An Naɗa Dawuda Sarkin Yahuza
1 Bayan wannan sai Dawuda ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ko in haura in mallaki ɗaya daga cikin garuruwan Yahuza?”
Ubangiji ya ce masa, “Ka haura.”
Dawuda kuma ya ce, “Zuwa wane gari zan haura?”
Sai Ubangiji ya ce masa, “Zuwa Hebron.”
2 Dawuda kuwa ya haura zuwa can tare da matansa biyu, wato Ahinowam Bayezreyeliya, da Abigail matar marigayi Nabal Bakarmele.
3 Ya kuma tafi tare da mutanen da suke tare da shi, kowa da iyalinsa. Suka zauna a garuruwan Hebron.
4 Mutanen Yahuza kuwa suka zo, suka naɗa Dawuda da man naɗawa domin ya zama Sarkin Yahuza.
Da Dawuda ya ji labari mutanen Yabesh-gileyad, sun binne Saul,
5 sai ya aiki manzanni da saƙo wurin mutanen Yabesh-gileyad ya ce, “Ubangiji ya sa muku albarka da yake kun yi wa Saul, ubangijinku, wannan alheri, har kuka binne shi.
6 Ubangiji ya nuna muku ƙaunarsa da amincinsa. Ni kuwa zan yi muku alheri saboda abin da kuka yi.
7 Yanzu sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Saul shugabanku ya rasu, mutanen Yahuza kuwa sun naɗa ni sarkinsu.”
Dawuda ya Yaƙi Gidan Saul
8 Abner kuwa ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul, ya tsere da Ish-boshet, ɗan Saul, zuwa Mahanayim.
9 Ya naɗa shi Sarkin Gileyad, da Ashiru, da Yezreyel, da Ifraimu, da ƙasar Biliyaminu, da dukan Isra’ila.
10 Ish-boshet, ɗan Saul, yana da shekara arba’in sa’ad da ya ci sarautar Isra’ila, ya yi shekara biyu yana sarauta. Amma mutanen Yahuza suka bi Dawuda.
11 Dawuda ya yi shekara bakwai da rabi yana sarautar Yahuza a Hebron.
12 Abner, ɗan Ner, tare da fādawan Ish-boshet, ɗan Saul, suka tashi daga Mahanayim zuwa Gibeyon.
13 Sai kuma Yowab, ɗan Zeruya, tare da fādawan Dawuda suka fita suka tafi tarye su a tafkin Gibeyon. Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe na tafkin.
14 Sai Abner ya ce wa Yowab, “Bari samarin su tashi su yi kokawa a gabanmu.”
Yowab kuwa ya ce, “To, sai su tashi.”
15 Sai suka tashi, suka haye. Mutum goma sha biyu a madadin mutanen Biliyaminu da Ish-boshet, ɗan Saul, mutum goma sha biyu kuma a madadin mutanen Dawuda.
16 Kowa ya kama abokin kokawarsa a kā, suka soki juna a kwiɓi da takuba. Suka faɗi tare. Aka sa wa wurin suna Helkat-hazzurim, wato filin takuba, wurin yana nan a Gibeyon.
17 Yaƙin kuwa ya yi zafi a ranar. Mutanen Dawuda suka ci Abner da mutanen Isra’ila.
18 ‘Ya’yan Zeruya, maza, su uku suna nan, wato Yowab, da Abishai, da Asahel. Asahel maguji ne kamar barewa.
19 Sai ya tasar wa bin Abner haiƙan, bai kauce ba.
20 Da Abner ya waiga, sai ya ce, “Kai ne Asahel?”
Ya amsa, “Ni ne.”
21 Abner ya ce masa, “Ka daina haye mini, ka runtumi ɗaya daga cikin samarin, ka kama shi, ka karɓe masa makaminsa.” Amma Asahel bai daina binsa ba.
22 Abner kuma ya sāke ce masa, “Ka daina bina, kada ka sa in kashe ka fa! Idan na kashe ka kuwa, yaya zan yi ido biyu da dan’uwanka, Yowab?”
23 Amma Asahel bai daina binsa ba, Abner dai ya nashe shi da gindin māshi a ciki, sai mashin ya fita ta bayansa. Ya fāɗi ya mutu nan take. Duk wanda ya zo inda Asahel ya fāɗi ya mutu, sai ya tsaya cik.
24 Amma Yowab da Abishai suka bi Abner, har faɗuwar rana, suka isa tudun Amma, wanda yake gaban Gaiya, a hanya zuwa jejin Gibeyon.
25 Mutanen Biliyaminu kuma suka haɗa kansu, suka goyi bayan Abner, suka zama ƙungiya guda, suka tsaya kan tudu.
26 Abner kuwa ya kira Yowab, ya ce, “Har abada ne takobi zai hallakar? Ba ka sani ba ƙarshen zai yi ɗaci? Sai yaushe za ka umarci mutanenka su daina runtumar ‘yan’uwansu?”
27 Yowab ya ce, “Na rantse da Ubangiji, hakika da ba domin ka yi magana ba, da mutanena ba za su daina runtumarka ba har gobe da safe.”
28 Sa’an nan Yowab ya busa ƙaho, dukan mutanensa kuwa suka tsaya, ba su ƙara runtumar mutanen Isra’ila ba, ba wanda kuma ya yaƙi wani.
29 Abner da mutanensa suka bi dare farai, suka ratsa Araba, suka haye Urdun. Suka yi ta tafiya dukan safiyan nan, suka shige Bitron, har suka kai Mahanayim.
30 Da Yowab ya komo daga runtumar Abner, ya tattara mutanensa duka, sai ya ga an rasa mutum goma sha tara daga cikin mutanen Dawuda, banda Asahel.
31 Amma barorin Dawuda suka kashe mutanen Biliyaminu mutum ɗari uku da sittin daga cikin waɗanda suke tare da Abner.
32 Suka ɗauki Asahel, suka tafi suka binne shi a kabarin mahaifinsa a Baitalami. Yowab kuwa da mutanensa suka bi dare farai, gari ya waye musu a Hebron.