Ƙasar da Ta Ragu da Za A Mallaka
1 Yanzu Joshuwa ya tsufa ƙwarai, sai Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi, ƙasar da za ku mallaka ta ragu da yawa.
2 Wannan ita ce ƙasar da ta ragu, dukan ƙasar Filistiyawa, da ta Geshuriyawa,
3 daga Shihor da yake gabas da Masar zuwa iyakar Ekron a wajen arewa. Wannan ƙasa ta Kan’aniyawa ce. Akwai ƙasar sarakuna biyar na Filistiyawa da yake a Gaza, da Ashdod, da Ashkelon, da Gat, da Ekron, da ƙasar Awwiyawa,
4 da dukan ƙasar Kan’aniyawa a wajen kudu, da Meyara ta Sidoniyawa, zuwa Afek, har zuwa iyakar Amoriyawa,
5 da ƙasar Gebaliyawa, da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba’al-gad a gindin Dutsen Harmon zuwa iyakar Hamat,
6 da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama’ar Isra’ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka.
7 Yanzu fa sai ka raba wa kabilai tara da rabi ɗin nan ƙasar ta zama gādonsu.”
Yankin Ƙasar da Aka Ba Manassa da Ra’ubainu da Gad
8 Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, sun karɓi nasu gādo wanda Musa ya ba su a hayin Urdun wajen gabas. Abin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba su ke nan,
9 daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu ta Medeba zuwa Dibon,
10 da dukan biranen Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, har zuwa iyakar Amoriyawa,
11 da Gileyad, da yankin ƙasar Geshuriyawa, da Ma’akatiyawa, da dukan Dutsen Harmon, da dukan Bashan, zuwa Salka,
12 da dukan mulkin Og a Bashan, wanda ya yi sarautar Ashtarot da Edirai (Og Kaɗai ne aka bari daga cikin Refayawa). Waɗannan su ne Musa ya ci da yaƙi, ya kore su.
13 Duk da haka jama’ar Isra’ila ba su kori Geshuriyawa, da Ma’akatiyawa ba, amma suka yi zamansu tare da Isra’ilawa har wa yau.
14 Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa na Ubangiji, Allah na Isra’ila, su ne gādonta, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.
15 Musa ya riga ya ba Ra’ubainawa nasu gādo bisa ga iyalansu.
16 Nasu yankin ƙasar ya miƙa daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon, da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba,
17 da Heshbon, da dukan biranenta da suke kan tudu, wato Dibon, da Bamot-ba’al, da Ba’al-mayon,
18 da Yahaza, da Kedemot, da Mefayat,
19 da Kiriyatayim, da Sibma, da Zeret-shahar da yake bisa tudun da yake cikin kwarin,
20 da Bet-feyor, da gangaren Fisga, da Betyeshimot.
21 Waɗannan duka su ne birane na kan tudu, da dukan masarautar Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya sarauci Heshbon. Musa ya ci shi da yaƙi da shugabannin Madayana, wato Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba, wato sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.
22 Jama’ar Isra’ila kuma suka kashe Bal’amu matsubbaci, ɗan Beyor, da takobi.
23 Urdun kuwa ya zama iyakar yankin ƙasar jama’ar Ra’ubainu. Wannan shi ne gādon Ra’ubainawa bisa ga iyalansu, da biranensu da ƙauyukansu.
24 Musa kuma ya ba Gadawa gādo bisa ga iyalansu.
25 Yankin ƙasarsu shi ne Yazar, da dukan biranen Gileyad da rabin ƙasar Ammonawa zuwa Arower wadda take gabas da Rabba,
26 daga Heshbon zuwa Ramat-mizfe, da Betonim, daga Mahanayim zuwa karkarar Debir,
27 da a kwarin Ber-aram, da Betnimra, da Sukkot, da Zafon, da kuma ragowar mulkin Sihon, Sarkin Heshbon. Kogin Urdun ne iyakar yankin ƙasarsu har zuwa wutsiyar Tekun Kinneret, a gabashin hayin Urdun.
28 Wannan shi ne yankin ƙasar, haɗe da garuruwa, da ƙauyuka, da aka ba mutanen kabilar Gad bisa ga iyalansu.
29 Musa kuma ya ba rabin jama’ar Manassa rabon gādo bisa ga iyalansu.
30 Yankin ƙasarsu ya bi daga Mahanayim, ya haɗa dukan Bashan, da dukan mulkin Og, Sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,
31 da rabin Gileyad, da Ashtarot, da Edirai, wato garuruwan sarki Og a Bashan. Mutanen Makir ne, ɗan Manassa, aka ba su wannan bisa ga iyalansu.
32 Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun daura da Yariko.
33 Amma Musa bai ba Lawiyawa gādon yankin ƙasa ba. Ya faɗa musu Ubangiji Allah na Isra’ila, shi ne rabon gādonsu.