An Kashe Firistoci
1 Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da ‘yan’uwansa da mutanen gidan ubansa, suka ji labari, suka tafi can wurinsa.
2 Kowane mutum kuma da yake matse, da wanda ake bi bashi, da wanda ransa ba ya kwance, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Sun kai wajen mutum ɗari huɗu.
3 Daga can Dawuda ya wuce zuwa Mizfa ta Mowab. Ya ce wa Sarkin Mowab, “Ina roƙonka, ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Ubangiji zai yi da ni.”
4 Sai ya bar iyayensa a wurin Sarkin Mowab, suka zauna a wurinsa duk lokacin da Dawuda yake ta ɓuya a kogwannin duwatsu.
5 Sa’an nan Gad, annabi, ya ce wa Dawuda, “Kada ka zauna a nan, maza ka tafi ƙasar Yahuza.” Sai ya tashi, ya tafi kurmin Haret.
Saul Ya Kashe Firistoci na Nob
6 Sai Saul ya ji labari an gane inda Dawuda da mutanensa suke. Saul kuwa yana zaune a Gibeya a gindin itacen tsamiya a kan tudu, yana riƙe da mashinsa. Dukan fādawansa suna tsaye kewaye da shi.
7-8 Sai ya ce wa fādawan da suke tsaye kewaye da shi, “Ku ji, ya ku mutanen Biliyaminu, ɗan Yesse zai ba kowannenku gonaki, da gonakin inabi ne? Zai maishe ku shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, har da dukanku kuka yi mini maƙarƙashiya? Ba wanda ya sanar da ni sa’ad da ɗana ya haɗa kai da ɗan Yesse? Ba wanda ya damu saboda da ni, balle a faɗa mini yadda ɗana ya kuta barana ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake a yau?”
9 Sa’an nan Doyeg, mutumin Edom, da yake tsaye tare da fādawan Saul, ya ce, “Na ga ɗan Yesse yana zuwa Nob wurin Ahimelek, ɗan Ahitub.
10 Shi kuwa ya roƙi Ubangiji domin Dawuda, ya kuma ba shi guzuri, har ya ba shi takobin Goliyat, Bafilisten.”
11 Sarki kuwa ya aika a kira Ahimelek, firist, ɗan Ahitub, da dukan mutanen gidan mahaifinsa, da firistocin da suke a Nob. Dukansu kuwa suka zo wurin sarki.
12 Saul kuwa ya ce, “Ka ji, ya ɗan Ahitub.”
Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka ya daɗe, ina ji.”
13 Saul ya ce masa, “Me ya sa ka yi mini maƙarƙashiya, kai da ɗan Yesse, da yake ka ba shi abinci, da takobi, ka kuma roƙar masa Allah, ga shi yanzu, ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake yi a yau?”
14 Ahimelek kuwa ya ce wa sarki, “Daga cikin barorinka duka wa yake da aminci kamar Dawuda? Wane ne surukin sarki? Wane ne shugaban jarumawanka, wanda ake girmamawa a gidanka?
15 Yau ne na fara roƙar masa Allah? A’a, kada dai sarki ya zargi baransa ko gidan mahaifina duka, gama baranka bai san kome a kan wannan ba.”
16 Sai sarki ya ce, “Hakika, mutuwa za ku yi, Ahimelek, kai da dukan gidan mahaifinka.”
17 Ya ce wa matsara da suke tsaye kewaye da shi, “Ku fāɗa wa firistocin Ubangiji, ku kashe su gama suna goyon bayan Dawuda, ga shi, sun sani ya gudu, amma ba su faɗa mini ba.” Amma barorin sarki ba su yarda su fāɗa wa firistocin Ubangiji ba.
18 Sa’an nan sarki ya ce wa Doyeg, “Kai ka fāɗa wa firistocin.” Sai Doyeg, mutumin Edom, ya faɗa wa firistocin, ya kashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke saye da falmaran na lilin a wannan rana.
19 Ya kuma hallaka Nob birnin firistoci, ya kashe dukan mata, da maza, da yara, da jarirai, da shanu, da jakai, da tumaki.
20 Amma Abiyata ɗaya daga cikin ‘ya’yan Ahimelek, ɗan Ahitub, ya tsere, ya gudu zuwa wurin Dawuda.
21 Sai ya faɗa wa Dawuda Saul ya kashe firistocin Ubangiji.
22 Dawuda kuwa ya ce wa Abiyata, “A ran nan Doyeg, mutumin Edom, yana wurin, na sani lalle zai faɗa wa Saul. Ni na zama sanadin mutuwar dukan mutanen gidan mahaifinka.
23 Sai ka zauna tare da ni, kada ka ji tsoro, gama wanda yake neman raina yana neman naka. Ka yi zamanka lafiya tare da ni.”