An Ci Ai da Yaƙi
1 Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoro ko ka firgita. Ka ɗauki mayaƙa duka, ka tashi, ka tafi Ai. Ga shi, na riga na ba da Sarkin Ai da mutanensa, da birninsa, da ƙasarsa a hannunka.
2 Za ka yi wa Ai da sarkinta kamar yadda ka yi wa Yariko da sarkinta, sai dai ganima da dabbobinta ne za ku washe domin kanku. Ku yi kwanto a bayan birnin.”
3 Joshuwa kuwa tare da dukan mayaƙa suka yi shirin tashi zuwa Ai. Sai Joshuwa ya zaɓi jarumawa ƙarfafa dubu talatin (30,000), ya aike su da dad dare.
4 Ya umarce su, ya ce, “Ku tafi, ku yi kwanto a bayan birnin, kada ku yi nisa da birni da yawa, amma dukanku ku kasance da shiri sosai.
5 Da ni da dukan mutanen da suke tare da ni za mu je kusa da birnin. Sa’ad da za su fito don su yi karo da mu kamar dā, za mu gudu daga gare su.
6 Za su kuwa fito su bi mu. Mu kuwa za mu janye su nesa da birnin, gama za su ce, ‘Suna gudunmu kamar dā.’ Haka fa, za mu gudu daga gare su.
7 Ku kuwa ku tashi daga kwanto, ku ci birnin, gama Ubangiji Allahnku zai ba da shi a hannunku.
8 A sa’ad da kuka ci birnin, ku sa wa birnin wuta yadda Ubangiji ya ce. Ku lura fa, da abin da na umarce ku.”
9 Sai Joshuwa ya sallame su, suka tafi inda za su yi kwanto. Suka yi fako tsakanin Betel da Ai, yamma da Ai, amma shi ya kwana tare da jama’a.
10 Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe ya tattara mutanen, ya tafi tare da shugabannin Isra’ilawa, suka wuce gaba, suka bi da mutane zuwa Ai.
11 Dukan mayaƙan da suke tare da shi, suka tafi kusa da birnin, suka kafa sansaninsu arewacin Ai. Tsakaninsu da Ai akwai kwari.
12 Ya kuma zaɓi mutum wajen dubu biyar (5,000) ya sa su yi kwanto tsakanin Betel da Ai, yamma da birnin.
13 Mutanensu suka kafa sansaninsu arewa da birnin, sansani na ‘yan kwanto kuwa yana yamma da birnin, amma Joshuwa ya kwana a kwarin.
14 A sa’ad da Sarkin Ai ya ga wannan, shi da mutanensa duka, wato mutanen birnin, suka gaggauta, suka tafi da sassafe zuwa gangaren wajen Araba don su gabza yaƙi da Isra’ilawa, amma bai san akwai ‘yan kwanto a bayan birnin ba.
15 Sai Joshuwa da mutanensa duka suka nuna kamar an rinjaye su, suka yi ta gudu, suka nufi jeji.
16 Saboda haka aka kira dukan mutanen da suke cikin birnin, su fafare su. Da suka fafari Joshuwa, sai aka janye su nesa da birnin.
17 Ba namijin da ya ragu cikin Ai da bai fita ya fafari Isra’ilawa ba, suka bar birnin a buɗe, suka fafari Isra’ilawa.
18 Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka miƙa mashin da yake hannunka wajen Ai, gama zan ba da ita a hannunka.” Sai Joshuwa ya miƙa mashin da yake hannunsa wajen birnin. Nan da nan da ya ɗaga hannunsa
19 ‘yan kwanto suka tashi da sauri daga maɓoyansu, suka shiga birnin, suka ci shi, suka yi sauri, suka cuna wa birnin wuta.
20 Da mutanen Ai suka waiga, sai ga hayaƙin birnin ya murtuke zuwa sama, suka rasa ikon da za su gudu gaba ko baya, gama mutanen da suka gudu zuwa jeji, sun juyo kan masu fafararsu.
21 Sa’ad da Joshuwa da dukan Isra’ilawa suka ga ‘yan kwanto sun ci birnin, da kuma hayaƙi ya murtuke bisa, suka juya kan mutanen Ai, suka ɗibge su.
22 Sauran Isra’ilawa kuwa suka fito daga cikin birnin suka fāɗa musu. Har ya zama suna tsakiyar Isra’ilawa gaba da baya. Isra’ilawa suka karkashe su, har ba wanda ya tsira ko ya tsere.
23 Amma suka kama Sarkin Ai da rai, suka kai shi wurin Joshuwa.
24 Sa’ad da Isra’ilawa suka gama karkashe mazaunan Ai duka a jeji inda suka fafare su, sai Isra’ilawa suka koma Ai, suka karkashe waɗanda suke cikinta.
25 A wannan rana aka ƙarasa mutanen Ai duka, mata da maza. Jimillarsu ta kai mutum dubu goma sha biyu (12,000).
26 Joshuwa bai janye hannunsa da riƙon mashin ba, sai da ya hallaka mazaunan Ai sarai.
27 Dabbobi da kayayyaki na birnin kaɗai Isra’ilawa suka kwashe ganima bisa ga faɗar Ubangiji zuwa ga Joshuwa.
28 Haka fa Joshuwa ya ƙone Ai, ya maishe ta tsibin kufai har abada. Tana nan haka har wa yau.
29 Ya rataye Sarkin Ai a bisa itace har maraice. Sa’ad da rana take faɗuwa Joshuwa ya umarta su ɗauke gawarsa daga itacen, su jefa a ƙofar birnin, su tsiba duwatsu da yawa a kanta. Tsibin duwatsun yana nan har wa yau.
An Karanta Albarka da La’ana a Dutsen Ebal
30 Joshuwa ya gina wa Ubangiji Allah na Isra’ilawa bagade a bisa Dutsen Ebal.
31 Ya gina shi kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra’ilawa, gama haka aka rubuta cikin Attaura ta Musa, aka ce, “Bagaden da aka yi da duwatsun da ba a sassaƙa ba, waɗanda ba mutumin da ya taɓa sa musu guduma.” A bisansa suka miƙa hadayu ta ƙonawa ga Ubangiji, da hadayu na salama.
32 A nan, a idon Isra’ilawa, Joshuwa ya kafa dokokin Musa a bisa duwatsun.
33 Sai Isra’ilawa duka, baƙi da haifaffun gida, tare da dattawansu da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya daura da akwatin alkawari, suna fuskantar firistoci, wato Lawiyawa, waɗanda suka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal kamar yadda Musa, bawan Ubangiji, ya riga ya umarta, cewa su sa wa jama’ar Isra’ila albarka.
34 Bayan haka ya karanta dukan zantuttukan shari’a, da na albarka da na la’ana, bisa ga dukan abin da aka rubuta cikin Attaura.
35 Babu wata kalmar da Musa ya umarta, da Joshuwa bai karanta a gaban dukan taron Isra’ilawa ba, tare da mata da ƙanana, da baƙin da suke zaune tare da su.