Haihuwar Samson
1 Isra’ilawa kuma suka sāke yi wa Ubangiji zunubi, sai Ubangiji ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba’in.
2 Akwai wani mutumin Zora daga kabilar Dan, sunansa Manowa, matarsa bakarariya ce, ba ta haihuwa.
3 Ga mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta, ya ce mata, “Ga shi, ke bakarariya ce, ba ki haihuwa, amma yanzu za ki yi ciki, za ki kuwa haifi ɗa.
4 Yanzu sai ki lura, kada ki sha ruwan inabi, ko abin sha mai gāfi, kada kuma ki ci haramtaccen abu,
5 gama za ki yi juna biyu, ki haifi ɗa. Ba za ki taɓa aske kansa ba Zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki. Shi ne zai ceci Isra’ilawa daga hannun Filistiyawa.”
6 Macen kuwa ta tafi ta faɗa wa mijinta cewa, “Mutumin Allah ya zo wurina, fuskarsa tana da bantsoro kamar fuskar mala’ikan Ubangiji. Ni kuwa ban tambaye shi inda yake ba, shi kuma bai faɗa mini sunansa ba.
7 Amma ya ce mini, zan yi juna biyu, in haifi ɗa, don haka kada in sha ruwan inabi, ko abin sa maye, kada kuma in ci haramtaccen abu, gama yaron zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki har zuwa ranar da zai rasu.”
8 Sa’an nan Manowa ya yi roƙo ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangijina, ina roƙonka ka bar mutumin Allah wanda ka aiko, ya sāke zuwa wurinmu, ya faɗa mana abin da za mu yi wa yaron da za a haifa.”
9 Allah kuwa ya ji roƙon Manowa, ya sāke aiko da mala’ikansa wurin matar, sa’ad da take a saura, mijinta kuwa ba ya tare da ita.
10 Don haka sai ta sheƙa a guje zuwa wurin mijinta, ta faɗa masa, “Ga mutumin da ya zo wurina ran nan, ya sāke zuwa.”
11 Manowa fa ya tashi ya tafi tare da ita. Da ya zo wurin mutumin, sai ya tambaye shi, “Kai ne mutumin da ya yi magana da macen nan?”
Sai ya amsa ya ce, “Ni ne.”
12 Manowa kuma ya ce, “Lokacin da maganarka ta cika, wane irin yaro ne zai zama, me kuma za mu yi?”
13 Mala’ikan Ubangiji ya amsa, ya ce wa Manowa, “Sai matarka ta kiyaye dukan abin da na faɗa mata.
14 Kada ta ci kowane irin abu da aka yi da inabi, kada kuma ta sha ruwan inabi ko abin sa maye. Kada ta ci haramtaccen abu, amma ta kiyaye dukan abin da na umarce ta.”
15-16 Manowa dai bai san mala’ikan Ubangiji ne ba, sai ya ce wa mala’ikan, “Ina roƙonka ka jira, mu yanka maka ɗan akuya.”
Amma mala’ikan ya ce masa, “Ko na jira ba zan ci abincinku ba, amma idan kana so ka yanka, sai ka shirya hadayar ƙonawa, ka miƙa ta ga Ubangiji.”
17 Manowa ya ce, “Ka faɗa mana sunanka domin lokacin da maganarka ta cika mu girmama ka.”
18 Mala’ikan Ubangiji ya ce masa, “Don me kake tambayar sunana? Sunana asiri ne.”
19 Manowa kuwa ya yanka ɗan akuya, ya kuma kawo hadayar gāri, ya miƙa a kan dutse ga Ubangiji, mala’ika kuma ya yi al’ajabi. Manowa da matarsa suka yi kallo.
20 Sa’ad da harshen wutar ya hau zuwa samaniya daga bagaden, sai mala’ikan Ubangiji ya hau zuwa sama ta cikin harshen wutar bagaden. Manowa da matarsa sun gani, suka fāɗi a fuskokinsu a ƙasa.
21 Mala’ikan Ubangiji bai sāke bayyana ga Manowa da matarsa ba. Manowa kuma ya gane mala’ikan Ubangiji ne.
22 Manowa ya ce wa matarsa, “Ba shakka za mu mutu gama mun ga Ubangiji!”
23 Amma matarsa ta ce masa, “Da Ubangiji yana so ya kashe mu, ai, da bai karɓi hadayar ƙonawa da hadayar gārinmu ba, da kuma bai nuna mana, ko ya faɗa mana waɗannan abubuwa ba.”
24 Matar kuwa ta haifi ɗa, aka raɗa masa suna Samson. Yaron ya yi girma, Ubangiji ya sa masa albarka.
25 Ruhun Ubangiji ya fara iza shi, sa’ad da yake a zangon Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.