’an nan zan tafi wurin bagadenka, ya Allah,

Zuwa gare ka, kai wanda kake sa ni in yi murna da farin ciki,

In raira waƙar yabo a gare ka da garayata,

Ya Allah, Allahna!

5 Me ya sa nake baƙin ciki?

Me ya sa nake damuwa?

Zan dogara ga Allah,

Zan ƙara yabonsa,

Mai Cetona, Allahna.