Dawuda Ya Zama Sarkin Isra’ilawa da Yahudawa
1 Dukan kabilan Isra’ila kuwa suka zo wurin Dawuda a Hebron, suka ce, “Ga shi, mu ‘yan’uwanka ne.
2 A dā sa’ad da Saul yake sarautarmu, kai kake bi da Isra’ilawa zuwa yaƙi, kai kake komo da su. Ubangiji kuma ya ce maka, ‘Kai za ka lura da jama’ata Isra’ila, za ka zama sarkinsu.’ ”
3 Sai dukan dattawan Isra’ila suka tafi wurin sarki Dawuda a Hebron, shi kuwa ya yi alkawari da su a gaban Ubangiji. Su kuwa suka naɗa shi Sarkin Isra’ila duka.
4 Dawuda ya ci sarauta yana da shekara talatin. Ya yi shekara arba’in yana sarauta.
5 Ya yi sarautar jama’ar Yahuza shekara bakwai da wata shida a Hebron. Ya kuma yi sarautar jama’ar Isra’ila duk da Yahuza shekara talatin da uku a Urushalima.
Dawuda Ya Ci Sihiyona
6 Sarki Dawuda da mutanensa suka tafi Urushalima su yaƙi Yebusiyawa mazaunan ƙasar. Su kuwa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka iya zuwa nan ba, makafi kawai da guragu za su kore ka.” A zatonsu Dawuda ba zai iya zuwa can ba.
7 Duk da haka Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, wato birnin Dawuda.
8 A ran nan Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kashe Yebusiyawa, to, sai kuma ya haura zuwa wuriyar ruwa ya fāɗa wa guragu da makafi waɗanda ran Dawuda yake ƙi.” Don haka a kan ce, “Makafi da guragu ba za su shiga Haikali ba.”
9 Dawuda ya zauna a kagara. Ya ba ta suna Birnin Dawuda. Ya kuma yi gine-gine kewaye da wurin. Ya fara daga Millo zuwa ciki.
10 Dawuda kuwa ya ƙasaita, gama Ubangiji Allah Mai Runduna yana tare da shi.
Hiram Sarkin Taya Ya Yarda da Dawuda
11 Hiram Sarkin Taya ya aiki jakadu zuwa wurin Dawuda. Ya kuma aika masa da katakan itacen al’ul, da kafintoci, da masu yin gini da duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda gida.
12 Dawuda kuwa ya gane lalle Ubangiji ya tabbatar da shi sarki bisa jama’ar Isra’ila, ya kuma ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa, Isra’ila.
‘Ya’yan da aka Haifa wa Dawuda a Urushalima
13 Bayan zuwan Dawuda Urushalima daga Hebron, sai ya ɗauki waɗansu ƙwaraƙwarai, ya kuma auri waɗansu mata. Aka kuma haifa masa waɗansu ‘ya’ya mata da maza.
14 Sunayen ‘ya’yan da aka haifa masa a Urushalima ke nan, Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu,
15 da Ibhar, da Elishuwa, da Nefeg, da Yafiya,
16 da Elishama, da Eliyada, da Elifelet.
Dawuda Ya Ci Nasara a kan Filistiyawa
17 Sa’ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra’ila, sai dukansu suka haura zuwa neman ran Dawuda. Da Dawuda ya ji Filistiyawa suna nemansa, sai ya gangara zuwa kagara.
18 Filistiyawa kuwa suka zo suka bazu a kwarin Refayawa.
19 Dawuda kuwa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?”
Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka haura, gama hakika, zan ba da Filistiyawa a hannunka.”
20 Sai Dawuda ya zo Ba’al-ferazim, ya ci Filistiyawa a wurin. Sa’an nan ya ce, “Ubangiji ya huda abokan gabana a idona kamar rigyawa.” Saboda haka aka sa wa wurin suna, “Ubangiji Mai Hudawa.”
21 Filistiyawa suka gudu, suka bar gumakansu a nan, Dawuda da mutanensa suka kwashe su.
22 Filistiyawa suka sāke haurawa, suka bazu a kwarin Refayawa.
23 Dawuda ya kuma roƙi Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Kada ka haura zuwa wurinsu gaba da gaba, amma ka bi ta bayansu, ka ɓullo musu daura da itatuwan doka.
24 Sa’ad da ka ji motsin rausayawar rassan itatuwan doka, sai ka yi maza, ka faɗa musu, gama Ubangiji zai wuce gaba domin ya bugi rundunar Filistiyawa.”
25 Sai Dawuda ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya yi ta bugun Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.