Saul Ya Tsananta wa Dawuda
1 Sai Saul ya yi magana da Jonatan, ɗansa, da dukan fādawansa, cewa yana shiri ya kashe Dawuda. Amma Jonatan ɗan Saul yana jin daɗin Dawuda ƙwarai.
2 Jonatan ya faɗa wa Dawuda ya ce, “Saul, mahaifina, yana so ya kashe ka, domin haka sai ka lura da kanka da safe, ka ɓuya a wani lungu.
3 Ni kuwa zan tafi in tsaya kusa da mahaifina a saura inda ka ɓuya, zan yi masa magana a kanka, abin da ya faru, zan sanar da kai.”
4 Jonatan kuwa ya yabi Dawuda a gaban Saul, ya ce masa, “Kada sarki ya yi wa baransa, Dawuda, laifi, gama shi bai yi maka laifi ba, ayyukansa kuma a gare ka masu kyau ne.
5 Ya yi kasai da ransa har ya kashe Bafilisten, Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa babbar nasara. Kai ma ka gani, ka kuwa yi murna. Me ya sa za ka ɗauki alhakin Dawuda, wanda bai yi maka laifin kome ba?”
6 Saul kuwa ya saurari maganar Jonatan, ya rantse masa ya ce, “Hakika, ba za a kashe shi ba.”
7 Jonatan kuwa ya kira Dawuda ya faɗa masa dukan abin da Saul ya faɗa. Ya kuma kai Dawuda gaban Saul, ya zauna tare da shi kamar dā.
8 Aka kuma yi yaƙi da Filistiyawa, Dawuda kuwa ya tafi ya yi yaƙi da su, ya kashe su da yawa, sai suka gudu a gabansa.
9 Ubangiji kuma ya sa mugun ruhu ya sauko kan Saul sa’ad da yake zaune a gidansa, da mashi a hannunsa. Dawuda kuma yana ta kaɗa masa garaya.
10 Saul kuwa ya yi shiri ya nashi Dawuda, ya kafe shi ga bango. Da ya nashe shi, sai ya goce, mashin ya sami bangon. Dawuda kuwa ya gudu, ya tsere.
11 A daren nan Saul ya aiki manzanni su je gidan Dawuda don su yi fakonsa, su kashe shi da safe. Amma Mikal, matar Dawuda, ta faɗa masa cewa, “Idan ba ka gudu da daren nan ba, gobe za a kashe ka.”
12 Sai ta zurarar da Dawuda ta taga, ya gudu, ya tsere.
13 Mikal kuwa ta ɗauki kan gida ta kwantar da shi a gado, ta kuma sa masa matashin kai na gashin awaki, sa’an nan ta lulluɓe shi da mayafi.
14 Sa’ad da manzannin Saul suka zo don su kama Dawuda, sai ta ce musu, “Ba shi da lafiya.”
15 Saul kuma ya sāke aiken manzannin su tafi su ga Dawuda, ya ce musu, “Ku kawo shi nan wurina a kan gadonsa don in kashe shi.”
16 Da manzannin suka tafi, sai suka tarar da kan gida a gadon, da matashin kai na gashin awaki wajen kansa.
17 Saul kuwa ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya tsere?”
Ta ce wa Saul, “Ya ce mini, idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni.”
18 Dawuda ya gudu, ya tsere zuwa wurin Sama’ila a Rama, ya faɗa masa dukan abin da Saul ya yi masa. Shi da Sama’ila suka tafi suka zauna a Nayot.
19 Aka faɗa wa Saul cewa, “Dawuda yana a Nayot ta Rama.”
20 Sai ya aika da manzanni su tafi su kama Dawuda. Da suka kai, suka iske ƙungiyar annabawa suna annabci, Sama’ila kuwa yana tsaye a gabansu. Ruhun Allah ya sauko a kan manzannin Saul, su kuma suka yi annabci.
21 Aka faɗa wa Saul, sai ya sāke aiken waɗansu, su kuma suka shiga yin annabci. Ya kuma sāke aiken manzanni aji na uku, su kuma suka shiga yin annabci.
22 Saul kuma ya tafi Rama da kansa. Da ya kai babbar rijiyar da suke a Seku, sai ya tambayi inda Sama’ila da Dawuda suke. Wani ya ce masa, “Suna Nayot ta Rama.”
23 Sai ya tashi daga can zuwa Nayot ta Rama. Ruhun Allah kuwa ya sauko a kansa, sai shi kuma ya shiga yin annabci har ya kai Nayot ta Rama,
24 ya kuma tuɓe tufafinsa, ya yi ta annabci a gaban Sama’ila. Ya kwanta huntu dukan yini da dukan dare. Don haka aka riƙa yin karin magana da cewa, “Har Saul ma yana cikin annabawa?”