Ƙasar da za ku Mallaka Mai Albarka Ce
1 “Sai ku lura, ku aikata dukan umarnan da na umarce ku da su don ku rayu, ku riɓaɓɓanya, ku shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku.
2 Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba’in a jeji don ya koya muku tawali’u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.
3 Ya koya muku tawali’u, ya bar ku da yunwa, ya ciyar da ku da manna wadda ba ku sani ba, kakanninku kuma ba su sani ba, domin ya sa ku sani, ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji.
4 A shekarun nan arba’in tufafinku ba su yayyage ba, ƙafafunku kuma ba su kumbura ba.
5 Kun san wannan a zuciyarku, wato kamar yadda mutum yakan yi wa ɗansa tarbiyya, haka kuma Ubangiji Allahnku yake yi muku tarbiyya.
6 Saboda wannan sai ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ji tsoronsa.
7 Ubangiji Allahnku zai kai ku ƙasa mai kyau. Ƙasa mai rafuffukan ruwa da maɓuɓɓugai, da idanun ruwa masu ɓuɓɓugowa daga cikin kwari da tudu.
8 Ƙasa mai alkama, da sha’ir, da inabi, da ɓaure, da rumman. Ƙasa ce mai itatuwan zaitun da zuma.
9 Ƙasa ce inda za ku ci abinci a yalwace, ba za ku rasa kome ba. Ƙasa ce wadda tama ce duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.
10 Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda kyakkyawar ƙasa mai albarka da ya ba ku.”
Faɗakarwa Kada a Manta da Ubangiji
11 “Ku kula fa, don kada ku manta da Ubangiji Allahnku, ku ƙi kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa waɗanda na umarce ku da su yau.
12 Sa’ad da kuka ci kuka ƙoshi, kuka gina kyawawan gidaje, kuka zauna ciki,
13 garkunanku na shanu da tumaki suka riɓaɓɓanya, azurfarku, da zinariyarku suka ƙaru, sa’ad da dukan abin da kuke da shi ya haɓaka,
14 to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta.
15 Ubangiji ya bishe ku cikin babban jejin nan mai bantsoro, ƙasa mai macizai masu zafin dafi, da kunamai, da busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa. Ubangiji kuwa ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.
16 Ya ciyar da ku da manna a jeji, abin da kakanninku ba su sani ba, domin ya koya muku tawali’u, ya jarraba ku, don ya yi muku alheri daga baya.
17 Kada ku ce a zuciya, ‘Ai, ikona da ƙarfin hannuwana ne suka kawo mini wannan wadata.’
18 Sai ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne ya ba ku ikon samun wadata domin ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku kamar yadda yake a yau.
19 Idan kun manta da Ubangiji Allahnku, kuka bi gumaka, kuka bauta musu, kuka yi musu sujada, to, yau ina faɗakar da ku, cewa lalle za ku hallaka
20 kamar al’umman da Ubangiji ya hallakar a gabanku. Haka za ku hallaka domin ba ku kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku ba.”