Iliya a Dutsen Sinai
1 Ahab kuwa ya faɗa wa Yezebel dukan abin da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe annabawan Ba’al duka.
2 Sai Yezebel ta aike a wurin Iliya ta ce, “Idan gobe war haka, ban kashe ka ba kamar yadda ka karkashe annabawan nan, to, alloli su hukunta ni.”
3 Sai Iliya ya ji tsoro, ya tashi, ya tsere zuwa Biyer-sheba ta Yahuza.
Ya bar baransa a can.
4 Iliya ya yi tafiyarsa yini guda cikin jeji, ya tafi ya zauna a gindin wani itace ya yi roƙo domin ya mutu, yana cewa, “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi raina, gama ban fi kakannina ba.”
5 Iliya kuwa ya kwanta, ya yi ta barci a gindin itacen. Farat sai mala’ika ya taba shi, ya ce masa, “Tashi, ka ci abinci.”
6 Da ya duba, sai ga waina da zafinta a bisa duwatsu, da butar ruwa a waje ɗaya. Ya ci, ya sha, ya koma kwantawa.
7 Mala’ikan Ubangiji kuma ya sake zuwa sau na biyu, ya taɓa shi, ya ce, “Tashi, ka ci abinci, in ba haka ba kuwa tafiya za ta gagare ka.”
8 Sai Iliya ya tashi ya ci abinci ya sha ruwa ya sami ƙarfi, sa’an nan ya kama tafiya kwana arba’in dare da rana har zuwa Horeb, wato dutsen Allah.
9 A can ya shiga wani kogo domin ya kwana.
Ba labari sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”
10 Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama’ar Isra’ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”
11 Ubangiji ya ce masa, “Tafi, ka tsaya a kan dutse, a gabana.” Sai ga Ubangiji yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsage dutsen, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasar.
12 Bayan girgizar kuma, sai wuta, amma Ubangiji ba ya cikin wutar. Bayan wutar sai ƙaramar murya.
13 Sa’ad da Iliya ya ji muryar, sai ya rufe fuskarsa da alkyabbarsa, ya fita, ya tsaya a bakin kogon. Sai ya ji murya ta ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”
14 Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama’ar Isra’ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”
15 Sai Ubangiji ya ce masa, “Ka juya zuwa jeji kusa da Dimashƙu, idan ka isa can, sai ka zuba wa Hazayel mai, ka keɓe shi, ya sama Sarkin Suriya,
16 da Yehu ɗan Nimshi, ka keɓe shi, ya zama Sarkin Isra’ila. Ka kuma zuba wa Elisha, ɗan Shafat na Abel-mehola, mai, ka keɓe shi, ya zama annabi a maimakonka.
17 Duk wanda zai tsere wa Hazayel, Yehu zai kashe shi. Wanda kuma ya tsere wa Yehu. Elisha zai kashe shi.
18 Duk da haka zan rage mutum dubu bakwai(7,000) na Isra’ila waɗanda ba su rusuna wa Ba’al da gwiwoyinsu ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.”
An Kira Elisha
19 Iliya fa ya tashi daga wurin nan, ya tarar da Elisha ɗan Shafat, yana tare da shanu, garma goma sha biyu. Yana tare da na sha biyun, sai Iliya ya bi ta kusa da shi, ya jefa masa alkyabbarsa.
20 Sai ya bar shanun noma, ya sheƙa gun Iliya, ya ce, “Bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa’an nan in zo in bi ka.”
Sa’an nan Iliya ya ce masa, “Koma, me na yi maka?”
21 Elisha kuwa ya koma, ya kama shanun noman, ya yanka, ya dafa su da karkiyoyinsu. Ya raba wa mutane, suka ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya zama mai taimakonsa.